Zaben 2019: Yadda yarfen siyasa ya yi kamari a Najeriya

Asalin hoton, Reuters
Manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya, PDP da APC sun ta yi wa juna yarfe gabanin zaben shugaban kasa da aka dage.
An baza labaran karya da gaskiya a shafukan sada zumunta kan yadda Atiku Abubakar dan takarar PDP ya sayar da kadarorin kasar nan.
A wani bangaren, 'yan adawa sun baza karairayi wai Buhari ya kawo yunwa, tare da cewa Buharin bogi ne ke shugabantar Najeriya.
An kirkiri labaran batanci a kowane bangare da manufar kawo wa 'yan takarar cikas a tsakanin masu zabe.
Sabanin yarfen da mutanen da suka ga jiya da yau a siyasar Najeriya, wato al'amarin da ake karkare shi a kan duro wajen taron siyasa da 'yan wake-wake, yanzu kuwa lamarin bazawa ake yi a shafukan sada zumunta na intanet.
Buhari
Dan takarar jam'iyyar APC, Shugaban kasa mai ci, Muhammadu Buhari, ya sha yarfen siyasa, cewar "tafiyar hawainiya da harkokin mulki, wato lakabin "Baba go slow."
Kuma ana ta baza cewa gwamnatin Buhari ce ta kawo yunwa, don haka 'yan adawa ke ikirarin cewa su za su kori yunwar.

Asalin hoton, Getty Images
Hasali ma da ya shafe watanni hudu a birnin Landan da ke kasar Birtaniya, inda ya yi jinya, sai aka yi ta baza rade-radin cewa ya mutu.
Bayan ya dawo aka ci gaba da ce-ce-ku-ce. Sannan da karatowar zaben 2019 sai aka rika cewa wai an musanya shi da Jibiril Sudan, kamar yadda aka ruwaito daga bakin Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutikar yankin Biyafura.
'Yan adawar har cewa suke yi yaki da cin hanci da rashawa da ya himmatu ka'in da na'in akwai son rai a cikinsa, inda ake ganin daukacin wadanda hukumar EFCC ke tuhuma da dama 'yan PDP ne.
Ci gaba da tsare tsohon mai ba da shawara kan harkar tsaro, Kanar Sambo Dasuki da tsohuwar Ministar Man fetur Diezani Alison-Madueke da wasu tsoffin gwamnonin PDP.

Asalin hoton, Getty Images
Atiku
A bangaren abokin karawarsa, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, 'ya'yan jam'iyyar APC da masu adawa da shi sai bankado yadda aka yi gwanjon kamfanonin kasar da watandar dukiyar al'umma a mulkin jam'iyyar PDP na shekaru 16.
A hirar da Ja-gaban na 'yan APC Bola Ahmed Tinubu ya yi da manema labarai cikin Janairun bana, ya yi ikirarin bambancin da ke tsakanin Shugaba Buhari da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku.
A cewarsa: "Halayyar 'yan takarar biyu ta bambanta. Shugaba Buhari mutum ne mai magana ta gaskiya kai tsaye."
"Domin idan ka bai wa Buhari damin Naira lokacin da yake rike da tsintsiyar shara, tabbas za ka dawo ka iske kudin a teburin da ka aje su."
"Idan Buhari ya ce 'E,' ko 'a'a' ka san matsayarsa; ya tsaya ne kan ra'ayinsa na gaskiya ba sauyi. Atiku kuwa al'amuransa a gauraye suke.
"Idan Atiku ya yi magana, ta yi wu 'E,'ko 'Aa'' 'ta yi wu,' ko ban sani ba,' dawo gobe,' 'daukacin al'amuran, ko babu ko daya daga cikinsu' yake nufi," in ji shi.

Asalin hoton, Getty Images
Malam Hassan Muhammad Lamin, Malamin Addini a Kano, ya yi nuni da cewa, wannan ita ce takaddamar da ake amfani da ita wajen karya lagon dan takara.
Shi ya sa ma a da za ka ji tsakanin PRP da NPN, jam'iyyun da suka yi karfi a Arewacin Najeriya a Jamhuriyya ta biyu, mawaka suka yi ta wake-wake:
"Wa ya kara kudin Omo da sabulu da mai mai gurguwa NPN!"
"Mai dara maye ne, mai zanna bukar angon jaka!"
Yada kage da yin yarfe don kassara abokin hamayyar takarar siyasa ba zai taba zama abun alheri ba ga Najeriya.
Don haka duk wata manufa da dan takara ya bijiro da ita, kamata ya yi a tuntubi masana a fannin zamantakewa da tattalin arziki da harkokin siyasa, domin su ne kawai za su iya fayyace wa jama'a hakikanin abin da ya dace da su, tare da dorewar Najeriya a tsararrakinta na kasashen duniya.

