Wace ce Darya Dugina? Matar da ake ganin kisanta na iya sauya fasalin yakin Rasha da Ukraine

Darya Dugina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An yi wani taro na tunawa da Darya Dugina a birnin Moscow ranar Talata

Mutuwar Darya Dugina, mai shekara 29 kuma 'yar mutumin nan mai kishin ƙasar Rasha Alexander Dugin, ya mayar da hankalin duniya daga fagen dagar da ke cikin Ukraine zuwa titunan wajen birnin Moscow, wurin da aka tarwatsa motar Dugina da bam, inda ta mutu nan take.

Hukumar leken asirin Rasha (FSB) ta ce Ukraine ce take da alhakin kai wannan harin kisan gillar, kuma ta ce ta gano wata mata 'yar Ukraine wadda a asirce ta rika bin Dugina da mahaifinta har zuwa wani bikin da aka yi a yankin birnin Moscow, domin ta sami damar kai wannan harin, sai dai daga baya ta tsere zuwa kasar Estoniya mai makwabtaka kafin jami'an tsaro su kama ta.

Amma jami'an gwamnatin Ukraine sun musanta hannun kasarsu a wannan harin, inda Mykhailo Podolyak, wani mai ba shugaban Ukraine shawara ya bayyana lamarin a matsayin "farfagandar Rasha ce kawai".

Shugaba Putin ya yi tir da kisan, inda ya kira shi "mummunan laifi mai cike da keta".

Mista Putin ya bai wa marigayiya Dugina wata babbar lambar yabo ta Rasha ta "Order of Courage" sannan mahaifinta Alexander Dugin ya jinjina wa 'yar tasa yayin wani taron tunawa da ita da aka yi a birnin Moscow ranar Talata, inda ya ce: "Ta sadaukar da ranta a fagen daga ne domin Rasha. Kuma fagen dagar na nan."

Wace ce ita?

Darya Dugina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Dugina ta rika fitowa cikin wasu shirye-shirye na tashoshin talabijin din Rasha tana sukar kasar Ukraine.

Ba a san Darya Dugina sosai a cikin Rasha ba, sai dai da ita da mahaifinta sanannu ne a kafafen yaɗa labarai, inda suke sukar Ukraine da ƙasashen yammacin Turai.

Akan kira mahaifin nata Alexander "kwakwalwar Putin", kuma ya daɗe yana bayyana irin wannan ra'ayin - matakin da ya sa ya zama fitacce cikin al'ummar birnin Moscow - duk da cewa bai taba riƙe wani mukami na siyasa ba.

Shi ne ya kafa wata kungiya mai suna Eurasian movement, kuma kalamansa sun sami karɓuwa sosai tsakanin manyan 'yan siyasar Rasha.

Akwai masu ganin cewa Alexander Dugin aka kai wa wannan harin tare da 'yar tasa, sai dai ya koma wata motar jim kadan kafin su shiga motocinsu.

An haife ta a shekarar 1992, kuma ta halarci Jami'ar Jihar Moscow inda ta karanci falsafa.

A 2012 zuwa 2013, ta yi karatu na wani lokaci a Jami'ar Bordeaux III ta kasar Faransa, inda ta mayar da hankalinta kan nazartar ayyukan Plato, wani fitaccen malamin falsafa na tsohuwar Daular Girka.

Wasu labaran da za ku so karantawa

Mahaifinta mai matukar kishin kasar Rasha ne

Alexander Dugin

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Alexander Dugin shi ne wanda aka alaƙanta da sauya yadda Shugaba Putin ke kallon siyasar duniya

A wancan zamanin, mahaifinta Darya, wanda sananne ne saboda irin ra'ayoyin da ya ke bayyana wa na kiyayyar da ya ke nunawa ga kasar Ukraine, ya ƙara yin fice.

A 2014 an ga Mista Dugin cikin wani bidiyo yana magana cikin Rashanci: "Ina tunanin, kashewa, kashewa da kashe [Ukreniyawa] shi ne abin yi, babu wani batu da za a yi magana a kai."

A 2015, Amurka da Canada sun daukai matakan ladabtarwa kansa kan rawar da ya taka da ya kai ga Rasha ta mamaye yankin Crimea kuma ta ƙwace shi.

Jim kadan bayan haka ne abokan darya Dugina suka ce ta kusanci addinin Kiristanci na darikar Russian Orthodox, matakin da ya ba ƙawayenta mamaki har dangantakarta da su ta yi tsami.

"Sannu a hankali ta koma ga goyon bayan ra'ayin mahaifinta na faɗaɗa ikon Rasha a yankin Turai da Asia, abin da yasa muka daina tattaunawa da ita", inji wata ƙawarta yayin wata hira da ta yi wadda shafin intanet na Meduza ya wallafa.

Mai goyon bayan mamayar da ake yi wa Ukraine

A ƙarshen shekarun 2010, Darya Dugina ta fara bayyana a tashoshin talabijin na Rasha, baya ga rubuce-rubucen da ta rika yi a wasu shafukan sada zumunta masu alaƙa da gwamnatin ƙasar.

Ta riƙa bayyana ra'ayinta na goyon bayan kungiyoyin siyasa wadanda ta ce su ne za su sami galaba kan masu sassauncin ra'ayi a ƙasar.

Ta riƙa amfani da sunan "Platonova" a yawancin rubuce-rubucenta, wadda ke nuna yadda ta ke son alaƙanta kanta da tsohon mai koyar da falsafancin nan na Girka wato Plato.

Jami'an kasar Rasha na bincike a wurin da motar ta tarwatse

Asalin hoton, Investigative Committee of the Russian Federation

Bayanan hoto, Jami'an kasar Rasha na bincike a wurin da motar ta tarwatse
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A watan Nuwambar bara, bayan da Rasha ta fara tara makamai da sojojinta a kan iyakarta da Ukraine, Dugina ta kira Ukraine "iyakar tsaftacewa" tsakanin Rasha da ƙasashen yammacin Turai.

Bayan da Rasha ta kutsa cikin Ukraine, Dugina ta fito fili tana goyon bayan matakin, inda ta wallafa cewa wannan "matakin da zai tabbatar da wanzuwar daular Rasha".

A watan Yuli, Burtaniya ta saka sunanta cikin waɗanda aka ladabtar saboda "rawar da ta ke takawa wajen juya gaskiyar lamari dangane da Ukraine."

A tsakiyar watan Yuli ta ziyarci masana'antar Azovstal mai ƙera karafa jim kadan bayan Rasha ta ƙwace ta.

Kafin kashetan da aka yi, ta fara aiki tare da wani gidan wallafa littattafai mai suna "The Black hundred" domin wallafa wani littafi mai suna "The Book of Z".

Baƙin na "Z" ya zama wata alama ta mamayar da Rasha ke yi wa Ukraine, inda dakarun Rasha suka rika rubuta baƙin a jikin motocin sulke da tankokin yaƙinsu har ma ga kayan da suke sanyawa da baƙin na "Z" tun da aka fara wannan mamayar watanni shida da suka gabata.