Ko da tsiya-tsiya: Shugaban APC a Kano ya fara ta da ƙura kafin 2023

Asalin hoton, Facebook/Faizu Alfindiki
- Marubuci, Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
Kamar yadda suka saba, wasu 'yan siyasa a Najeriya sun ɗora daga inda suka tsaya wajen yin duk mai yiwuwa don jam'iyyarsu ta ci zaɓe yayin da babban zaɓen 2023 ke ƙaratowa.
A wannan karon, mutumin da aka saba ji da irin waɗannan kalamai ne ya sake yin su - wato Shugaban Jam'iyyar APC mai mulkin Jihar Kano Abdullahi Abbas.
"Ko da tsiya ko da tsiya-tsiya, ko ana ha-maza ha-mata, ko me za a yi, ko me zai faru, ko mai tafanjama fanjam sai mun ci zaɓe," in ji Abdullahi Abbas.
Shugaban jam'iyyar APC ɗin, wadda ke mulkin Najeriya da jihar ta Kano, ya yi waɗannan kalamai ne a ranar Laraba yayin da suke ƙaddamar da kamfe ɗin takarar gwamna a Ƙaramar Hukumar Gaya.
A bayyane take ciyaman ɗin yana sane da cewa kalaman da yake yi ba su dace ba amma duk da haka sai ya faɗa.
Kafin ya fara ɓaɓatun sai da ya ce: "...ina tabbatar muku cewa wannan alama ce ta cin zaɓe. Wannan karon, duk da cewa an ce na daina faɗa, ko da tsiya..."
BBC ta nemi jin dalilinsa na yin waɗannan kalamai amma bai ɗaga waya ba sannan kuma bai amsa saƙon tes da muka tura masa ba.
Gwamnan Kano Abdullahi Ganduje ne ya jagoranci taron, wanda ya samu halartar mataimakin gwamnan kuma ɗan takarar APC, Nasiru Yusuf Gawuna, da abokin takararsa Murtala Garo, da Sanata Kabiru Ibrahim Gaya.

Asalin hoton, Facebook/Faizu Alfindiki
Kalaman nasa na zuwa ne a lokacin da hukumomi a cikin gida da ƙasashen waje ke kira ga 'yan siysa da guji kalaman tayar da fitina.
A ranar Alhamis Birtaniya ta ce ta zura ido kan 'yan siyasa da jam'iyyu, da jami'an tsaro da duk wani mutum da zai haifar ko ingiza rikici ta shafukan sada zumunta a zaɓen 2023 da zimmar hana shi shiga ƙasarta.
A farkon makon nan, tsohon Shugaban Mulkin Soja Janar Abdulsalami Abubakar da Ƙungiyar Kiristoci ta CAN suka gargaɗi 'yan siyasa game da tashin hankali kafin da kuma yayin zaɓen.
'Duk wanda aka kama za mu sake shi kuma ɗan sandan zai rasa aikinsa'

