Zaben 2023: Shin farin-jini a shafukan sada zumunta na tasiri a lokacin zaɓe?

- Marubuci, Mustapha Musa Kaita
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Journalist
Jama'a da dama, musamman a shafukan sada zumunta a Najeriya, suna ci gaba da bayyana mamakinsu game da kayen da wasu da suka yi fice a shafukan sada zumunta suka sha a zabukan fitar da gwanin da aka gudanar a jam'iyyu daban-daban.
Sai dai masana harkokin siyasar kasar na ganin wannan ba abin mamaki ba ne ga waɗanda suka san siyasa da yadda ake yin ta - daga sama har ƙasa.
Sun bayyana cewa ko da yake shafukan sada zumunta, irin su Facebook da Twitter da makamantansu, suna taka muhimmiyar rawa wurin tallata ƴan takara da bunkasa siyasa sai dai a Najeriya wasu na zuzuta tasirin su.
Akwai wasu mutane da suka yi fice a shafukan sada zumunta waɗanda idan suka ce tak, sai ka ga dimbin mutane sun yi tsokaci a ƙasan abin da suka rubuta a shafukansu na sada zumunta, wanda hakan yake sa wasu mutane suke ganin za su iya yin tasiri a zaɓuka.
Abin da mutane da dama ba su fahimta ba shi ne, galibin mabiyan wadannan mutane na shafukan sada zumunta sun fito ne daga yankuna daban-daban na kasar, wasu ma ba a Najeriya suke ba, don haka ba za su yi tasiri kan zabukan da wadannan 'yan siyasa na shafukan sada zumunta za su fafata a ciki ba.
Alal misali, idan akwai ɗan siyasa a jihar Filato da ke da mabiya miliyan guda a shafin Facebook, kada mutane su ɗauka mutum miliyan guda ɗin nan gaba ɗaya ƴan jihar Filato ne domin zai iya kasancewa akwai wasu daga Kaduna da Legas da Kogi da kasar Faransa da sauransu.

Wasu labaran da za ku so

Sai mutum ya ga yana da mabiya miliyan guda amma a cikin miliyan guda ɗin nan ƴan jiharsa ba su fi watakila dubu ɗari biyu ba.
Haka kuma a cikin dubu ɗari biyun nan watakila masu katin zaɓe ba su wuce dubu hamsin ba; haka ma a cikin dubu hamsin ɗin nan waɗanda ke a gunduma ko mazaɓar mutum ba su wuce dubu biyu ba.
A siyasar shafukan sada zumunta, akwai wasu da ake kira sojojin-baka ko kuma ƴan social media waɗanda ba su da aiki sai koɗa ɗan siyasa da faɗin alherinsa, waɗanda kuma suke adawa da shi ba su da aiki sai faɗin alfanunsa.
Idan sojojin-baka na shafukan sada zumunta suka rika kambama alherin mutum, wasu kan ɗauka cewa shi ne zai ci zaɓe, haka kuma idan suka taso mutum gaba da faɗin sharrinsa sai a ɗauka mutum ya faɗi warwas a zaɓe.
A kwanakin baya da aka gudanar da zaɓukan fitar da gwani na jam'iyyar APC da PDP, akwai wasu sanannu a shafukan sada zumunta waɗanda ke da miliyoyin mabiya da mutum zai ɗauka adadin mabiyansu zai sa su ci zaɓe.
Alal misali, Sanata Shehu Sani, wanda ke da mabiya a shafin Twitter miliyan biyu da dubu ɗari biyar haka kuma yana da mabiya dubu ɗari uku da tamanin da biyar a shafin Facebook, wannan adadi mai yawa na mabiya bai sa daliget sun zaɓe shi ba a matsayin ɗan takarar gwamnan Kaduna na jam'iyyar PDP a zaben fitar da gwani.
Hasalima, daliget biyu ne suka zabe shi kamar yadda ya bayyana da kansa.
Akwai tsohon Hadimin Shugaba Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad, wanda shi ma yana da mabiya miliyan ɗaya da dubu ɗari ɗaya a shafin Twitter, yayin da a Facebook yake da kusan mutum dubu ɗari da sittin da ke binsa.
Bashir yana daga cikin matasa waɗanda suka shiga siyasa a baya-bayan nan kuma an yi tsammanin saboda yadda yake da kusancin da shugaban ƙasa da kuma yawan mabiyansa a shafukan sada zumunta zai taɓuka abin a zo a gani a lokacin zaɓen.
Sai ga shi bai yi nasara ba tun a zaɓen fitar da gwani na dan majalisar dokokin tarayya a jam'iyyar APC.
Shi ma Sanata Dino Melaye, dan siyasa mai yawan magana a shafukan sada zumunta haka kuma yana da mabiya miliyan uku da dubu ɗari uku a shafin Twitter inda kuma a shafin Facebook yana da mabiya miliyan ɗaya da dubu ɗari shida.
Duk da waɗannan mutanen da ke biye da shi a shafukan sada zumunta hakan bai sa burinsa ya cika ba na lashe zaɓen fitar da gwani na takarar dan majalisar dattawa karkashin jam'iyyyar PDP, domin zama sanata a karo na biyu.
Haka shi ma Mu'azu Magaji, da ake yi wa lakabi da Ɗan Sarauniya, wanda a Jihar Kano ya shahara a shafin sada zumunta kuma ana kallonsa a matsayin mai mabiya da dama da ke ba shi goyon baya a siyasance a shafukan sada zumunta.
Amma duk da haka shi ma bai samu nasara ba a zaben fitar da gwani na takarar gwamna a jam'iyyar PDP.

