Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
'Rashin manufofi ne ke jawo kalaman ɓatanci tsakanin Atiku da Tinubu'
'Yan takarar shugaban ƙasa na manyan jam'iyyun siyasa a Najeriya na jefa wa junansu zarge-zarge game da lafiyarsu da kuma cin hanci da rashawa yayin da ya rage saura kwana 43 a gudanar da babban zaɓen ƙasar na 2023.
Tawagar yaƙin neman zaɓen Bola Tinubu na jam'iyyar APC mai mulki ce ta fara sukar Atiku Abubakar, na babbar jam'iyyar adawa ta PDP, tana mai cewa ba shi da lafiyar jagorantar Najeriya.
Tinubu ya ce ya kamata 'yan Najeriya su ji da lafiyar Atiku domin su yana da cikakkiyar lafiyar gudanar da mulki.
Da suke mayar da martani, tawagar kamfe ɗin Atiku ta zargi Tinubu da aikata cin hanci da rashawa, tana mai cewa "Tinubu kansa shi ne cin hanci".
Atiku wanda tsohon mataimakin shugaban ƙasa ne daga 1999 zuwa 2007, yana da shekara 76 da haihuwa.
Shi kuwa Tinubu, wanda tsohon gwamna ne a Jihar Legas tsawon shekara takwas daga 1999 zuwa 2007, shekararsa 70 da haihuwa.
An daɗe ana tafka muhawara kan ƙoshin lafiyar 'yan takarar shugabancin ƙasa a Najeriya, inda Shugaba Buhari da ke mulki a yanzu ya shafe watanni yana jinya a Birtaniya a wa'adin mulkinsa na farko.
Tuni 'yan takarar suka fara karaɗe lungu da saƙo don yaƙin neman zaɓe, inda Tunubu ya ziyarci Jihar Enugu a ranar Laraba, shi kuma Atiku ya tafi Birtaniya duka don neman ƙuri'a a gida da wajen ƙasa.
End of Wasu labaran da za ku so karantawa
Ya kamata Atiku ya faɗi gaskiya kan lafiyarsa - Tawagar Tinubu
Cikin wata sanarwa da tawagar yaƙin nema zaɓen Bola Tinubu na APC ta fitar a ranar Laraba, sun zargi Atiku Abubakar na PDP da ɓoye ainahin ƙoshin lafiyarsa da kuma cin hanci.
"Lokaci ya yi da Atiku Abubakar zai faɗi gaskiya game da abu biyu: ƙoshin lafiyarsa da kuma yadda ya haɗa baki da tsohon mai gidansa Olusegun Obasanjo wajen sace dukiyar Najeriya," a cewar sanarwar da mai magana da yawun tawagar ya fitar, Bayo Onanuga.
Mista Onanuga ya ce tawagar Kamfe ɗin Atiku na ɓoye batun lafiyar ɗan takararsu ta hanyar ƙirƙirar ƙarairayi kan nasu ɗan takarar.
"Atiku ne ɗan takarar da 'yan Najeriya ya kamata su damu a kansa. Ƙarairayi na tsawon lokaci da sauran hanyoyin kawar da hankali sun daina aiki yanzu.
"Tabbas Atiku ba shi da lafiya kuma hanyoyin da ake bi wajen ɓoyewa sun yi kaɗan."
Tinubu kansa shi ne cin hanci - Tawagar Atiku
Da ya ke mayar da martani game da zarge-zargen, kakakin tawagar kamfe ɗin Atiku da abokin takararsa Kashim Shettima Kola Ologbondiyan, ya ce abin dariya ne game yadda APC ke yi wa ɗan takararsu ƙagen rashin lafiya.
"Kazalika, shashanci ne yunƙurin da Tinubu ya ke yi, wanda ya yi shuhura da zama cin hanci shi kansa, na ɓata sunan ɗan takarar PDP," in ji shi.
Sanarwar ba ta gushe ba sai da ta zargi Tinubu da mu'amala da miyagun ƙwayoyi.
A siyasar Najeriya, ba sabon abu ba ne 'yan takara su dinga jifan junansu da manyan zarge-zarge irin waɗannan a bainar jama'a.
Sai dai kuma ba za a taɓa ganinsu tare suna ce-c-eku-ce a juna ba ballantana rikici.
'Rashin manufofi ne ke jawo waɗannan zarge-zarge'
A kowace irin dimokuraɗiyya, manufofin ɗan takara game da yadda zai sauya rayuwar al'ummarsa ne ke sakawa masu jefa ƙuri'a su zaɓe shi don ya yi nasara.
Sai dai rashin irin waɗannan manufofi ne ke jawo irin waɗannan munanan zarge-zarge tsakanin PDP da APC a Najeriya, a cewar Farfesa Kamilu Sani Fagge, wani masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero ta Kano.
"Wannan al'amari ya nuna irin yadda siyasarmu take, saboda 'yan takarar ba su da wani tsari na tunkarar matsalolin da suka addabi ƙasa shi ya sa ake ta zargin juna da kalaman ɓatanci da siyasar banga," in ji shi.
Farfesa Fagge ya ce irin waɗannan kalamai ba za su yi wani tasiri ba a kan masu zaɓe.
"Ba zai sauya ra'ayin wani mai jefa ƙuri'a ba don ya zaɓi wani takara."
Haka nan, masanin kimiyyar siyasar na ganin cewa kalaman za su ƙara zafafa yayin da zaɓe ke ƙara ƙaratowa, "amma da zarar an yi zaɓe sai ka ji shuru, a bar magoya baya da cecekuce".
Hukumar zaɓe ta Independent National Electoral Commission (Inec) ta ce 'yan Najeriya miliyan 93.4 ne suka yi rajistar kaɗa ƙuri'a a zaɓen na watan Fabarairu.
Za a jefa ƙuri'a a ranar 25 ga wata don zaɓar shugaban ƙasa da 'yan majalisar tarayya, kafin a zaɓi gwamnoni da 'yan majalisar jiha a cikin watan Maris.