Asalin hoton, Kano Municipal
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ga 'yan Kano da masu bin siyasar jihar, ba za su yi mamaki ba domin sun san da ma ana yi wa Abdullahi Abbas laƙabi da "ko da tsiya" saboda irin waɗannan kalamai da ya yi gabanin babban zaɓen 2019.
Yayin da jam'iyyarsu ta APC ke kan siraɗin yin nasara ko shan kaye a zaɓen 2019, Abdullahi ya nemi matasa su tabbatar cewa jam'iyyarsu ta yi nasara, yana mai barazanar korar duk ɗan sandan da ya kama su daga aiki.
"Sai dai ba mu sani ba ko za a iya kai mutum ofishin 'yan sanda, amma ina tabbatar muku ko wane ne za mu sake shi, kuma ba zancen zuwa Bompai (hedikwatar 'yan sanda a Kano), kuma ɗan sandan da ya yi kamun idan bai yi sa'a ba ya bar aiki," kamar yadda ya faɗa wa matasan.
Cikin sowa da yi masa kirari, Abdullahi Abbas ya ci gaba da cewa: "Ina tabbatar muku za mu kare mutuncinku. Zaɓen nan ko da tsiya-tsiya sai mun ci shi."
Tarihin Abdullahi Abbas a taƙaice:
- Ya zama shugaban APC a Kano a 2018
- Ana kiran sa ɗan sarki saboda ɗa ne ga Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi - ɗan marigayi Sarkin Kano Sanusi I
- Ya yi kwamashinan ayyuka na musamman a gwamnatin Ganduje
- Ya yi kwamashinan muhalli a gwamnatin Rabiu Kwankwaso
Zaɓen gwamna na 2019 na ɗaya daga cikin mafiya zafi da aka yi a tarihin siyasar jihar, abin da sai da ya kai ga zuwa zagaye na biyu tsakanin PDP da APC kafin hukumar zaɓe INEC ta bayyana Ganduje a matsayin wanda ya lashe shi a wa'adi na biyu.
An shiga zagaye na biyun ne sakamakon soke ƙuri'u masu yawa da aka kaɗa ba bisa ƙa'ida ba a unguwar Gama da ke cikin Ƙaramar Hukumar Nassarawa, waɗanda INEC ta ce sun zarta yawan tazarar da ke tsakanin Abba Kabir Yusuf da Gwamna Abdullahi Ganduje.
Rahotanni sun bayyana cewa har sai da rundunar 'yan sandan jihar ta tsare Mataimakin Gwamna Nasiru Gawuna da Kwamashinan Ƙananan Hukumomi a lokacin Murtala Sule Garo saboda zargin tayar da hankali.
Hukuncin da doka ta tanada kan kalaman ta da fitina
Sashe na 92 zuwa 96 na Dokar Zaɓe ta 2022 a Najeriya ne suka yi magana kan yaƙin neman zaɓe da kuma hukunce-hukunce kan laifuka, cikinsu har da na kalaman tayar da fitina a lokutan yaƙin neman zaɓen.
Sashe na 93 (1) na dokar ya ce: "Haramun ne jam'iyya ko ɗan takara ko wani mutum ko rukuncin mutane su yi wa wani barazana ba ta hanyar yin amfani da ƙarfi ko tashin hankali yayin yaƙin neman zaɓe don tilasta wa mutumin ko wani daban wajen goyon bayansu ko kuma ya daina goyon bayan wata jam'iyya ko wani ɗan takara."
"(2) na dokar ya ce: "Duk jam'iyya ko ɗan takara ko mai neman takara ko wani rukunin mutane da suka saɓa wa tanadin wannan sashe ya aikata laifi kuma za a hukunta shi da:
"(a) Idan ɗan takara ne ko mai neman takara ko wani mutum ko rukunin wasu mutane, tarar abin da bai wuce naira N,1,00,000 ko kuma ɗaurin wata 12.
"(b) Idan kuma jam'iyya ce, tarar naira N2,000,000 a karon farko, da kuma naira N500,000 idan ta sake yin laifin a gaba."
'Idan ba a ɗauki mataki ba lamarin zai haifar da fitina'
Jim kaɗan bayan ciyaman Abdullahi Abbas ya yi waɗancan kalamai sai jagororin jam'iyyar da magoya baya suka ɓarke da sowa da ƙyaƙyata dariya, cikinsu har da Gwamna Ganduje.
"Yadda ake fatan a kammala zaɓe lafiya, idan kuma aka fara irin waɗannan kalamai ana tunzuro sauran mutane ne su ma su dinga yin hakan," in ji masanin kimiyyar siyasa a Kano Malam Kabiru Sufi.
Masu sharhi kan al'amuran siyasa na kallon kalaman a matsayin na tunzuri, waɗanda idan ba a ɗauki mataki ba zai haifar da matsala.
"'Yan siyasa na cewa kowa na da ikon tayar da fitina, idan wani ya nuna cewa tashin hankali ne makaminsa to yana bai wa wani dama ne shi ma ya yi," a cewar Sufi.
"Wannan dalilin ne ya sa ya kamata a kauce wa irin waɗannan kalaman don a samu tsaftatacciyar siyasa, a ja hankalin masu yin su don kar a ɗumama siyasar baki ɗaya."
Tuni ma'abota shafukan sada zumunta suka laƙaba wa Abdullahi Abbas sunan "tsiya-tsiya" tare da mayar da abin raha a muhawara da sauran hirarrakinsu na yau da kullum.
Hakan yana alamta cewa ko dai masu zaɓe - waɗanda ake yin abin don su - ba su fahimci girman matsalar ba, ko kuma ba su ɗauki abin da muhimmanci ba.
Sai dai Sufi na ganin suna yin hakan ne don su rage zafin abin tun da hukumomi ba su yi magana ba.
"Sun fahimci girman matsalar, wataƙila sun jira ne su ga ko za a samu tsawatarwa, rashin samun tsawatarwar kuma sai suka mayar da shi raha, kuma akwai hikima cikin hakan."
Tarihi ya nuna cewa siyasar Kano ta gaji kalamai na tayara da hankali duk lokacin da 'yan siyasa suka hau duro. Sai dai Kabiru Sufi na ganin kalaman ciyaman sun fi zafi ne saboda girman muƙaminsa.










