NNPP: 'Ba za mu sa hannu kan shirin zaman lafiya lokacin zabe a Kano ba'

Asalin hoton, OTHER
Jam'iyyar adawa ta NNPP da ɗan takararta na gwamna a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya, sun yi barazanar ƙauracewa sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya don tabbatar da ganin an gudanar zaɓuka cikin kwanciyar hankali da lumana.
Shugaban jam’iyyar a Kano, Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya shaida wa BBC cewa, su a tsarinsu ba zasu je su sanya hannu a kan abin da suka san cewa idan aka tabasu ba zasu kyale ba.
Ya ce, an yi irin haka ba sau daya ba to a yanzu sun kai makura.
Shugaban na NNPP a Kano, ya ce ko baya bayan nan shugaban APCn, Abdullahi Abbas sai da ya ce koda tsiya-tsiyar sai sun ci zabe.
Alhaji Umar Haruna Doguwa, ya ce “ Mu muna wakiltar jama’a ne don haka ba zamu rungume hannu mu tsaya muna kallo ana gaya mana maganar da aka ga dam aba, don haka muma mun shirya mun kuma tanadi matakan da zamu rinka dauka domin duniya taji abin da ke faruwa a Kano.”
Ya ce, “ Kowa a Kano ya yarda cewa mu masu son zaman lafiya ne kuma masu son yin abin da yakamata ne, abin haushin shi ne irin kalamai da APC ke yi a gaban jami’an tsaro ake yi kuma ba a daukar wani mataki.”
A don haka muna ganin zamu kauracewa sanya hannu a kan yarjejeniyar zaman lafiyar, saboda mutanen da muke gani zasu ba da takardar da za a sanya hannu sune jami’an tsaro, to a gabansu aka yi wadannan abubuwan kuma basu ce komai ba, inji shi.
Shugaban na NNPP a Kano, ya ce su abin da suke so shine jami’an hukuma su duba takardar korafinmu, su duba mutanen da suka kira sunayensu a ciki a bincike sus ai ayi abin da ya dace.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ce, “ Kuma a rinka hukunta duk wanda ya yi laifi koma a tagawar wa yake a kamo shi a hukunta shi, wannan shi ne zai kawo dauwamammen zaman lafiya a jihar Kano.”
Shima a nasa bangaren, dan takarar kujerar gwamna a jam’iyyar ta NNPP a Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce ba za su shiga yarjejeniyar ba muddin hukumomi ba su kama tare da gurfanar da shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Kano, Alhaji Abdullahi Abbas gaban kotu ba, bisa zarginsa da furta kalaman da ka iya ta da rikici.
Abdullahi Abbas ya musanta zarge-zargen da ake masa na amfani da kalaman tunzura gangamin yaƙin neman zaɓe da tarukan siyasa.
Kalmar "ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, sai mun ci zaɓe", ba baƙon abu ne domin an sha jiyo Abdullahi Abbas na ambato wadannan kalamai a tarukan siyasa tun daga zaben 2019.
Ƴan adawa a jihar na cewa irin wadannan kalamai na Abdullahi Abbas, wata alama ce da ke nuna cewa mai yiwuwa akwai wani mummunan nufi da APC ta yi game da babban zaɓe da ke tafe a jihar.
Sai dai a tattaunawarsa da BBC, shugaban APCn a Kano ya ce an yi wa maganganunsa mummunar fahimta ce kawai.
A makon da ya gabata ne BBC ta kawo rahoto kan zargin da ake yi wa shugaban jam'iyyar APC na yin kalaman tunzura rikici.
"Tsiya-tsiya takobi ce? Tsiya-tsiya mashi ne? Tsiya-tsiya wuƙa ce? Tsiya- tsiya bindiga ce? Ai dagewa ce lallai ka tsaya sai an ci zaɓe, abin da ake nufi kenan.
Abdullahi Abbas ya ce ai "abokan hamayyar mu shaƙiyanci ne, ai sun san abin da muke nufi, batu ne na jefa ƙuri'a kuma mu kuri'a da ake jefawa muke nufi da tsiya-tsiya, domin ita ce tsiyar ai da muke nufin zamu saka musu a zaɓe".
Ya yin da ya rage kasa da kwanaki 100 a gudanar da babban zabe a Najeriyar, abin jira a gani shi ne irin matakin da jami'an tsaro za su dauka musamman dakile kalaman tunzuri tsakanin 'yan siyasa a yakin neman zabe.










