Wasu ƴan Najeriya a Facebook sun fusata kan shirin janye tallafin man fetur

..

Asalin hoton, Getty Images

Da alama yan Najeriya da dama sun fusata game da shirin da gwamnatin kasar take yi na janye tallafin man fetur baki daya daga shekara mai zuwa.

Hakan ya sa Shugaban kamfanin man fetur na kasar, Mele Kyari, ya ce idan aka cire tallafin za a iya sayar da man fetur ɗin tsakanin 320 zuwa 340.

A shafukan sada zumunta musamman Facebook, kusan duk inda mutum ya leƙa zancen ake yi inda akasari ake ta Allah-wadai da lamarin.

Akasari mutane suna watsi da wannan lamarin ne saboda kuka da suke yi na tsadar rayuwa musamman hauhawar farashin kayayyakin abinci da kuma rashin tsaro da ake fama da shi.

Wannan ne ya sa sanannun mutane da dama da ƙungiyoyi masu zaman kansu suka fito suna watsi da wannan lamari.

A nata ɓangaren, ƙungiyar ƙwadago ta ƙasar wato NLC ta gargaɗi gwamnatin ƙasar.

Cikin sanarwar NLC ta ce tunanin raba wa ƴan Najeriya miliyan 40 naira 5000 domin rage musu raɗaɗin ƙarin farashin man fetur 'abin dariya ne', inda ta ce idan aka lissafa kuɗin zai haura na tallafin man fetur ɗin da ake bayarwa a kasar.

Haka kuma sanarwar ta ce abin takaici ne ganin cewa Najeriya ce kadai kasa cikin mambobina OPEC da ba ta tace man da ta ke samarwa a cikin gida, sai an fitar da shi kasashen ketare.

Haka shi ma ɗan gwagwarmayar nan na Najeriya wato Sanata Shehu Sani ya ce idan aka cire tallafin komai zai karu, kama daga kuɗin makaranta da gidajen haya da abinci da kudaden wuta da makamantansu.

Me ƴan Najeriya ke cewa game da yunƙurin cire tallafin man fetur ɗin

Muhawara dai ba ta ƙare ba a shafukan sada zumunta kan wannan lamari inda jama'a suke ta bayyana ra'ayoyi daban-daban.

..

A shafin Facebook dai Babawo Mato Mai'adua ya goyi bayan maganar Shehu Sani inda ya ce cire tallafin man zai jefa talakawan Najeriya cikin wani hali.

..

A nasa ɓangaren, Saleh Garba Toro ya ce a ganinsa ko an cire wannan tallafin ba zai kawo ƙarshen cin hanci ba kuma ba ƴan ƙasar tallafin dubu biyar ba ita ce mafita ta rage talauci ba.

..

Shi ma Gambo Barau Potiskum yana ganin cewa raba wa mutane dubu biyar a duk wata wata hanya ce ta ɓarnata kuɗin Najeriya.

,.

Haka shi ma Falal Ango cewa ya yi kwata-kwata ba ya goyon bayan cire tallafin man fetur ɗin inda ya ce hakan zai jawo ƙarin wahala ne kawai ga jama'a.