Alamomi 10 da za ku gane idan ƴaƴanku sun fara shaye-shaye

Asalin hoton, Getty Images
Shaye-shayen miyagun ƙwayoyi matsala ce da ta jima tana ci wa al'umma tuwo a ƙwarya, musamman a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka.
Gwamnatoci a matakai daban-daban sun sha ɓullo da matakan yaƙi da ɗabi'ar, ciki har da kafa hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya ta NDLEA.
Galibi dai matasa ne suka fi faɗawa tarkon ɗabi'ar ta shaye-shaye.
Kuma a lokuta da dama shaye-shayen kan haifar da wasu munanan ɗabi'u, kamar sace-cace, da dabanci da sauran laifuka.
Hukumar NDLEA dai ta ce matasa ne rukunin al'umma da ke kan gaba wajen ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.

Asalin hoton, Getty Images
Abdullahi Sardauna, babban mataimakin kwamandan hukumar NDLEA mai kula da kama masu laifi da horas da ma'aikatan hukumar reshen jihar Borno, kuma tsohon jami'i mai kula da fadakarwa da gyaran halin masu ta'ammali da ƙwaya na hukumar ya shaida wa BBC wasu alamomi guda 10 da iyaye za su lura da su domin gane yaransu sun fara shaye-shaye, kamar haka:
1 - Sauyawar ɗabi'a
Abu na farko da iyaye za su lura da shi, shi ne sauyawar halayyar ƴaƴansu, kamar yadda jami'in ya bayyana.
''Idan a baya yaronka yana da ladabi da biyayya, sai kuma daga baya ka fahimci ya daina, ya kuma koma wasu ɗabi'u marasa kyau to ya kamata ka zurfafa bincike a kansa'', in ji shi.
2 - Sauya abokai ko ƙawaye
Wata alamar da za ka iya gane yaronka ya fara ta'ammali da ƙwaya, ita ce ka ga ya sauya abokansa na arziki - da a baya ka san shi da su.
Ko kuma idan mace ce ta sauya ƙawayenta na arziki da ka santa da su, ta koma wasu, ba tare da wata hujja mai ƙarfi ba
''Yau ka ganshi da wannan, gobe ka gan shi da wannan, waɗanda kuma ba ka aminta da halayensu ba'', in ji shi.
3) Chanjin tsarin rayuwa
Idan yaro ko yarinya suka fara shaye-shaye za su sauya yadda suka saba gudanar da rayuwarsu a cewar jami'in hukumar ta NDLEA.
''Alal misali da 'yarka ko ɗanka sun saba yin barci da wuri, sai ka ga yanzu sun dawo ba sa barci da wuri sai lokaci ya ja, ko a baya sun saba ba sa barci da wuri, sai kuma daga baya suka koma da wuri suke barci, ko kuma sun koma yin barcin a lokacin da ba su saba yi ba''.
''Ko kuma a baya suna tashi barci da wuri, amma sai ka ga yanzu ba su tashi sai lokaci ya ja, to ya kamata ka zurfafa bincike'', in ji shi.
4) Chanji a cin abinci
Idan yaro ya fara shaye-shaye, cin abinsa ma kan sauya a cewar jami'in na NDLEA.
''Idan a baya ka san ɗanka ko 'yarka ba mai yawan cin abinci ba ce, sai kuma daga baya ka fahimci sun ƙara yawan abincin da suke ci, ko kuma baya suna da yawan ci, amma daga baya suka rage ci, to nan ma ya kamata ka bincika''.
5) Yawan ɓatan abubuwa a gida
Yawan ɓatan abubuwa a gida na daga cikin alamun da za ka iya zargin ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-shaye, musamman idan ba shi da sana'ar.
"Yau an ajiye naira 50 ko 100 ta ɓata ba a ganta ba a cikin gida, gobe ma haka, to yana da kyau ka binciki 'yayanta'', in ji Abdullahi Sardauna.
Jami'in na NDLEA ya ce abubuwan da yara suka fi sata a gida domin samun na shaye-shaye sun haɗa da abubuwan amfani, ko sutura ko kamar sarƙar gwal ko awarwaro masu tsada.
6) Ƙarya
Ƙarya na daga cikin alamomin da za ka gane ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-shaye.
''Zai riƙa yin abubuwan da bai saba ba, kuma idan ka tambaye shi zai riƙa yi maka ƙarya, to daga nan ya kamata ka gane akwai abin da yake ɓoye maka'', a cewar Abdullahi Sardauna.
7) Saurin fushi
Wannan alama ce da za ka iya gane ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-sayen miyagun ƙwayoyi.
''Abu kaɗan sai ka ga yaro ya fusata yana faɗa da abokansa ko da 'yan'uwansa ko da mutanen gari'', in ji Abdullahi Sardauna.
8) Jin haushin jami'an tsaro
Wannan ma wata alama ce da ke nuna cewa ɗanka ko 'yarka sun fara shaye-shaye a cewar jami'in hukumar yaƙi da miyagun ƙwayoyin.
''Za ka ga ko a talbijin ya ga jami'in tsaro, ɗan sanda ko wani jami'in, sai ka ga yana fushi da shi, yana yawan zaginsa''.
9) Chanjin kamanni
Idan yaro ya fara shaye-shaye wasu da dama daga cikin kamanninsa za su sauya ba yadda aka san shi ba.
''Idan yaro fari ne , za ka ga ya fara rinewa yana komawa baƙi, fararen haƙoransa za su fara komawa baƙaƙe, fatarsa za ta fara tsagewa, musamman ƙafarsa, hannayensa za su koma baƙaƙe''.
10) Dawowa gida a makare
Na daga cikin alamomin yaro ya fara shaye-shaye ya riƙa dawowa gida a makare ba kamar yadda ya saba a baya ba.
''Da ya saba da wuri yake dawowa gida, amma yanzu sai ka lura ba ya dawowa sai dare ya fara yi, to ya kamata ka bincika''.
Abin da ke sa matasa faɗawa shaye-shaye

