Yadda ake fafata yaƙin Isra'ila da Gaza a shafukan sada zumunta kamar TikTok

Social media
    • Marubuci, Daga Marianna Spring
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC disinformation and social media correspondent

Matashi ko tsoho. TikTok ko dandalin X. Mai goyon bayan Isra'ila ko mai goyon bayan Falasɗinawa. Shafinka na sada zumunta ya keɓenta da kai. Ko suna iya sarrafa yadda kuke ganin yaƙin Isra'ila da Gaza?

Sa'ar da na buɗe shafina na TikTok, bidiyo guda biyu ne ya buɗe, ɗaya bayan ɗaya. Na farko yana nuna sojojin Isra'ila huɗu suna rawa riƙe da bindigoginsu, sun ɗaga bakunansu suna kallon shuɗin sararin samaniya. Ɗayan kuma na wata matashiya ne tana magana daga cikin ɗakinta, da wani fitaccen taken rubutu na goyon bayan Falasɗinawa.

Tsarin lissafin TikTok ne, zai tantance wanne irin bidiyo nake son gani, sannan ya ba da shawarar irinsa, bisa la'akari da bidiyon da na kalla a cikin biyun can har zuwa ƙarshe.

Irin wannan tsarin lissafi ne kuma yake aiki a sauran dandalin shafukan sada zumunta, hakan dai na nufin ana tura ƙara ingiza masu amfani da shafukan sada zumunta ne zuwa ga tabbatattun bidiyo game da Isra'ila da Gaza da kawai suke sanya hange da ra'ayoyin son ransu kafewa a wuri ɗaya.

Hakan abin la'akari ne saboda zantuka a shafukan sada zumunta na iya yin tasiri kan ra'ayin jama'a - har ma a saba da kalaman gugar zana waɗanda za su iya fita wajen shafukan sada zumunta, su ingiza zanga-zanga da ma abin da ya fi haka.

Irin wannan kuwa, har da a Birtaniya, inda dandalin sada zumuta ga alamu suka ƙarfafa gwiwar mutane masu yawa waɗanda akasari ba su damu da harkar siyasa ba, wajen ɗaukar mataki.

Layla Moran, 'yar majalisa daga jam'iyyar Liberal Democrat wadda mahaifiyarta Bafalasɗiniya ce, ta faɗa min cewa ita da sauran 'yan siyasa suna samun "ɗumbin shigowar" saƙonni ciki har daga matasa da ke buƙatar a tsagaita wuta. Ga alama, suna samun ƙaimi ne saboda"Bidiyon TikTok da na Facebook reel waɗanda ake aikawa ta dandalin WhatsApp".

"Duk wani abu da ya fita fes ya yi tsari, abu na farko da zuciya za ta raya maka - kada ka yarda da shi. Suna tsammanin labaran ƙarya ne daga masu yaɗa farfaganda," 'yar majalisar mai wakiltar Oxford West da Abingdon ta ce.

Ɗan majalisa na jam'iyyar Conservative, Andrew Percy, mataimakin shugaban ƙungiyar Abokan Isra'ila 'Yan Kwanzabatib, ya ce yaƙi "bai samu tattaunawa sosai da shiga bakunan mutane ba", a mazaɓarsa kamar sauran batutuwa.

Sai dai, ya ce: "Mafi yawan bidiyon da ake yaɗawa wani abu mai matsala shi ne na ƙin jinin Yahudawa ne. Wannan kuwa, babbar matsala ce tun ma kafin a fara wannan yaƙi - sai kuma a wannan karo, dandalin sada zumunta suka sanya faruwar hakan cikin hanzari."

Bambance-bambancen TikTok

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

To, me ya fi jan hankula a TikTok, kuma su wa yake ja?

Shafina na TikTok a ko da yaushe cike yake da bidiyo waɗanda ƙarara na goyon bayan Isra'ila ko na goyon bayan Falasɗinawa ne - inda kowanne ɓangare sau da yawa yake sukar ƙunshin bidiyon ɗan'uwansa. Bidiyon goyon bayan Falasɗinawa ne ga alama ya fi samun karɓuwa a wajen masu shafukan sada zumunta 'yan bana-bakwai - matasan da aka haifa daga 1997 zuwa 2012.

An kalli bidiyon TikTok mai amfani da taken "istandwithisrael" wato ina goyon bayan Isra'ila, fiye da sau miliyan 240, idan an kwatanta da wanda aka kalla fiye da sau miliyan 870, da taken "istandwithpalestine" wato ina goyon bayan Falasɗinawa.

Wannan haka yake har a sauran dandalin sada zumunta masu nuna bidiyo da ke da farin jini ga matasa.

