Dalilai biyar da suka sa Siyasar Kano ta fi jan hankali a Najeriya

.

"Siyasar Kano sai Kano" - wannan kirari ne na siyasar Kano da ke jan hankali a arewacin Najeriya.

Yana da wahala a ce siyasa ta zama iri ɗaya, a kan samu bambanci lokaci zuwa lokaci daga wuri zuwa wuri.

Ko wane lokaci yakan tafi daidai da yanayi na tirihin siyasar Kano, musamman idan an buga gangar siyasa a Najeriya.

BBC ta tattauna da masanin siyasa a Najeriya Dr Kabiru Sufi wanda ya yi bayani kan abubuwa biyar da suka shafi siyasar Kano.

Masanin ya ce akwai abubuwan da suka sa ake yi wa siyasar Kano kirarin "Siyasar Kano sai Kano" wanda har ya sa ta banbamta kuma take jan hankali - waɗanda ya bayyana kamar haka:

Tarihi

Tarihin siyasar Kano yadda aka fara da yadda aka yi gwagwarmayar siyasa ya tasirantu ne kan al'ummar jihar.

Tahirin ya tasirantu ya samo asali ne daga gwagwarmayar siyasar da aka yi kafin samun ƴancin kai musamman bayan ƙirkirar yankin arewa da aka yi a shekarar 1946, da kuma kafa siyasar farko ta NPC da aka yi a yankin a 1949 da kuma kafa jam'iyyar NEPU a 1950.

Daga lokacin da aka kafa NEPU gwagwarmayar siyasa ta fara a Kano, saboda a Kano ne aka yanke mata cibiya.

Mafi yawan wadanda suka yi gwagwarmayar NEPU mazauna Kano ne. A nan ne ta kafu kafin sauran yankuna suka ɗauka, inda jam'iyyar ta zama babbar jam'iyyar adawa a yankin arewa gaba ɗaya.

Gwagwarmayar NEPU a tarihance ta yi tasiri sosai kan yanayin siyasar kano - inda ya kasance NEPU ta zama jam'iyyar masu ra'ayin neman sauyi.

Tasirin NEPU ya sa duk lokacin da aka buga gangar siyasa a Najeriya ake samun wata jam'iyyar da ke maimaita makamancin tsarin NEPU, wato jam'iyyar da ta ƙunshi ƴan gwagwarmaya.

Yanayin NEPU da yadda ta yi gwagwarmaya da NPC, shi ne yake maimaita kansa yawanci lokaci zuwa lokaci jam'iyyu da suka biyo bayansu a siyasar Kano.

Short presentational grey line

Yawan al'umma

Kano jiha ce mai yawan al'umma a Najeriya, kuma ɗaya daga cikin jihohin da ke tasiri a siyasar Najeriya.

Yawan al'umma wanda ke tasiri ga yawan ƙuri'a ne ke sa ake sa ido a siyasar Kano.

Duk lokacin da ake batun siyasar ƙasa, dole ba za a manta da siyasar Kano ba, saboda ruwan ƙuri'un al'ummar jihar.

A wani lokacin siyasa, manyan jam'iyyun siyasa kan mayar da hankali a Kano su jira su ga tsari da alƙiblar Kano kafin su san me za su yi don saboda yawan kur'iu na yawan al'ummar jihar.

Siyasa ta yi tasiri a Kano kuma ta shiga ran al'umma wanda ya sa mutane ke fitowa su yi zaɓe, kumwa wanda ya sa siyasar Kano ke ɗaukar hankali a Najeriya.

Short presentational grey line

Sauyin da siyasa ta samu

Zuwan kafofin sada zumunta na intanet da yawaitar kafafen yaɗa labarai sun ƙara haifar da sauyin siyasa a Kano.

An samu wayewar kai sosai saboda wanzuwar kafafen yaɗa labarai na zamani da kafofin sada zumunta - zuwansu da ƙaruwarsu ya sa yanayin siyasar ya sauya.

Kano tana daga cikin jihohin da suke da yawan kafafen yada labarai na rediyo da talabijin kuma ko wannensu yakan fito da shirin siyasa wanda ke tasiri sosai kan yadda al'umma suke ilmantuwa da yadda siyasar ke shiga ransu.

Haka kuma tasirin kafofin sadarwa na intanet ya taimaka wajen ƙara zafin siyasa da jan hankalin siyasar Kano - manyan ƴan siyasa suna da waɗanda suke masu gwagwarmaya a kafofin sadarwa na intanet, musamman masu kare muradunsu da ƙoƙarin tura muradunsu.

Akwai kuma "ƴan baka" waɗanda ke shiga kafofin yaɗa labarai na rediyo da talabijin suna suka da kare manufar siyasar uwayen gidansu.

Short presentational grey line

Rarrabuwar kai

Tun bayan jamhuriyya ta ɗaya zuwa jamhuriyya ta biyu kamar rikicin da aka samu a jam'iyyar PRP ya sa a cikin jam'iyya ɗaya za a samu rarrabuwar kai a samu gidajen siyasa sun rarrabu.

A 1981 zuwa 1982 an samu rabbuwar kai a PRP inda aka samu ɓangarori biyu na "ƴan taɓo da Tsantsi" wanda ake gani shi ne na farko da aka samu faruwarsa a siyasar Najeriya.

Rarrabuwar kan ya sa ɓangaren santsi ya ɓalle suka kafa wata jam'iyya. Kuma wannan ne yake ci gaba da maimatuwa da abin da ake gani a siyasasun da suka biyo baya.

Wannan rarrabuwar da ake samu na siyasa, shi ma wani abu ne da ya samo asali a yanayin siyasar Kano.

Yanayin ne ke sa ake tsallakawa daga wannan ɓangaren zuwa zuwa wani ɓangaren, ko kuma har ta kai a haɗe tsakanin wani ɓangare da wani.

Wannan ne ke ci gaba da sauyawa har ake yi wa siyasar Kano da kirarin siyasar Kano sai Kano.

Short presentational grey line

Rashin tabbas

Yanayin siyasar Kano ya sa ba za a iya ci mata alwashi ba.

Tarihi ya nuna babu tabbas a yanayin siyasar Kano. Abubuwa na iya sauyawa, haka ma lisaffi da alƙalumman yanayin siyasar na iya canzawa cikin ƙanƙanin lokaci.

Zai kasance komi zai iya sauyawa a hasashen da ake yi cikin sati daya ko biyu ko uku, wanda ke tabbatar da babu tabbas a siyasar Kano.

Ba sabon abu ba ne a siyasar Kano cikin lokaci ƙanƙani abokan hamayya da juna su rungumi juna. Wanda wannan ne yake sa siyasar Kano ke da bambanci.

Wannan layi ne