Isra'ila ta gargaɗi Erdogan kada ya bi 'sawun Saddam Hussein'

Asalin hoton, Reuters
A ranar Lahadi 28 ga watan Yuli shugabanTurkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi iƙirarin cewa Turkiyya na iya afkawa Isra'ila.
Erdogan ya ce Turkiyya za ta iya shiga Isra'ila kamar yadda ta yi a baya a Libiya da kuma Nagorno-Karabakh na Azarbaijan.
Sai dai kuma shugaban na Turkiyya bai bayyana irin kutsen da yake nufi ba.
Erdogan dai ya dade yana sukar yadda Isra'ila ke kashe fararen hula a hare-haren da take kai wa Gaza, kuma ya yi tsokacin na baya-bayan nan ne a yayin da yake jinjina wa ɓangaren tsaron ƙasarsa a wani shiri da aka gudanar.
Erdogan ya ce: ''Ya kamata mu tsaya tsayin daka saboda kada Isra'ila ta aikata munanan abubuwan da take yi wa Falasɗinawa. Yadda muka shiga Karabakh da yadda muka shiga Libya, za mu iya yin haka kan Isra'ila.''
A kan wannan tsokacin da Erdogan ya yi, Ministan Harkokin Wajen Isra'ila Israel Katz ya wallafa hotunan Saddam da Erdogan a shafukan sada zumnuta, inda ya rubuta: ''Erdogan yana bin sawun Saddam Hussein. A tunatar da shi kan abin da ya faru da kuma yadda lamarin ya ƙare''.
Erdogan ya kwatanta Natanyahu da Hitler
Erdogan ya ce: ''Babu dalilin da zai hana aiwatar da haka. Ya kamata mu tsaya tsayin daka domin mu iya ɗaukar waɗannan matakan.''
Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya nemi ƙarin bayani daga wakilan Shugaba Erdogan amma ba su ce uffan ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Bayan wannan tsokacin da Erdogan ya yi, akwai wata magana kuma da ake taƙaddama a kanta a kafafen yaɗa labaran Isra'ila.
A cewar wani rahoto na jaridar Times of Isreal, Erdogan ya kwatanta Firaministan Isra'ila Benjamin Natanyahu da Adolf Hitler.
Erdogan ya ce: ''Kamar yadda mai kisan kiyashi Hitler ya gamu da ƙarshensa, shi ma mai kisan kiyashi Natanyahu zai gamu da nasa ƙarshen.''
A cewar Times of Isreal, Ergogan ya ce: ''Waɗanda ke ƙokarin kashe Falasdinawa su ma za a tuhume su kamar yadda aka tuhumi ƴan Nazi. Ɗan'adam na tare da Falasɗinu. Ba za ku iya kashe Falaɗinawa ba.''
A lokacin mulkin Hitler, an kashe Yahudawa miliyan shida. Bayan kammala yaƙin duniya na biyu an shigar da ƙara kan jami'an Nazi kuma an hukunta su.
A ranar 7 ga watan Oktoba na 2023, Isra'ila ta ƙaddamar da aikin soji a Gaza bayan harin da ƙungiyar Hamas ta kai, inda aka kashe kimanin ƴan Isra'ila 1200.
A cewar ma'aikatar lafiyar da ke ƙarƙashin ikon Hamas, sama da Falasɗinawa 39,000 Isra'ila ta kashe a martanin da take mayarwa, akasrinsu kuma mata ne da ƙananan yara.
Erdogan ya kwatanta Isra'ila da Hitler a lokuta da dama a baya.

Asalin hoton, Reuters
Martani kan kalaman Erdogan
Tsohon Firaministan Isra'ila Yair Lapid ya mayar da martani kan kalaman na Erdogan.
''Maganar banza ce Shugaba Erdogan yake yi. Ya zama barazana ga yankin Gabas ta Tsakiya. Ya kamata duniya baki ɗaya musamman ma ƙungiyar tsaro ta Nato su yi tir da wannan barazanar kuma su dage kan ya janye goyon bayan da yake bai wa Hamas. Ba za mu lamunci barazana daga mutumin da ke son ya zama mai mulkin kama-karya ba," in ji Lapid.
An ci gaba da mayar da martani kan kalaman na Erdogan a shafukan sada zumunta na Isra'ila.

