NLC: Kungiyar kwadago ta Najeriya ta ce ba ta amince a janye tallafin mai ba

Ayuba Wabba

Asalin hoton, Other

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta yi watsi da shirin gwamnatin kasar na janye tallafin mai wanda zai kai ga ƙara tsadar farashin man fetur.

Kungiyar ta ce ba za ta faɗa gadar zaren da gwamnatin ƙasar ke neman shiryawa mutanenta ba, yadda ta bayyana a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugaban NLC Ayuba Wabba.

Kwamared Ayuba Wabba ya ce batun da shugaban NNPC Malam Mele Kyari ya yi ta karin farashin man fetur zuwa 340 daga watan Fabirairu ba ta yi wa 'yan kasar dadi ba.

Cikin sanarwar NLC ta ce tunanin rabawa ƴan Najeriya miliyan 40 naira 5000 domin rage musu radadin karin farashin man fetur 'abin dariya ne', inda ta ce idan aka lissafa kudin zai haura na tallafin man fetur din da ake bayarwa a kasar.

Gwamnatin Najeriya dai ta ce za ta janye tallafin mai baki ɗaya a tsakiyar 2022, kuma tana tunanin raba wa ƴan Najeriya kuɗin tallafin domin rage raɗaɗin da tasirin janye tallafin zai haifar.

Amma ƙungiyar kwadagon ta jaddada rashin amincewa da cire tallafin man inda ta ce zai karawa 'yan kasar matsin rayuwa.

Haka kuma sanarwar ta ce abin takaici ne ganin cewa Najeriya ce kadai kasa cikin mambobina OPEC da ba ta tace man da ta ke samarwa a cikin gida, sai an fitar da shi kasashen ketare.

A karshe Ayyuba Wabba ya ce kamar yadda suka saba yi a kowanne lokaci, suna kira ga gwamnatin tarayya ta duba wasu hanyoyi uku da suke ganin ya kamata abi domin kawo sauki kan batun.

  • A rika saukakawa masu sayar da mai da faduwar da darajar Naira ta yi ke shafar su, ta hanyar shiryawa kasasahe makwabta wajen amfani da matatun mansu domin tace man da Najeriya ke samarwa zuwa kasashen.
  • A yi kokarin farfado da matatun mai guda hudu da Najeriyar ke da su, wanda za su saukaka fitar da man fetur din da kasar ke hakowa, ta hanyar tace shi da sarrafawa a cikin gida.
  • Tattara kididdigar yawan man fetur din da 'yan Najeriya ke amfani da shi kowacce rana, saboda wannan na daga cikin abubuwan da babu ainahin kididdigar yadda ake amfani da shi a kasar.

A karshe sanarwar ta ce matukar ba a dauki matakin ba, tabbas wahalar za ta kare kan talakan Najeriya, sakamakon yadda farashin dalar Amurka ya kai naira 560.

A shekarar 2009 da gwamnatin Najeriya ta cire tallafin mai, kungiyar kwadago ta jagoranci gagarumin jerin-gwano da don nuna rashin amincewa da shirin gwamnatin kasar na janye tallafi daga harkar mai.

A wancan lokacin hukumomi a Najeriya sun ce babu makawa sai an aiwatar da shirin inda suka ce janye talafin nada fa`ida ga jama`ar kasar, saboda zai magance tsada da karancin mai.

Amma kungiyar kwadagon a nata bangaren, ta ce kasashen da ba su da arzikin mai suna daukan matakan tallafa wa al`umominsu, don haka ba ta ga dalilin da zai sanya Najeriyar ta janye nata tallafin ba.

A halin yanzu, abin jira a gani shi ne matakin da kungiyar kwadagon za ta dauka matukar gwamnatin Najeriya, ta ki amincewa da janye aniyarta ta cire tallafin man.