Da yawan waɗannan bidiyo, an wallafa su ne tun lokacin da Hamas - wadda Birtaniya da sauran gwamnatoci suka haramta ta, a matsayin ƙungiyar 'yan ta'adda - ta kai wa Isra'ila hari ranar 7 ga watan Oktoba, amma akwai wasu da suka gabaci wannan lokaci.

Akwai ƙwaƙƙwaran bambanci na abin da ke ƙunshe a bidiyon goyon bayan kowanne ɓangare da ya fi samun karɓuwa.

Social media
Bayanan hoto, Bidiyon TikTok video daga mai wallafa bayanai a shafukan sada zumunta daga fagen yaƙi a Gaza

Ga misali, bidiyon da masu wallafe-wallafe da ke fagen yaƙi a cikin Gaza - da waɗanda masu shafukan sada zumunta da ke goyon bayan Falasɗinawa ke sharhi a kan yaƙin Isra'ila da Gaza daga ɗakunan barcinsu - suna tunzura martanin da aka fi buƙata a tsakanin matasa masu shafukan sada zumunta.

A lokaci guda, bidiyo daga sojojin rundunar tsaron Isra'ila sun fi bayyana cikin sigar ƙwarewa, kuma ya fito daga kafa amintacciya - a ƙoƙarin ganin ya shiga sahun bidiyo mafi tashe.

Social media
Bayanan hoto, Bayanan da Rundunar Sojin Isra'ila take wallafawa a wasu lokuta yakan ambaci taken bidiyo masu tashe a TikTok - kamar dai wannan da ake kira "girl math"

Abin tambayar dai shi ne ko yaya yawan bidiyon da kowanne ɓangare - kama daga gwamnatin Isra'ila ko Hamas, wadda ke mulkin Gaza - da suke ƙarfafa gwiwa ko ma ba da umarnin fitarwa.

Ƙiyayya da raba kawuna

Na bi diddigin 'yan Tiktok da yawa don samo ƙarin bayani, a cikinsu har da wani sojan Isra'ila da ake kira Daniel.

An kalli bidiyonsa da ya fi tashe sau miliyan 2.1, inda yake nuna shi tare da wasu sojoji guda uku - da a yanzu haka ke aiki da rundunar sojin ƙasar - suna rawa ɗauke da bindigogi kwanaki da dama bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba.

Tun daga sannan, masu kallon bidiyonsa sai suka yi ta ƙanƙancewa, zuwa kamar abin da bai fi sama da 10,000 ba kowanne, amma dai babu wani abu kamar miliyan biyun farko.

Yana da 'yar rikitarwa a yi hasashen lokacin da bidiyo yake yin tashe a TikTok.

Samun raguwar masu kallo ba ƙaƙƙautawa na iya nuna cewa masu amfani da shafukan sada zumunta ba sa haba-haba da waɗannan bidiyo kamar a baya - musamman yayin da tashin hankali ke rincaɓewa a Gaza - kuma sanadin haka ba a tuttura irin wannan bidiyo don su zagaya sosai da sosai.

Sannan kuma abin lura ne cewa yawan masu kallon bidiyo, ba lallai yana nuna yadda ya samu karɓuwa ba ne. Ana iya yaɗa bidiyo kuma a yi ta caccakar sa. Masu amfani da Tiktok sau da yawa sukan haɗa bidiyo - inda suke sake wallafa shi, a gefe guda kuma da nasu bidiyon suna mayar da martani.

Na lura da faruwar hakan a wasu daga cikin bidiyon Daniel. A duka bidiyon da wasu suka sake wallafawa tare da nasu, da kuma a sharhin da suke yi a ƙasan bidiyon Daniel, mutane na nuna cewa bidiyon rawarsa, cin fuska ne ga fararen hula da ake kashewa a Gaza. Wani ya yi sharhi da cewa "maras kunya" yayin da wani kuma ya ce: "Da haka dai kuke nuna muguntarku a idon duniya."

Daniel ya faɗa min martanin da yake samu a bidiyonsa sun rabu gida biyu a tsakanin "masu goyon baya" da kuma waɗanda ke nuna tsana da kuma, a wasu lokutan ma, har da zagin ƙin jinin Yahudawa.

Kalaman zage-zagen ga bidiyon nasa, da sauran abubuwan da ake wallafawa game da Isra'ila, sun haɗar da sharhin wasu shafuka masu nuna goyon bayan Falasɗinawa waɗanda bisa ƙarya suke iƙirarin cewa mutanen da aka sace ranar 7 ga watan Oktoba, taurarin fina-finai ne da aka biya su ko kuma dakarun Isra'ila ne suka kashe su.

"Martanin ƙiyayyar da ake nuna min, ni dai ba sa damuna saboda, na farko dai ban aikata wani abu ba daidai ba, [kuma] na biyu kuma mutane a faɗin duniya sun duƙufa a kan tsanar Isra'ila don haka duk ba ya damuna," Daniel ya bayyana.

