Yadda shugaban Iran ya yi shekara ɗaya yana mulkin ƙasar cikin matsaloli

Asalin hoton, AFP via Getty Images)
- Marubuci, Aydin Salehi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC World Service
- Lokacin karatu: Minti 6
Lokacin da Masoud Pezeshkian ya ya fara mulki kwana ɗaya bayan rantsar da shi a matsayin shugaban ƙasa a watan Yulin 2024, da rikice-rikicen siyasa da sauran matsaloli ya yi sallama.
Jim kaɗan bayan rantsar da shi ne kwatsam aka samu labarin kashe Ismail Haniyeh - jagoran ƴan Hamas, wanda kuma ya halarci rantsuwar. Kuma an kashe shi ne a wani harin jirgin sama - ba a Gaza ba - amma a tsakiyar birnin Tehran. Iran ce kan gaba wajen taimakon ƙungiyar Hamas da kuɗi da makamai da harkokin siyasa.
Kashe jagoran ƙungiyar ya ɗaga hankali a ƙasar da ma yankin baki ɗaya, sannan ya buɗe ƙofar shiga shekarar wadda ke cike da ƙalubale a tarihin ƙasar ta Iran.

Asalin hoton, Iranian Presidency handout via Getty Images
Matsaloli
Pezeshkian ya samu mulki ne bayan jimamin da ƙasar ta shiga na rasuwar shugaban ƙasar Ebrahim Raeisi tare da ministan harkoki wajenta a haɗarin helikwafta, lamarin da ya sa dole aka gudanar da babban zaɓe a ƙasar ba tare da shiri ba.
A wannan yanayin ne, Pezeshkian, wanda likitan zuciya ne, kuma tsohon ministan lafiya, sanna tsohon ɗanmajalisa, ya samu damar ɗarewa karagar mulki.

Asalin hoton, Majid Saeedi / Getty Images
Yanayin mulkinsa na sassauci musamman kan tilasta saka hijabi da wasu abubuwan more rayuwa, da kuma alƙawarinsa na mayar da hankali kan sasanci maimakon yawan fito na fito da ƙasashen yamma ne suka sa aka fara tunanin akwai haske a gaba ga ƙasar wadda takunkumi da dama suka yi wa katutu.
Amma watanni bayan ya ɗare kan karagar mulki sai Isra'ila ta ƙaddamar da wasu hare-hare a cibiyoyin nukiliya na ƙasar, sannan Amurka ma ta biyo baya. Tattalin arzikin ƙasar, wanda dama yake cikin tasku, sai ya ƙara taɓarɓarewa. Ana cikin haka kuma sai rashin makamashi da rashin ruwan sha suka mamaye ƙasar.
Wannan ya sa murnar da aka fara a farkon mulkinsa a 2024 ya fara komawa ciki.

Asalin hoton, Majid Saeedi / Getty Images
Ina aka samu matsala?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Amsar wannan tambayar ita ce: A Iran shugaban ƙasa yana jagoranci ne kawai, amma ba ya mulki.
Ba kamar sauran ƙasashe ba, shugaban ƙasar Iran ba shi ba ne wanda ya fi ƙarfin iko a ƙasar. A tsarin mulkin musulunci na ƙasar, ƙarfin madafun iko ya fi yawa a hannun jagoran addini. Tun a shekarar 1989, Ayatollah Ali Khamenei ne yake riƙe da matsayin, kuma shi ne yake da iko a kan sojoji da ɓangaren shari'a da sashen tattara bayanan sirri da ma uwa-uba, harkokin wajen ƙasar.
Za a iya ce Pezeshkian ne zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, amma ƙarfin ikonsa taƙaitacce ne, saboda akwai ɓangarorin dakarun juyin juya-hali da majalisar shura da kuma ofishin jagoran addini da suke da ƙarfin iko sosai.
Ko ministocin da zai naɗa sai ya samu amincewa daga sama. Idan aka zo maganar diflomasiyya - kamar a batun makamashin nukiliya da sauran rikice-rikicen da ƙasar ke fuskanta daga ƙasashen waje, ƙarfin ikonsa ba shi da yawa, sai ya zama tamkar wani mai magana da yawun gwamnati, inda yake sanar da matsayar da ka ɗauka.

