Mutuwar jarirai da ta girgiza Turkiyya

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ege Tatlici
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Turkish
- Lokacin karatu: Minti 5
A zargin wata badaƙala da ta shafi sauya wa jariran da aka haifa a asibitoci domin kula da su - wanda ya yi sanadiyyar mutuwar aƙalla jarirai 10 - ta girigiza Turkiyya, inda ake ta kiraye-kirayen korar duka ma'aikatan da ke da hannu a badaƙalar, tare da faɗaɗa bincike.
A ɗaya daga cikin badaƙala da ta shafi lafiya mafi girma a Turkiyya, an zargi likitoci da ma'aikatan jinya da direbobin motocin ɗaukar marasa lafiya da yin ƙaryar sauya wa jariran daga asibitocin gwamnati, zuwa asibitoci masu zaman kansu 19 domin su samu kulawar da suke buƙata a tsawon lokacin da za su ɗauka a asibitocin.
A watan Nuwamban 2016, matarTolga Oymak, Nukhet ta haifi 'yan uku a wani babban asibiti da ake martabawa a Turkiyya.
Sai dai an haifi 'yan ukun a matsayin bakwaini, kuma sashen kula da bakwaini a asibitin ba shi da kwalabe ukun da za a saka duka jariran a ciki.
Don haka dole iyalan suka nemo wani asibitin da za a mayar da jarirain cikin gaggawa.
“Kwana uku bayan haka ɗaya daga ckin jariran ya mutu,'' kamar yadda Tolga ya shaida wa BBC. Likitocin sun faɗa masa cewa jaririn ya rasu ne sakamakon matsalar da ta shafi numfashi da wata cutar da ke kama jarirai 'yan ƙasa da wata uku.
“Ya rage mana saura jarirai biyu. Likitocin sun riƙa faɗa mana cewa suna cikin ƙoshin lafiya.
Kwana biyar bayan nan, likita ya kira shi tare da faɗa masa cewa ɗaya daga cikin jariran biyu ya rasu, sabo da dai wannan matsala ta numfashi, sannan ya buƙaci ya hanzarta zuwa asibitin
“Ba mu samu shiga sashen kula da bakwainin ba, amma ta cikin taga muka ga yadda jaririnmu ya rasu.''
“’Kun riga kun kashe min jarirai biyu, shi ma wannan ɗin kashe shi za ku yi? ''Na faɗa wa ma'aikacin lafiyar.''
Sai suka ce da shi ''Ka kwantar da hankalinka''.
Karya ƙa'idojin walwala
Kundin zargin mai shafuka kusan 1,400, ya nuna cewa jariran da ake kai wa ɗaya daga cikin waɗannan asibitci 19, ba sa samun irin kulawar da ta dace a wasu lokuta, don haka waɗanda ke ha hannu a shirin suna karya ƙa'idojin walwala na Turkiyya.
Gungun ma'aikatan jinyar da ake zargi da hannu a wannan zamba - da kafofin yaɗa labaran Turkiyya suka yi wa laƙabi da ''gungun masu harƙallar jarirai'' - na karɓar dala 231 a kowace rana kan kowane jariri da ya kwana ɗaya a ɗakin kula da jariran.

Asalin hoton, Getty Images
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Aƙalla jarirai 10 ake zargi sun mutu sakamakon rashin kula ko rashin iya aiki a hannun waɗancan gungun ma'aikatan lafiya.
A wannan makon ne aka gurfanar da mutum 47 a wata kotu a birnin Santambul. An kuma kama mutum 22 da ake zargi kawo yanzu.
Waɗanda ake zargin sun musanta aikata ba daidai ba, sun kuma dage cewa sun kula da jariran da kyakkyawar niyya.
Babba daga cikin waɗanda ake tuhumar shi ne Dr. Firat Sari, wanda ake tuhumar sa da laifin kafa wata ƙungiya da nufin aikata laifukan damfarar cibiyoyin gwamnati da amfani da jabun takardu da kuma kisan kai ta hanyar sakaci.
Kuma zai iya fuskantar hukuncin ɗaurin shekara 583 a gidan yari idan har aka same shi da laifukan da ake zarginsa da su.
Dr Sari - wanda ke kula da sashen kula da jarirai na wasu asibitoci masu zaman kansu da ake zargi da hannu a badaƙalar - ya musanta zargin cewa suna wahalar da jariran.
"Duk abin da muke yi, muna yin sa ne bisa tsarin doka," kamar yadda ya shaida wa masu gabatar da ƙara.
Ƙwace lasisin asibitocin
Sai dai Doğukan Taşçı, ɗaya daga cikin ma’aikatan jinya da aka kama, ta amince da wasu kura-kurai da suka haɗa da sayar da magunguna da kuma yin lissafin majinyata domin karɓar kuɗi daga hukumar lafiyar ƙasar.
"Yawan aikin sashen kula da jariran, yawan kuɗin da muke samu," kamar yadda ta bayyana a gaban kotun.

Asalin hoton, Getty Images
An buɗe shari'ar ne bayan da ƴansanda suka ƙaddamar da bincike bayan samun bayanan sirri kan wannan badaƙala a cikin watan Maris ɗin 2023.
Sakamakon binciken ya kai ga ƙwace lasisin asibitoci 10 daga cikin 19, ciki har da wani mallakin wani tsohon ministan lafiya na jam'iyya mai mulki.
Kawo yanzu fiye da iyalai 350 ne suka buƙaci a gudanar da bincike kan mutuwar jariransu, a cewar kafofin yaɗa labaran ƙasar.
Akwai kuma kiraye-kiyan ministan lafiyar ƙasar ya yi murabus tare da mayar da duka asibitoci masu zaman kansu, da aka zarga a badaƙalar, ƙarkashin kulawar gwamnati.
Shugaban ƙasar Recep Tayyip Erdogan ya ce waɗanda ke da alhakin mace-macen za su ɗaɗana kuɗarsu, amma ya yi gargaɗi game da ɗora wa tsarin lafiyar ƙasar laifi.
“Ba za mu amince a ɗora wa tsarin lafiyar ƙasarmu laifi, saboda aikin wasu ɓata-gari marasa yawa ba,” in ji shi.
‘Rayuwa cikin damuwa’
Tun bayan bayyanar badaƙalar mutuwar jariran, iyalai da dama da lamarin ya shafa sun fuskanci wata sabuwar matsalar.
“A lokacin da na fara karanta labarin badaƙalar, na kasa yin maganar da matata,” in ji Tolga.
“Ganin sunan asibitin [da jariranmu suka rasu] a cikin kanun labarai ya sake tayar min da hankali,” kamar yadda ya faɗa wa BBC.
“Ina son in sani a yaznu ko za a iya tabbatar da fargabar da muka yi a baya. Ina son tabbatar da cewa ko a baya kashe jariranmu aka yi''.
Jaririn Tolga guda da ya rage cikin ƴan ukun a yanzu shekararsa takwas. Shi da matarsa sun fitar da ran sake samun haihuwa.
“An cutar da mu matuƙa; har yanzu matata ta kasa yarda cewa ba sakaci ba ne (ya kashe jariranmu guda biyu). Don haka muna fargabar sake fuskantar makamanciyar wannan matsala idan muƙa ƙara haihuwa'', in ji shi.
*Ƙarin rahoto daga Emre Temel da Fundanur Ozturk.










