Shin duniya za ta iya rayuwa ba tare da dogora da fetur da gas na Rasha ba?

.

Asalin hoton, Getty Images

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta amince da toshe duka man Rasha da ake shiga da shi ta ruwa. Duka dai Tarayyar Turan ta ce waɗannan sabbin matakan za su zaftare adadin man da ake shiga da shi da kashe 90 cikin 100.

Sai dai duk da haka za a ci gaba da amfanin da gas ɗin Rasha sakamakon ƙasashe kamar Jamus sun dogara ne da gas ɗin na Rasha.

Wane irin tasiri takunkumin Tarayyar Turai zai yi?

Rasha tana kai kusan kashi ɗaya bisa huɗu na man da Tarayyar Turai ke amfani da shi.

Tarayyar Turan na da niyyar haramta man Rasha da ke shiga ta ruwa zua ƙarshen shekara. Hakan ai yi sanadiyyar rage man da aike kaiwa da kashi biyu bisa uku.

Sai dai Turan za ta ci gaba da bari ana shiga da man ta bututu, shi ma na wucin gadi. Wannan na zuwa ne sakamakon ƙasar Hungary na shiga da kashi 65 cikin 100 na duka man da take amfani da shi ta bututu tun daga Rasha.

Wasu ƙasashe biyu waɗanda ke shigar da adadi mai girma na man Rasha kamar su Jamus da Poland sun ce za su daina hakan zuwa ƙarshen shekara.

A wani ɓangaren, Amurka ta sanar da haramta amfani da man Rasha baki ɗaya da gas da kuma gawayi, haka kuma Birtaniya za ta daina amfani da man baki ɗaya zuwa ƙarshen shekara.

Wane makamashi ne EU ba za ta haramta ba?

Rasha na kai wa Tarayyar Turai kashi 40 cikin 100 na gas ɗin da take buƙata. Ƙasashe kamar Jamus sun dogara ne da gas ɗin

Hakan na nufin wannan lamarin na da wahala a ce ƙasashen Turai za su haramta gas ba tare da sun ƙuntata wa wasu ƙasashen ba.

A watan Maris, Tarayyar Turai ta sha alwashin rage shigar da gas da kashi biyu bisa uku a cikin shekara guda. Sai dai babu wata yarjejeniya da aka cimmawa kan wani ƙari.

Rasha dai ta samu tagomashi sakamakon ƙaruwar farashin makamashi, inda aka ƙiyasta cewa ta samu ribar dala biliyan 430 daga sayar da fetur da gas zuwa Turai a cikin shekara guda.

Mene ne adadin man da Rasha ke fitarwa

Rasha ita ce ƙasa ta uku a duniya wajen samar da mai bayan Amurka da Saudiyya.

Kusan rabin man da Rasha ke fitarwa na zuwa Turai ne kafin aka sanar da takunkumin.

A 2020, Netherlands da Jamus kusan kullum sai sun shiga da man Rasha ƙarsu.

Sai dai Rasha ta shigar da 8 cikin 100 na man da Birtaniya ke buƙata a 2020 da kuma kashi 3 cikin 100 na wanda Amurka ke buƙata a 2020.

Wane mai za a yi amfani da shi amadadin na Rasha?

Mai sharhi da bincike Ben McWilliams ya bayyana cewa abu ne mai sauƙi a samu masu samar da mai da gas ganin cewa idan ana samun mai daga Rasha, akwai wani mai ko gas mai yawa a sauran wurare.

Wasu ƙasashe waɗanda mambobi ne na IEA sun samar da kusan ganga miliyan 120 na mai - wanda wannan adadi ne mafi girma a tarihin duniya.

Zuwa ƙarshen watan Maris, Shugaban Amurka Joe Biden ya bayar da umarnin fitar da fetur mai ɗumbin yawa daga rumbu domin karya farashin mai.

Amurka na kuma son Saudiyya ta ƙara adadin man da take samarwa haka kuma Amurkar ta soma tunanin sassautawa a takunkumin da ta saka wa Venezuela.

.

Asalin hoton, AFP

Sai dai bayan da ƙasashen yamma suka saka takunkumi kan Rasha, Shugaba Putin ya sanar da cewa dole ƙasashen da ba ya shiri da su su biya gas a kuɗin Rasha.

Kamfanin makamashi na Rasha Gazprom ya rage kayan da yake kaiwa Poland da Bulgaria da Finland inda ya ce ba zai ci gaba ba sai an biya shi kuɗi a roubles.

Akwai yiwuwar matakin da Rasha ta ɗauka na rage kai kaya Finland ya samo asali ne daga matakin da Finland ɗin ta ɗauka na son shiga Nato.

Finland na sawo akasarin gas ɗinta daga Rasha. Tarayyar Turai ta ce tana kallon matakin da Rasha ta ɗauka a matsayin bita-da-ƙulli.

Akwai ƙasashen EU da dama da ke shirin fuskantar irin wannan matsala a kusan tsakiyar watan Mayu a lokacin da za a biya kuɗi.

Biyan kuɗi a roubles zai ƙara haɓaka tattalin arzikin Rasha haka kuma tattalin arzikin ƙasar zai samu tagomashi.

Su wa za su biya a kuɗin roubles?

Ms Von der Leyen ta yi gargaɗin cewa bin abin da Rasha ke so zai ci karo da ƙa'idojin Tarayyar Turai kuma hakan zai kasance wata barazana ga kamfanonin da za su yi haka.

Ƙasashen Tarayyar Turai an raba kansu kan batun yadda za su dogara da man Rasha.

Kamfanonin gas a wasu ƙasashen Turai ciki har da Jamus da Hungary da Slovakia duka sun amince su biya kuɗin gas ɗinsu a euros ta hanyar bankin Rasha wato Gazprombank waɗanda za a mayar da su roubles.

Jaridar Financial Times ta bayar da rahoton cewa kamfanonin gas a Austria da Italiya na shirin yadda za su buɗe asusun ajiya.

A makon da ya gabata ne Tarayyar Turai ta ce idan masu sayen gas daga Rasha za su iya kammala biyan kuɗaɗensu a kudin euros kuma za su samu tabbacin hakan, wannan ba zai iya cin karo da yarjejeniyar ba.

Ya adadin gas ɗin da Rasha ke kai wa Turai?

A 2019, Rasha ta kai wa Turai kashi 41 cikin 100 na gas ɗin da take amfani da shi.

Idan Rasha ta daina kai wa Turai gas, Italiya da Jamus za su sha wahala sakamakon sun fi dogara ne a kan gas din Rasha.

Russia gas exports

Rasha na samar da kashi 5 cikin 100 na gas ɗin Rasha haka kuma Amurka ba ta shigar da wani gas daga Rasha cikin ƙasarta.

Rasha na tura gas zuwa Turai ta hanyoyi ko bututu da dama. Gas ɗin na taruwa ne a tashoshi na yankuna daga nan sai a rarraba shi zuwa nahiyoyi.

Reality Check branding