'Surutu kawai'
BBC ta tattauna da Dakta Abubakar Kari, Malami a Jami'ar Abuja kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, wanda ya bayyana cewa akwai ƙasashen da suka ci gaba a duniya da ke amfani da shafukan sada zumunta su yi tasiri ƙwarai da gaske wurin cin zaɓe.
Ya bayyana cewa akasari mutanen da ke zaune a ƙasashen da suka ci gaba suna da katin zaɓe kuma suna jefa ƙuri'a duk da suna amfani da shafukan sada zumunta wurin tallata ɗan takara ko kuma karanta abubuwan da ake wallafawa game da ɗan takara.
Amma ya ce wannan abin ya bambanta da halin da ake ciki a Najeriya domin kuwa da dama daga cikin masu tsokaci a shafukan sada zumunta ba sa yin zabe yana mai cewa "yawanci waɗanda suke a shafukan sada zumunta surutu kawai suka iya amma ba su da katin zaɓe kuma ba su da tasiri a jam'iyya.
"Tasirinsu kawai shi ne a yi ta muhawara ana rubuce-rubuce da kuma raha da sauransu," in ji Dakta Kari.
Ya kuma bayyana cewa ana yin siyasa ne idan kana da katin zaɓe ko kai ɗan jam'iyya ne ko kuma kai daliget ne.
"A Amurka kusan duka wanda yake yin Facebook ko Twitter ko Instagram yana da katin zaɓe, yana kaɗa ƙuri'a ko kuma shi ɗan jam'iyya ne, amma a Najeriya akasin haka ne.
"Shi ya sa tasiri ko kuma muhimmancin irin waɗannan mutane bai da yawa ko kuma ba shi da girma kamar ƙasashe irin su Amurka," in ji Dakta Kari.
Ya bayyana cewa yadda matasa da sauran jam'a ke nuna kuzari a shafukan sada zumunta da a ce za su fito a zahiri su yi haka a fagen siyasa da za su yi tasiri ƙwarai da gaske.
Ya kuma ce ƙididdiga ta nuna cewa matasa sun fi yawa a cikin masu rajistar zaɓe inda ya ce amma yawancin waɗanda suka yi rajistar zaɓen babu ruwansu da shafukan sada zumunta.