Asalin hoton, Reuters
Matsalolin da Natanyahu ke fuskanta
A baya-bayan nan Firaminitan Isra'ila Benjamin Natanyahu ya kai ziyara Amurka.
Yayin ziyarar, ƴar takarar shugaban ƙasa a jami'iyyar ɗemocrat Kamal Harris ta ce: ''Yanzu ne lokacin da ya kamata a kawo ƙarshen yaƙin kuma a yi shi ta yadda za a tabbatar da tsaron Isra'la. Ya kamata a sako duka waɗanda aka yi garkuwa da su. Ya kamata a kawo ƙarshen wahalhalun da Falasɗinawan Gaza ke fuskanta, kuma ya kamata Falasdinawa su samu damar yin amfani da ƴancinsu na walwala.''
Bayan ganawa da Shugaba Biden da Kamala Harris, Natanyahu ya kuma tattauna da Donald Trump.
Bayan wannan ganawar, Natanyahu ya ce zai aike da tawaga zuwa Roma domin tattaunawa. Trump ya dade yana iƙirari a yaƙin neman zaɓensa cewa yana zama shugaban ƙasa zai kawo ƙarshen yaƙin Gaza.
A yayin da Natanyahu ke kan ziyararsa ta Amurka, a ranar 27 ga watan Yuli, an kai wani harin roka kan Tuddan Golan da Isra'ila ta mamaye inda aka kashe mutane 12. Akasarin waɗanda suka mutu yara ne.
Bayan wannan harin Natanyahu ya ce ƙungiyar Hezbollah za ta fuskanci mummnar sakamako, bayan ya furta waɗannan kalamai ne ya katse ziyarar ta sa ya koma Isra'ila.
Natanyahu yana shan suka a kasarsa sakamakon gazawarsa na dawo da wadanda Hamas ta yi garkuwa da su a Gaza.
A halin da ake ciki, Natanyahu wanda ya koma Isra'ila bayan harin na Tuddan Golan na fuskantar barazana daga Erdogan. Sakamakon haka, zamantakewa tsakanin ƙasashen biyu na ƙara taɓarɓarewa.

Asalin hoton, Reuters
Yadda mu'amala tsakanin Isra'ila da Turkiyya ke sauyawa
An daɗe ana takun-saƙa tsakanin Turkiyya da Isra'ila, kuma yadda kalaman Erdogan ke sauyawa cikin wannan lokacin na nuni da hakan.
Akwai huldar diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu tun shekarar 1949.
Turkiyya ce ƙasar musulmi ta farko da ta fara amincewa da ƙasar Isra'ila. Amma Turkiyya ta kai suka a lokacin da Haɗaɗɗiyar daular larabawa da Morocco da Bahrain da Sudan suka amince da ƙasar Isra'ila har ma suka kulla mu'amula da ita bayan yarjejeniyar Abraham Accords
A shekarar 2005, Erdogan ya kai wata ziyar kwanaki biyu Isra'ila tare da wata babbar tawagar ƴan kasuwa daga Turkiyya.
A yayin wannan ziyarar, Erdogan ya gana da Firaministan Isra'ila na lokacin Ariel Sharon inda ya ce shirin Nukiliyar Iran ya kasance barazana ga Isra'ila da ma duniya baki ɗaya.
A shekarar 2010, dakarun Isra'ila sun afkawa wani jirgin ruwan Turkiyya inda suka kashe mutane 10. Bayan haka ne hulɗa tsakanin kasahen biyu ta fara taɓarɓarewa.
A 2014, sama da Falasdinawa 2300 ne suka rasa rayukansun a rikicin Gaza. A wannan lokacin Erdogan ya ce -''Yan Isra'ila na aibanta Hitler amma wannan ƙasar ta ƴan ta'adda ta aikata ta'asar da ta zarce ta Hitler da wannan mummunar aikin da ta aiwatar a Gaza.''
Erdogan ya kuma mai do da wata lambar yabo da wata ƙungiya mai suna 'American Jewish Congress' kan yunƙurinsa na wanzar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
Zamantakewa tsakanin ƙasashen biyu ta ƙara rugujewa a 2018 bayan Erdogan ya yi tsokaci kan matakin da Amurka ta ɗauka na mayar da ofishin jakadancinta birnin Ƙudus da kuma mutuwar wasu gomman Falasɗinawa sakamakon hare-haren Isra'ila.
Turkiyya ya kuma dawo da jakadanta daga Isra'ila.
Tun 2020, Turkiyya ta inganta dangantakarta da ƙasashe da dama a yankin ciki har da Isra'ila.











