Abin da ya sa ƙabilar Ijaw ke tsunduma jarirai a kogi bayan haihuwarsu

Me ya sa wasu mutane ke tsunduma jarirai cikin kogi?
Mutanen da ke zaune a kusa da rafi irin al'ummar Ilaje da ƙabilar Ijaw da wasu ƴan gargajiya masu bautar halittun cikin ruwa sun yi amanna cewa ruwa shi ne rayuwa kuma ba a iya raba tsakanin asalinsu da ruwa.
Matashiya...
A ƙarshen mako ne aka yaɗa wani bidiyo da ya nuna yadda aka jefa jariri cikin rafi lokacin wani bikin al'adu a jihar Sokoto, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
Wannan ne ya sa BBC ta yi bincike domin gano dalilin da ya sa wasu mutanen ke jefa jariransu a cikin rafi.
Wannan al'ada ce da ta daɗe a tsakanin al'ummar Ijaw da Ilaje da ke gefen rafi da kuma Yarabawa da suka gasgata bautar halittun cikin ruwa da suka yi wa laƙabi da Osun da kuma Oya.
Al'ummar Ilaje, Yaarbawa ne a jihar Ondo wadanda ke maƙwabtaka da al'ummomin Ijebu da Itsekiri da Ikale da kuma Apoi Ijaw. Ana kuma samunsu a yankin Douala a jamhuriyar Kamaru da Sapele a garin Warri na jihar Delta da Asejire a Oyo da kuma wasu sassan jihar Lagos.
Su kuma al'ummar Ijaw a ɗaya ɓangaren suna daga cikin ƙabilu mafiya daɗewar tarihi a a Najeriya, waɗanda kuma aka sani da “Ijo” ko “Izon” ko kuma “Ƴan Niger-Delta” wadanda su ne asalin mutanen bakin ruwa a jihohin Bayelsa da Delta da Rivers da Akwa Ibom da Edo da kuma Ondo a Najeriya.
Masana tarihi sun ce suna da alaƙa da al'ummar Oru waɗanda suka yi ƙaura daga kogin Nile da tafkin Chadi a arewa maso gabashin Najeriya.
Osun, ɗaya ne daga cikin abubuwan bautar wasu al'ummar Yarbawa, musamman wajen addu'oin neman haihuwa da ci gaban rayuwa a Kudu maso yammacin Najeriya, inda suka fi yawa a Osogbo a jihar Osun.
Sun gasgata cewa Osun ɗaya ce daga cikin matan Sango, wanda ake taruwa kowacce shekara domin bauta masa a garin Osogbo na jihar Osun.

Dalilan da suka sa al'ummar Ijaw / Ilaje ke tsunduma jarirai a kogi:-
BBC ta zanta da Chief Mrs Mercy Tansemi, wata malama kuma dattijuwa a al'ummar Bolowo ta ƙaramar hukumar Ilaje Ese Odo a jihar Ondo a kan abin da ya sa ake tsunduma jarirai cikin kogi kuma ta yi bayanin cewa al'adar ba ta yin wata illa ga jariran, kuma wata hanya ce ta sanya jariran a kan turbar sanin muhimmancin kogin.
Cheif Tansemi ta ce: “Tsunduma jariran mu cikin kogi al'ada ce mai matuƙar muhimmanci gare mu al'ummar Ijawa''.
Ta ce al'ummar Ijaw da ta Ilaje suna zaune ne a wuraren da ke kewaye da koguna domin haka suna buƙatar sabawa da ruwa tun daga yarintar su.
Tansemi ta kuma yi bayanin cewa ana bari jariran su ɗan yi ƙwari kafin a tsunduma su a cikin kogin, kamar idan sun yi watanni biyu haka.
Ta ce a bisa wannan al'ada ne yaran suke tashi cikin sabo da shiga cikin ruwa tun kafin girman su.

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Abin da ya sa masu bautar Osun ke tsunduma jarirai a cikin ruwa:-
BBC ta kuma tuntuɓi Oloye Ifayemi Elebuibon, wani basaraken Yarbawa domin sanin abin da ya sa masu bauta a Osun suke bin irin wannan al'ada.
Ya yi bayanin cewa kowanne iyali a ƙasar Yarbawa suna da tasu al'adar, wadda suke ƙoƙarin garin ƴaƴansu sun tashi da ita.
Elebuibon ya ce al'adar tsunduma jarirai cikin ruwa ta zama ruwan dare a cikin yarbawa, musamman iyalan da ke bautar Osun da suka yarda cewa sanya jariran cikin ruwan saboda hanya ce ta jaddada imanin da bautar halittun cikin ruwa.
Ya ce: “Tsunduma jarirai cikin kogin hanya ce ta koya masu yanayin bautar iyalan su, masu bautar Osun”.
Ya bayyana cewa ta haka ne yara suke tashi da sanin yadda al'ada da addinin iayayen su suke, kuma al'adar bata da wata illa, domin dattawan mata ake bai wa jariran sun tsunduma a kogi. Ya kuma ce ba a bari jariran sun nutse sosai ikin ruwan.
Ifayemi Elebuibon ya ce ta wannan hanya ake koya wa ƙananan yara al'adu da adnin iyayen su, kuma ana yin wannan al'ada ne yayin da jariri yake da watanni biyu zuwa shida.

Asalin hoton, @Yemi Elebuibon
Kammalawa:
Bayan amfani da wannan hanya wajen tabbatar da al'ada a tsakanin wasu Yarabawa, akwai kuma masu amfani da tsunduma jariran cikin kogi a matsayin hanyar tantance ko waye mahaifin na asali, kamar dai yadda a zamanance ake yin gwajin ƙwayar halitta na DNA wajen tantance mahaifin jariri.
Sai dai dukkan hanyoyin ba su da wani tushe a tsarin kimiyya, kuma tuni wasu daga ciki suka fara gushewa.