Asalin hoton, Getty Images
Yarfe dai ya yi kamari, inda adawar siyasa ke kewaye da kalaman batanci ga daukacin 'yan takarar shugabancin kasar a manyan jam'iyyun PDP da APC.
Buhari dai ana ta zarginsa da lakaki da tsuke bakin aljihu da yaki da cin hanci da rashawa a kan mafi yawan 'yan jam'iyyar adawa ta PDP.

Game da Atiku Abubakar kuwa, duk da cewa a karkashin kulawarsa aka yi gwanjon kamfanonin kasar nan, wadanda suka hada da kamfanin wayar tarho na kasa NITEL da kamfanin wutar lantarki na kasa PHCN da makamantansu, amma Malam Nasiru el-Rufa'i ma na da hannu a wannan hada-hadar da aka gudanar a tsakanin shekarun 1999 zuwa 2007.
Ko da yake a ganawarsa da kwamitin Majalisar Dattijai, wanda ya bi kadin yadda aka sayar da dukiyar kasa, El-Rufa'i ya bayyana cewa: "Duk lokacin da za a sayar da wani kamfani Obasanjo da Atiku sukan tuntube shi, don ganin an sayar da kadarar ga mutanen da suke so."
Abin da dai aka fi yin yamadidi da Atiku Abubakar a kai, shi ne, irin manufarsa ta sayar da kadaddarorin kasa, al'amarin da ya tabbatar da hakan a wani rahoton da kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ya baza.
Atiku Abubakar bayyana cewa ne, zai rubanya bunkasar tattalin arzikin Najeriya nan da shekarar 2025.
A ganawar da tsohon mataimakin shugaban na Najeriya ya yi da 'yan kasuwa a Jihar Legas ya ce zai sayar da kamfanin Mai na kasa NNPC, "ko da za a halaka ni, zan aikata hakan."
"Sannan zan rubanya hada-hadar tattalin arzikin Najeriya ta kai Dalar Amurka biliyan 900 nan da 2025," kamar yadda Reuters ya ruwaito.
Ba yau aka saba yarfe ba
Tun a jamhuriya ta farko aka yi irin wannan takaddamar a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun da suka fi karfi a Arewacin Najeriya: NEPU da NPC, a cewar Malam Hassan Muhammad Lamin.
"Bata abokin hamayyar siyasa ba bakon abu ba ne a kasar nan, domin cikin Jamhuriyya ta farko aka yi ta yada batanci a tsakanin 'ya'yan jam'iyyun NEPU da NPC."
"Kuma an fi fito da munin abokin hamayya lokacin da zabe ya karato," inji shi.
Sannan a jamhuriyya ta biyu marigayi Alhaji Muhammadu Abubakar Rimi tsohon Gwamnan Kano, har Jihar Sakkwato ya je ya caccaki jam'iyyar NPN mai mulki ta Alhaji Shehu Shagari.

Asalin hoton, Getty Images
Kafafen yada labarai sun ruwaito mai Magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Buhari, Mista Festus Keyamo, yana zargin Jakadan kasar Amurka a Najeriya Stuart Symington da sauran jakadun kasashen Yammacin Turai da nuna goyon baya ga dan takarar shugaban kasa na Jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.
Jakadan Amurka tuni dai ya musanta wannan zargi, kai hasali ma dai tun a fitowar Mujallar Magama, ta Disambar 2018 zuwa Janairun wannan shekarar 2019, jakadan Amurka a sakonsa na fatan alheri game da zabukan Najeriya na 2019 ya nuna cewa: "Dan takara guda kawai Amurka ke mara wa baya, wato tsarin gudanarwa mai inganci da tsafta."
Alhaji Ishak Hadeja, wani tsohon mai gabatar da shirin talabijin tun a Jamhuriya ta biyu, mai shirin Lale-kati a gidan talabijin na CTV 67, wadda ta koma ARTV, kuma shi ne Manajan-Daraktan Hukumar Rediyo da talabijin ta Jihar Jigawa, ya bayyana cewa: "Mutanen da ba su da abin fada su ne ke yada kage da yarfen siyasa don su samu lagon abokin hamayyar siyasa."
Ishak Hadeja ya ce: "A da babu kafafen sada zumunta na intanet irin su Facebook da Whatsapp, don haka hazakar mawaka kawai ake amfani da ita; a sa su yi wa abokin hamayya shagube."
Bisa la'akari da kamarin yarfen siyasa yana bayar da shawara ga 'yan Najeriya idan sun ji yarfe ko kagen karairayi game da wani dan takara, musamman a kafafen sadarwar intanet, ka da a yi saurin yarda, har sai an auna kimar mutuntakar mutumin, ta yadda za a bambance tsakanin karya da gaskiya.