Asalin hoton, Majid Saeedi / Getty Images
Zaɓen mai muhimmanci
Akwai magana da ake yi a Iran cikin raha: "Muna so a ba mu dama mu kaɗa ƙuri'a a zaɓen Amurka - mu ne muke fuskantar matsalolin zaɓen ƙasar."
A watan Nuwamban 2024 ne wannan maganar ta ƙara yawa a bakin mutane, lokacin da shugaban ƙasar Donald Trump ya sake lashe zaɓe - lamarin da wasu suka yi tunanin shi ne zai zama matsala babba ga ƙasar.
A zamanin mulkinsa na farko, alaƙa tsakanin Amurka da Iran ya matuƙar lalacewa: Da farko ya fice daga yarjejeniyar nukiliya da ƙasar ke ciki da Iran, ya ƙaƙaba wasu takunkumi, sannan ya bayar da umarni a ƙashe Janar Qassem Soleimani, ɗaya daga cikin manyan sojojin ƙasar ƙasar.
Hakan ya sa da Trump ya sake samun mulki, sai Iran ta fara tunanin akwai matsala.
Jim kaɗan, sai Isra'ila ta ƙara ƙaimi wajen kai hare-hare a kan ƙawayen Iran da ke yankin: Hamas a Gaza da Hezbollah a Lebanon da Houthi a Yemen. Wannan ya sa shekarar ta zama shekara da ke cike da matsaloli. A wajen Pezeshkian, lokaci ne mai muni; shugaban ƙasa mai sassauci, amma ya tsinci kansa a lokacin yaƙi.

Asalin hoton, Atta Kenare / AFP via Getty Images
'Kai ba Zelensky ba ne'
Yadda ya fuskanci yaƙin ƙasar da Isra'ila wanda aka yi kwana 12 ana fafatawa ya ƙara jawo hankalin mutane. An fara yaƙin ne a ranar 13 ga watan Yunin 2025 lokacin da Isra'ila ta ƙaddamar da manyan hare-hare a ƙasar - wanda shi ne karon farko. Isra'ila ta kai hare-haren ne a birane da dama na ƙasar, inda suka kashe fararen hula da dama.
Pezeshkian ya gaza wajen suranta yadda ya dace shugaba ya tsaya da ƙafarsa a lokacin yaƙi. A daidai lokacin da aka kai hare-hare a biranen ƙasar, ake kashe manyan hafsoshin ƙasar, shugaban ƙasa, kamar jagoran addini, bai kamata ya yi gum ba. Bai yi jawabai ba, babu wani mataki mai zafi da ya ɗauka, sannan babu wata sanarwa mai ƙarfi da ya fitar ga al'umma.
Wannan ya sa wasu ƴan ƙasar suka riƙa rubutawa a kafofin sadarwa cewa, "kai ba kamar Zelensky ba ne," inda suke kwatanta shi da yadda shugaban Ukraine ya riƙa fitowa yana magana game da yaƙin ƙasarsa da Rasha.
A lokacin da ƙasar ke buƙatar ƙwarin gwiwa, sai Pezeshkian ya ɓace.
Hijab, danniya da tsaiko a harkokin walwala

Asalin hoton, ERFAN / Middle East Images / AFP via Getty Images
Har yanzu abubuwan more rayuwa a ƙasar na fuskantar ƙalubale. Zanga-zagar "Mata, rayuwa da ƴanci' na cikin abubuwan da suka girgiza ƙasar a 2022, duk an kwantar da zanga-zangar, har yanzu muradunta na nan na cigaba.
Mata na cigaba da ƙin saka hijabi, wanda suke yi duk da sun san matsalar da ke tattare da haka. Ana cigaba da kama ƴanjarida da ɗalibai da masu fafutika.
Pezeshkian ya yi kira da a "samu sasanci a ƙasar" tare da "girmama juna."
Ya fito fili ya bayyana cewa, "ba zan tilasta amfani da hijabi ba saboda hakan na kawo matsala ga mutanenmu."
Amma wasu ƴan Iran, musamman matasa suna ganin magana ce kawai, wadda ba ta da amfani.
Matsala a kwance
Shekara ɗaya da fara mulkin Pezeshkian, mafi yawan ƴan ƙasar canji kaɗan suka gani. Farashin kayayyaki ya hauhawa, sannan babu wani sauƙi da aka samu wajen ƴancin ƴan siyasa, sannan saɓani da ke tsakanin gwamnati da al'umma na ƙara faɗi ne.
Shugaban zai iya bayyana buƙatar haɗin kai - amma haɗin kai ba a baki kawai ake yi ba, musamman ganin ƙarfin ikon tabbatar da hakan ya fi ƙarfinsa.
Iran na fuskantar wasu matsaloli da suke kwance: a ɓangaren diflomasiyya da tattalin arziki. Idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, masana suna ganin matsalolin da ƙasar za ta fuskanta ba daga takunkumi ba ne na ƙasashen waje, a'a, matsalolin ne za su iya tasowa daga cikin gida.