Yayin wata ganawa a baya-bayan nan da manyan jami'an Tiktok, wani tauraron fim Sacha Baron Cohen ya zargi dandalin da "kafa matattarar ƙin jinin Yahudawa mafi girma, tun bayan gwamnatin 'yan Nazi". Ba shi kaɗai ba ne fitaccen Bayahuden da ya bayyana irin wannan damuwa ba, tun bayan hare-haren 7 ga watan Oktoba.

A wani saƙo da ya wallafa a baya-bayan nan, TikTok ya ce: "Tsarin lissafinmu da ke bayar da shawara kan bidiyon da mutum zai gani, ba ya 'nuna bambanci' kuma akwa matakai ƙwarara da aka shimfiɗa don hana yin almundahana."

Kamfanin mai mallakar dandalin sada zumuntar ya kuma faɗa mana cewa daga ranar 7 ga watan Oktoba zuwa 17 ga watan Nuwamba, ya cire bidiyo sama da 1.1 daga yankin da ake yaƙi saboda saɓa dokokinsa - ciki har da bidiyon kwarzanta Hamas da kalaman nuna ƙyama da ta'addanci da kuma yaɗa kalaman ƙarya.

Tsare-tsarensa sun hana wallafa "bidiyon da ke yayata ƙin jinin Musulunci ko ƙin jinin Yahudanci", waɗanda TikTok ya ce yana ɗaukar mayaki a kai.

Da na dubi bidiyon goyon bayan Falasɗinawa, wasu masu ƙirƙirar bidiyon suna da salo na daban.

Ariana, wadda ke yaɗa bidiyon yaƙi daga gidanta da ke Amurka, sau da yawa takan yi magana ne kai tsaye a cikin kyamara daga ɗakin barcinta. Takan ba da ra'ayinta a kan wallafe-wallafen bidiyo masu alaƙa da yaƙi daga fitattun mutane ko kuma a kan hotunan da ke fitowa daga Gaza.

Social media
Bayanan hoto, Hoton bidiyon TikTok daga Daniel (a hagu) da kuma Ariana

"Karon farko da na fara wallafa bidiyo game da Falasɗin [bayan 7 ga watan Oktoba], mutanen da ke kallon bidiyona sun ragu. Na rasa ɗumbin masu bibiya," Ariana ta faɗa min, ta bayyana sukar da ta fuskanta daga masu shafukan da ke goyon bayan Isra'ila.

Sai dai, ta fara samun ƙarin masu bibiyar bidiyonta a TikTok cikin makonnin da suka biyo baya, lokacin da ta fara wallafa abubuwan da ta yi imanin farfagandar Isra'ila ce.

"Mutane suka fara binciko bidiyona, kuma nan da nan lambobi suka yi ta hauhawa," in ji ta.

Ta ce mafi akasari, ta riƙa "samun ɗumbin goyon baya" a intanet ne, musamman daga mutanen da suke "jin kamar ba za su iya aminta da kafofin yaɗa labarai na al'ada ba".

Amma kuma ta gamu da ƙyama daga masu ƙin jinin Musulunci, ba kawai a TikTok ba - har ma a Instagram da sauran shafukan sada zumunta.

Da Daniel, da Ariana duka sun ce babu wani ɗan siyasa ko wata ƙungiya da ke ɗaukar nauyin bidiyon da suke wallafawa.

Wasiƙar Osama Bin Laden

A duk lokacin da masu shafukan sada zumunta suka yi ta tura wani abu da aka wallafa da ke tabbatar da wani bayani, yana zama abu mai sauƙi a fahimci yadda ƙarin tsauraran aƙidu ke iya fara samun karɓuwa.

Hakan ta faru kwanan nan a TikTok, lokacin da matasa 'yan bana-bakwai da dama suka fara yayata "Wasiƙa ga Amurka" daga Osama Bin Laden tun a shekara ta 2002 - wadda ya rubuta don kafa hujjar kai hare-haren ta'addanci na 11 ga watan Satumba, da suka halaka mutum 3,000 a Amurka.

Irin waɗannan abubuwan da aka riƙa wallafa suna nuna cewa tunanin Bin Laden ba zai kasance maras tushe ba, kuma sun riƙa ba da madadin hange a kan ruwan da tsakin da Amurka ta yi a rikice-rikicen Gabas ta Tsakiya.

Amma ba sa bayani a kan ainihin kalaman ƙin jinin Yahudawa da ke ƙunshe a wasiƙar da na ƙin 'yan luwaɗi.

TikTok ya ce adadin bidiyon da aka wallafa game da wasiƙar bai kai ya kawo ba, amma ta samu kambamawa ne bayan an yi wallafa bayaninta a dandalin X, wanda a baya ake kira Tuwita. Tuni dai TikTok ya goge bidiyon tare da toshe "Wasiƙa ga Amurka" daga tsarin bincika bidiyonsa.