'Yan Majalisun Najeriya na shan suka kan ware wa kansu maƙudan kuɗaɗe daga tallafi

Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya

Asalin hoton, NIGERIA SENATE

'Yan Najeriya sun fara sukar 'yan majalisar dokokin kasar kan matakin da suka dauka na ware wa kansu Naira biliyan 70 daga cikin biliyan 500 din da suka amince a kashe wajen bai wa 'yan kasar tallafin rage radadin janye tallafin man fetur da gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu ta yi.

Ita dai Majalisar ta ce ta yi hakan ne, domin inganta yanayin aiki na sabbin mambobinta, wadanda wannan ne zuwansu na farko majalisar, don haka suna bukatar su samu don abin tasarufi kafin komi ya daidaita.

Matakin dai ya haifar da ce-ce-ku-ce da kuma martani inda kungiyar kare haƙƙin dan'Adam ta Serap ta yi barazanar kai ƙara kotu matuƙar ba a janye kuɗin da ƴan majalisar suka amince wa kansu ba.

Ita ma kungiyar CAJA, mai fafutukar tabbatar da adalci da daidaito a Najeriyar ta yi shuri da matakin, da ta bayyana a matsayin rashin tausayi ga halin da 'yan kasar suka samu kansu a ciki.

Shugaban kungiyar Kwamared Kabiru Sa'idu Dakata, ya shaida wa BBC Hausa cewa:

''Wannan abun mamaki ne, kuma ya yi wuri, a ce sun fara fito da zalamarsu a fili, tun da an zabo su ne domin su tsara dokoki da za su fitar da 'yan Najeriya daga halin kuncin da suke ciki, yanzu wasu na ganin kokari suke yi su mayar da kudin da suka kashe a lokacin yakin neman zabe'' in ji shi.

Da yake kaso 70 cikin 100 na 'yan majalisar sabbi ne, wasu daga cikinsu na korafin cewa har sun fara cin bashi, saboda rashin abin da za su yi amfani da shi wajen rike kansu, da kuma tafiyar da harkokinsu na yau da kullum.

Sai dai a cewar Kwamared Dakata, yawancinsu dama sun fi karfin abin da za su rayu da shi na yau da kullum, kuma akwai bukatar su sadaukar da kansu wajen hidimta wa jama'a, ba wai wata dama ce suka samu ta holewa ba.

Wasu bayanai dai na cewa wannan adadi na Naira biliyan 70 da 'yan majalisar suka ware wa kansu, ya zarce wanda aka ware wa manoma cikin tallafin rage radadin.

Shi ma Kwamared Awwal Ibrahim Musa Rafsanjani na kungiyar CISLAC mai sanya ido kan harkokin majalisun Najeriyar, ya ce abin da 'yan majalisar suka yi garaje ne.

''A halin da ake ciki su kansu 'yan Najeriya da dama ba sa samun abinci, ba sa iya biyan kudin makaranta, amma su yanzu daga zuwansu tun ma ba su fara aikin komai ba sun fara nema wa kansu mafita.''

Ya ce idan ma za su yi haka, da sai su jira su fara aiki a fara ganin amfaninsu ga jama'a tukuna.

Ita dai gwamnatin Shugaba Bola Ahmad Tinubu, ta ce za ta shafe watanni shida ne tana raba wa mutane miliyan 12 Naira dubu takwas duk wata, domin ganin arziki ya yadu.