Abin da ya sa za mu raba wa kanmu motoci - Majalisar wakilai

NATIONAL ASSEMBLY

Asalin hoton, NATIONAL ASSEMBLY

Majalisar wakilan Najeriya ta tabbatar da rahotanni da ke cewa tana shirin sayan motoci domin raba wa mambobinta.

Sai dai ta musanta cewa kuɗin kowane mota zai kai naira miliyan 200.

Mai magana da yawun majalisar Akin Rotimi shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a ranar Lahadi a Abuja, inda ya ce mutane na ta kambama batun sayo motocin wanda kuma ba sabon abu ba ne, a cewarsa.

Tun farko dai a cikin kwanaki da suka gabata an yi ta tafka muhawara kan cewa majalisar wakilan za ta sayo motoci, waɗanda kowace ɗaya kuɗinta ya kai kimanin naira miliyan 200 domin raba wa mambobin.

Duk da cewa mai magana da yawun majalisar bai faɗi kuɗi da kuma irin motoci da za a sayo ba, ya ce abin da take niyyar yi yana bisa tsarin doka, kuma majalisun da suka gabata ma sun yi haka.

Ya ce ko a mafi yawan lokuta "ana saya wa jami'an gwamnati a ɓangaren zartaswa daga matakin darekta zuwa sama, motoci na aiki a ofisoshinsu."

"Abu ne mai kyau mu fito mu fayyace wa ƴan ƙasa komai. Motocin da za a saya wa ƴan majalisa za su kasance waɗanda za a yi amfani da su wajen yin ayyukansu musamman ma na kwamitocinsu. Ba motoci ne na kashin kansu ba ko kuma kyauta," in ji sanarwar.

Majalisar ta goma, ta ce a tsawon aikin da za ta yi daga 2023 - 2027, motocin za su kasance mallakin majalisar dokoki.

"A karshen wa’adin majalisa ta goma a shekarar 2027, idan har tsarin sayar da kayan gwamnati na nan, ‘yan majalisar za su iya samun zaɓin sayen motocin daidai darajarsu a lokacin inda za su biya kuɗin a asusun gwamnati kafin su zama nasu, in ba haka ba kuma, sun zama mallakin Majalisar Dokoki ta Ƙasa."

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Al'ummar Najeriya dai na kokawa kan matsananciyar rayuwa sanadiyyar tashin farashin kayan abinci da na masarufi da ma sufuri.

Ana ɗora laifin hakan ne kan matakin cire tallafin man fetur na gwamnatin tarayyar kasar.

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya ta zargi gwamnatin ƙasar da laifin cire tallafin ba tare da ta ɗauki matakan kawo sassauci ga al'ummar ƙasar ba.

Bugu da ƙari akwai rashin yarda tsakanin al'umma da shugabanni, musamman ma zaɓaɓɓun ƴan siyasa a ƙasar ta Najeriya.

Sau da dama akan zargin ƴan siyasa da yin wadaƙa da kuɗaɗen gwamnati a maimakon gudanar da ayyukan da za su shafi rayuwar al'umma.

Sai dai kamar yadda majalisar ta bayyana a bayanin nata, motocin da za ta raba wa mamabobinta za su yi amfani da su ne wajen gudanar da ayyukan da suka shafi al'umma.

Majalisar wakilan ta ce tana so mutane su gane cewa manufar majalisar ta goma na tabbatar da aminci, mambobi sun kuduri aniyar ci gaba da yin aiki tukuru, musamman a batutuwan da suka shafi sanya ido, ciki har da kai wa ga wurare masu wahala a cikin ƙasar.

"Ko yaya wuri ya kasance mai wahalar kai wa, in dai har akwai ƴan Najeriya da ke rayuwa a wurin, ya zama tilas su samu wakilai da za su je su ga halin da suke ciki da tabbatar da cewa tallafin gwamnati ya kai gare su, da kuma ganin cewa an tafiyar da tsare-tsaren gwamanati yadda ya kamata," in ji Majalisar.

Ta ce hakan zai yiwu ne kaɗai idan aka samar da motoci masu inganci da za su kai waɗannan wurare.

Haka-kuma, majalisar ta ce tana da zimmar ganin an rage yawan kuɗaɗen gudanarwa da gwamnati ke kashewa, ganin halin da ake ciki a yanzu.

Majalisar wakilan ta ce rarraba motocin da ake sa ran yi zai taimaka wajen inganta wakilci, wayar da kan al'ummar mazaɓu da kuma ayyukan sanya ido.

Ƴan Najeriya da dama sun yi Alla-wadai da batun sayawa ƴan majalisar ta wakilai motoci, musamman ma a daidai lokacin da ƙasar ke fama da tsadar rayuwa sakamakon cire tallafin man fetur.