Yadda Rasha da ƙasashen Yamma ke rububin samun goyon bayan Afirka

Fafutikar Rasha da ƙasashen Yamma a Afirka

Asalin hoton, EPA

Yayin da Rasha ke fuskantar tsangwama daga ƙasahen duniya, an yi wa Ministan Harkokin Wajen Rashar Sergei Lavrov kyakkyawar tarba a ziyararsa a ƙasashen Afirka huɗu.

Ziyarar ta Mista Lavrov ta nuna cewa har yanzu Rasha na da ƙarfi irin na difilomasiyya da za ta iya karawa da ƙasashen Yamma wajen samun goyon bayan ƙasashen Afirka.

Ministan ya ziyarci Masar, da Habasha, da Uganda da kuma Congo-Brazzaville.

Akasarin ƙasashen Afirka - kamar Najeriya da Kenya, waɗanda su ne mafiya girman tattalin arziki a yamma da kuma gabashin Afirka - sun goyi bayan yin Allah-wadai da hare-haren Rasha a Ukraine a ƙuri'ar da aka kaɗa a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) a watan Maris, inda suka nemi ta janye daga ƙasar.

Sai dai kuma kusan rabin ƙasashen da suka kauce wa kaɗa ƙuri'ar guda 17 daga Afirka suke.

Cikinsu har da Afirka ta Kudu - wadda ke jin Rasha ta taimaka mata wajen yaƙi da gwamnatin wariyar launin fata.

Da kuma Uganda wadda ke shirin karɓar shugabancin ƙungiyar ƙasashen 'yan ba-ruwanmu, wadda aka kafa lokacin Yaƙin Cacar-Baka tsakanin ƙasashen da ba sa son su ɗauki ɓangare a rikicin Tarayyar Soviet da ƙasashen Yamma.

Yayin wani taron manema labarai tare da Mista Lavrov, Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya jaddada matsayinsa na 'yan ba-ruwanmu kan yaƙin Ukraine.

"Ba ma son zama abokan gabar abokin gabar wani mutum," in ji shi.

A wajen Lavrov, muhimmancin ziyarar shi ne ya musanta batun cewa Rasha ce ke haifar da yunwa a Afirka.

Ya ɗora alhakin hauhawar farashin kayan da ake fuskanta kan takunkuman da ƙasashen Yamma suka ƙaƙaba wa ƙasarsa.

Kayan abinci

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Iyalai da dama na fama da hauhawar farashin kayayyakin abinci

Sai dai bai yi wa ƙasashen Afirka tayin komai ba don rage musu raɗaɗin halin da suke ciki.

Idan aka kwatanta da sanarwar Amurka da ta ce za ta bai wa ƙasashen tallafin dala biliyan ɗaya da ɗoriya domin su rage, da kuma shirin Faransa na noma domin tallafa wa ƙasashe Afirka, za a ga bambanci mai girma.

Shi ma Shugaban Faransa Emmanuel acron na yin tasa ziyarar a ƙasashen Afirka, inda yake ziyartar Kamaru, da Benin, da Guinea-Bissau.

Ya faɗa a Kamaru: "Wasu na zarginmu cewa takunkuman da ƙasashen Turai suka saka ne ke jawo matsalar ƙarancin abinci a Afirka.

"Wannan ba gaskiya ba ce. Rasha ta mayar da abinci da makamashi a matsayin makamin yaƙi."

Emmanuel macron

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto, Emmanuel Macron na ta ƙoƙarin gyara kyautata alaƙa da ƙasashen Afirka da ta yi wa mulkin mallaka a baya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Da yake mayar da martani kan wannan iƙirari, Lavrovya ce matsalar abincin ta fara ne daga lokacin annobar korona, amma ya yarda cewa "halin da ake ciki a Ukraine ya shafi kasuwar abinci".

A Masar, Mista Lavrov ya ba da tabbaci cewa kamfanonin fitar da abinci na Rasha za su cika alƙawuransu. Tattalin arziƙin Masar ya fi dogara da Rasha fiye da sauran ƙasashen Afirka.

Kusan kashi 80 cikin 100 na alkamar da take shigarwa cikin ƙasarta na fitowa ne daga Rasha da Ukraine, kuma ɗaya cikin uku na 'yan yawon buɗe-ido da ke zuwa ƙasar, daga Rasha suke.

A al'adance, alaƙar Rasha da Afirka ta ta'allaƙa ne kan harkokin tsaro - inda ake cinikin bindigogi da kuma jiragen sama na yaƙi.

A baya-bayan nan, an ga sojojin haya na Rasha da ke fafata yaƙi a Mali da kuma Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya da zimmar taimaka wa dakarun gwamnati murƙushe 'yan tawaye.

Yayin ziyarar tasa, Mista Lavrov ya mayar da hankali kan taron ƙawance da za a yi tsakanin Rasha da Afirka a Habasha a watan Oktoba mai zuwa, inda ake sa ran saka hannu kan yarjejeniyoyi da suka shafi tsaro da kasuwanci don yauƙaƙa alaƙa.

Shi ma wakilin musamman na Amurka a kusurwar Afirka Michael Hammer, Michael Hammer na ziyartar Masar da Habasha, yayin da shi kuma jakadan Amurka a MDD, Linda Thomas-Greenfield zai je Uganda da Ghana a mako mai zuwa.

Ƙasashen Yamma sun zaƙu su nuna wa ƙasashen Afirka rawar da za su iya takawa da kuma tuna musu cewa suna yin hakan ta hanyar ba da tallafi da kuma kasuwanci.