Ba gudu ba ja da baya kan manufofina – Tinubu

Lokacin karatu: Minti 3

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya ce ba ya nadamar cire tallafin man fetur da ya yi a farkon kama mulkinsa.

Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Litinin da daddare, a tattaunawarsa ta farko da kafafen yaɗa labaru tun bayan hawa mulkin Najeriya a watan Mayun 2023.

Shugaban na Najeriya ya bayyana hakan ne a lokacin da aka yi masa tambaya kan 'ko da ya fi kyau idan an jinkirta cire tallafin man fetur da kuma barin kasuwa ta tantance darajar naira'.

Tinubu ya ce "babu yadda za a yi na bari ana sayar da man fetur ta yadda ƙasashe maƙwafta za su riƙa samun garaɓasa. Ba na nadamar komai game da cire tallafin man fetur.

''Muna kashe abin da za mu amfana da shi a gaba ne, muna yaudarar kanmu ne kawai, wannan sauyi dole ne, '' in ji shi.

Sannan ya kara da cewa shi ko alama bai yarda da tsarin kayyade farashi ba kuma ba zai yi hakan ba, illa dai za su yi aiki tukuru su tabbatar sun samar da man a kasuwa.

A ranar 29 ga watan Mayun 2023, lokacin jawabin karɓar mulki ne Bola Tinubu ya bayyana cire tallafin man fetur.

Masana da dama na kallon cire tallafin man fetur da barin kasuwa ta tantance darajar naira a matsayin abubuwan da suka ta'azzara matsalar tattalin arziƙi da al'ummar ƙasar suka faɗa ciki.

Tun bayan cire tallafin farashin man daga kusan naira 200 a kan lita daya zuwa sama da naira dubu daya abubuwa suka ta'azzara ga 'yan kasar kasancewar man ya damfara ga yawancin harkokin rayuwar al'ummar.

Najeriya, kasar da ta fi yawan jama'a a Afirka shekara da shekara tana fama da matsalar mai, inda kusan dukkanin matatun man fetur dinta mallakar gwamnati kusan ba sa aiki.

Wannan ya sa kasar ta dogara kusan kacokan a kan man da ake tacewa a waje, inda kamfanin mai na kasar NNPCL, ke zaman babban mai sayo man daga waje, yayin da ita kuma take sayar da nata danyen ga kasashen waje.

Haka kuma a dai wannan lokaci da gwamnatin ta cire tallafin ta kuma bar kudin kasar naira ya sama wa kansa daraja a kasuwar kudaden waje baya ga rage darajar kudin da gwamnati ta rinka yi.

Wannan ya sa darajar kudin ta yo kasa warwas daga matsayin dala daya a kan naira 700 zuwa sama da dala daya a kan naira 1600 a kasuwar bayan fage.

Wannan ma ya haifar da gagarumar hauhawar farashin kayayyaki da 'yan kasar ba su taba gani ba.

Babu gudu babu ja da baya a kan dokar haraji:

A yayin wannan tattaunawa ta musamman da manema labarai da shugaban na Najeriya ya yi ya kuma jaddada matsayinsa a kan sauyin da ya sanya a gaba a kan haraji inda ya gabatar da kudurin doka ga majalisar dokokin kasar domin ta amince ya aiwatar, dokar da ta janyo takaddama a kasar musamman kin amincewa daga yankin arewaci lamarin da ya tilasta wa 'yanmajalisar tuntuba a kai.

Wannan matsin lamba da adawa da kudurin na Tinubu ta gamu da shi daga wasu gwamnoni da sanatoci, hatta ma daga cikin jam'iyyar APC ta shugaban ya sa ya ce a shirye yake da a tattauna a kan batun, ya kuma bayar da kofar yin hakan.

Ya ce amfanin kudurin dokar nesa ba kusa ba ya dara illolinsa, inda ya kara da cewa kuduri ne da zai amfani jama'a wanda zai kare masu rauni.

Tinubu ya ce babu maganar janye kudurin domin abu ne na kishin talaka kuma zai fadada yadda ake biyan haraji, ta yadda za a samu karin jama'a da ke biya.

A dangane da wannan ma ya ce ba ta yadda zai ja da baya daga abin da yake da kyau da amfani ga jama'a.

Ya ce, ''alamar shugaba na gari ita ce iya jajircewa kan yin abin da ya wajaba ya yi a lokacin da ya wajaba a yi shi.

Najeriya na ci gaba in ji Shugaba Tinubu

Duk da irin katutun matsalolin da 'yan kasar ke fama da su na tsadar rayuwa sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin ke bullo da su, Shugaban na Najeriya, ya bugi kirji da cewa kasar na kan turbar cigaba.

Tinubu ya ce tsawon wata uku a jere ya cimma bukatun kudi na kasar ba tare da ya taba ko kwabo daga kudaden da kamfanin mai na kasar NNPCL ke samarwa ba, ko kuma karbar kudi daga babban bankin kasar, CBN ba.

''Ba zan rage yawan ministocina ba''

Shugaban na Najeriya ya mayar da martani ga masu suka da ke cewa majalisar ministocinsa ta yi yawa, inda ya ce ba zai rage yawan ministocinsa daga 48 da suke a yanzu ba.

Tinubu ya kafa hujja da cewa ya zabi ministocinsa a bisa aiki tukuru saboda haka ba shi da niyyar rage su.

A watan Oktoba na wannan shekarar mai karewa ne Shugaban ya sauya wa ministoci 10 wurare tare da nada wasu bakwai sababbi. Haka kuma ya sauke guda biyar to amma duk da haka masu suka na cewa majalisar ministocin ta yi girma da yawa.