Yamal ya zama matashin da ya ci ƙwallo a Euro Sifaniya ta kai wasan karshe

Tawagar ƙwallon kafa ta Sifaniya ta kai wasan karshe a Euro 2024, bayan da ta doke Faransa 2-1 ranar Talata a filin wasa na Allianz Arena.

Faransa ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Randal Kolo Muani a minti na tara da fara wasa, amma Sifaniya ta farke ta hannun Lamine Yamal a minti na 21.

Yamal ya zama matashin da ya ci ƙwallo a gasar nahiyar Turai ko kofin duniya mai shekara 16 da kwana 362 ranar Talata.

Wanda yake rike da tarihin shi ne Pele na Brazil lokacin da ya ci Wales ƙwallo a gasar kofin duniya a 1958, yana da shekara 17 da kwana 239.

Dani Olmo ne ya samu ƙwallo ya tsame Aurelien Tchouameni ta gefe, sannan ya bugu, inda Jules Kounde ya sa kafa ta fada raga, bayan da ta wuce mai tsaron raga Mike Maignan.

Da wannan sakamakon Sifaniya za ta buga wasan karshe da duk wadda ta yi nasara ranar Lahadi 14 ga watan Yuli a filin Olympiastadion.

Ranar Laraba za a buga ɗaya wasan daf da karshe tsakanin Netherlands da Ingila a Signal Iduna Park.

Tawagogin sun kara a wasa 14 a bayan tun kan gumurzun Talata a Euro 2024, inda kowacce ta ci shida da canjaras biyu.

Sun kuma hadu karo hudu a gasar cin kofin nahiyar Turai, inda Faransa ta yi nasara a wasan karshe a 1994 da kwata fainal a 2000.

Sifaniya ce ta ci Faransa a 2012 a zagayen daf da na kusa da na karhe, sun tashi 1-1 a 1996.

Duk lokacin da aka hadu tsakanin Sifaniya da Faransa a Euro, duk wadda ta yi nasara ita ke lashe kofin nahiyar Turai a shekarar.

Sifaniya tana da Euro uku da ta lashe a 1964 da 2008 da 2012.

Ita kuwa Faransa mai biyu da ta dauka a 1984 da kuma 2000.

Ƴan wasan da suka buga wa Sifaniya da Faransa tamaula

An fara karawar da Nacho da Jesus Navas a tawagar Sifaniya, wadanda suka maye gurbin Robin le Normand da kuma Dani Carvajal.

Shi kuwa Pedri, wanda ke jinya an maye gurbinsa da Dani Olmo, wanda ya ci Jamus ya kuma bayar da ɗaya aka zura a raga a zagayen kwata fainal.

Ƴan wasan Sifaniya 11: Simon, Jesus Navas, Nacho, Laporte, Cucurella, Olmo, Rodri, Fabian, Yamal, Morata, Williams.

Masu jiran ko-ta-kwana: Raya, Vivian, Merino, Joselu, Torres, Grimaldo, Remiro, Baena, Zubimendi, Oyarzabal, Lopez, Perez.

Faransa ta ajiye Antoine Griezmann a benci, wanda ke kasa cin ƙwallo a gasar bana, inda ta saka Ousmane Dembele madadinsa.

Adrien Rabiot an fara wasan da shi a tawagar Faransa, bayan da ya gama hutun dakatarwa, an kuma fara da Kylian Mbappe a matakin ƙyaftin.

Ƴan ƙwallon Faransa 11: Maignan, Kounde, Upamecano, Saliba, Hernandez, Kante, Tchouameni, Rabiot, Dembele, Muani, Mbappe.

Masu jiran ko-ta-kwana: Samba, Pavard, Mendy, Camavinga, Giroud, Thuram, Zaire Emery, Fofana, Coman, Clauss, Areola, Konate, Barcola, Griezmann.