Asalin hoton, FATHI MOHAMED AHMED
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Jami'in hukumar ta NDLEA ya ce akwai abubuwa da dama da ke jafa matasa cikin sabgar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi a Najeriya da suka haɗa da.
Rashin kula daga iyaye: A lokuta da dama rashin kula da yara daga ɓangaren iyaye ne ke jefa wasu matasan shaye-shaye.
''A wannan lokaci da muke ciki iyaye suna da sakaci sosai dangane da yaransu'', kamar yadda jami'in ya bayyana.
''A wasu lokutan rabuwar aure tsakanin ma'aurata kan sa yaro ta taso ba tare da samun kulawar da ta dace daga iyayensa ba, sai ka ga wani lokaci yana wajen mahaifinsa, wani lokaci kuma a wajen mahaifiyarsa'', in ji shi.
Miyagun abokai: Hausawa na cewa zama da maɗauki kanwa ke kawo farin kai, a lokuta da dama abokai ne je jafa wasu matasa harkar shaye-shaye, a cewar jami'in.
Gurɓacewar rayuwa: Abdullahi Sardauna ya ce gurɓacewar rayuwa na daga cikin abubuwan da ke ƙara ruruwar matsalar shaye-shaye tsakanin matasa, musamman a ƙasashen Afirka.
''Yadda rayuwar yanzu ta koma, inda inda ka je za ka taras ana rikici-rikice, babu zaman lafiya, to hakan ya sa matasa da dama sun faɗa harkokin shaye-shaye'', in ji shi.
Sauƙin samun kayan maye: Wani abu da ke ƙara sanya matasa faɗawa harkar shan miyagun ƙwayoyi shi ne saukin samunsu kamar yadda jami'in hukumar NDLEA ya bayyana.
''Misa sholisho, wanda ake facin tayar mashin ko ta keke, a kowane shagon gyara za ka same shi, sannan magungunan tari suma a kowane shagon sayar da magunguna za ka samu'', in ji shi.
Zaman banza: ɗaya daga cikin manyan matsalolin da ke haifar da shan ƙwaya shi ne rashin sana'a.
''Yaro ya riƙa zama a cikin marasa aikin yi, sai ya fara tunanin koyon abin da takwarorinsa marasa aikin yi ke yi, wato shaye-shaye''.
'Kayan mayen da aka fi sha a Najeriya'
Jami'in hukumar ta NDLEA ya ce abin da masu ta'ammali da ƙwaya suka fi amfani da shi a Najeriya ya danganta da inda mutanen suke.
''Abin nan ne da Hausawa ke cewa kowane allazi da nasa amanu, kowane yanki da irin kayan mayen da aka fi samu a wajen'', a cewarsa.
Ya ƙara da cewa a yankin arewa maso gabashin Najeriya, galibi masu ta'ammali da ƙwaya sun fi amfani da tabar wiwi, da magungunan tari na ruwa da ƙwayoyi irin su tramadole, saboda saukin samunsu da kuma araharsu.
Sannan kuma jami'in ya ce akwai wasu abubuwan da ke sa maye waɗanda ba su cikin jadawalin Majalisar Dinkin Duniya irin su Akurkura da haɗa magi da lemon Laksara da sholisho da madarar sukudaye da sauransu.
Girman matsalar shaye-shaye a Najeriya
''Alƙaluman hukumar yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi ta Majalisar Dunya, (UNODC) na 2018 sun nuna cewa yawan masu shaye-shaye a Najeriya ya kai miliyan 14.3 ne shaye-shayen miyagun ƙwayoyi daban-daban a ƙasar'', in ji jami'in na NDLEA.
Ya ƙara da cewa ƙiyasin hukumar ta UNODC, ya kuma ce duk inda ka samu mutum huɗu masu ta'ammali da ƙwaya a Najeriya to guda ɗaya daga ciki mace ce.
Sannan kuma ya ce alƙaluman sun nuna cewa a cikin 'yan Najeriya takwas, mutum guda daga cikin na cutuwa saboda alaƙa da masu ta'ammali da ƙwaya.
Haka kuma jami'in ya yi kira ga iyaye da su sanya idanu kan 'ya'yansu domin tabbatar da cewa ba su faɗa wannan mummunar ɗabi'a ba.











