Ko Tinubu na rasa goyon bayan Arewacin Najeriya ne?

Tinubu

Asalin hoton, Bayo/x

Lokacin karatu: Minti 5

Da alama tsuguno ba ta ƙare ba dangane da irin lallashin da shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu yake ta fama yi wa ƴan arewacin ƙasar wajen nuna cewa yana tare da yankin, a daidai lokacin da alamu ke nuna yana buƙatar sake tsayawa takara a 2027.

Ƴan arewacin ƙasar dai na dab da aminta da cewa shugaba Tinubu yana nufin yankin da alkairi musamman bisa duba da irin karramawar da ya yi wa tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari lokacin da rasuwar da aka ce ba a taɓa yi wa wani shugaba ba a Najeriya.

To sai dai kalaman da ke fitowa daga bakunan ƙungiyoyi da ƴansiyasar yankin a baya-bayan nan na nuni da cewa akwai sauran rina a kaba.

Masu lura da al'amuran yau da kullum na yi wa da taron kwana biyu da gidauniyar tunawa da Sardaunan Sokoto ta shirya a Kaduna da wani yunƙurin gwamnatin na ankarar da al'ummar yankin dangane da irin aikace-aikace da gwamnati Tinubu ke yi musu.

Taron ya ƙunshi jami'an hukumomin gwamnatin tarayya da ƴan yankin arewacin ƙasar ne inda suka kwashe kwana biyu suna fayyace wa mahalarta taron irin rawar da gwamnatin Tinubu ke takawa a yankin a tsawon shekaru biyu na mulkinta.

Ƙungiyar ACF ta fusata

Tinubu

Asalin hoton, Bayo/X

Ƙungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ACF ta zargi gwamnatin Bola Tinubu da nuna son kai da shakulatin ɓangaro da yankin arewacin Najeriya, a kasafin kuɗin ƙasar da ma ayyukan raya ƙasa duk da irin goyon bayan da gwamnatin ta samu a zaɓen 2023.

Shugaban kwamitin amintattun na ƙungiyar, Alhaji Bashir Ɗalhatu na daga cikin mutanen da suka gabatar da ƙorafin yankin.

"Abin mamaki waɗanda ba su goyi bayansa ba, ba su zaɓe shi ba....sun yi ƙoƙarin saka shinge tsakaninsa da Arewa.

Misali, daga cikin naira tiriliyan 1.013 da aka ware wa titunan a cikin kasafin kuɗi na yanzu, naira biliyan 24 ne kacal wato ƙasa da kaso 1, aka ware ga ayyuakan a Arewa maso Gabas."

Tsohon ministan ya kuma nuna damuwarsa dangane da irin rashin ci gaba da yankin ke fuskanta dangane da kayan more rayuwa da kuma harkar noma.

Kwankwaso ne ya fara zunguro gidan rina

Kwankwaso

Asalin hoton, Kwankwaso/x

Tsohon gwamnan jihar Kanox, Rabi'u Musa Kwankwaso dai shi ne ɗan siyasa daga arewacin Najeriya da ya fara zargin gwamnatin Tinubu a bainar jama'a da nuna wariya ga yankin.

Kwankwaso ya yi kalaman ne a lokacin wani taron masu ruwa da tsaki kan gyaran tsarin mulki a birnin Kano, inda ya nusar da gwamnatin tarayya dangane da matsalolin tsaro da na tattalin arziƙi da zamantakewa- da yankin ke fama waɗanda ya ce sakamakon nuna wa yankin wariya ne.

"Bayanai da muka samu na nuna cewa kamar rabin kasafin kuɗi na tafiya zuwa wani ɓangare guda a ƙasar nan.

Bari in bai wa waɗanda ke ƙoƙarin yin duk mai yiwuwa wajen ɗaukar komai, su tuna cewa wasu batutuwan da muke ciki a ƙasar nan a yau suna da alaƙa da rashin isassun kuɗaɗe da kuma almubazzaranci da wasu ke yi." In ji Rabi'u Musa Kwankwaso.

Ba mu ga komai ba - Babachir

Shi ma tsohon sakataren gwamnatin Najeriya lokacin shugaba Buhari, Babachir Lawal ya ƙalubalanci gwamnatin bisa abin da ya kira gazawarta na samar da "ayyukan cigaba da za ta iya nunawa a yankin" na arewa.

Babachir ya shaida hakan ne yayin hira da gidan talbijin na Channel a shirinta na siyasa "Sunday Politics" na ranar Lahadi.

"Babu wani aiki da ake yi a arewa tunda ba mu gan su a ƙasa ba. Wataƙila suna sauwala yin aikin ne mu dai ba mu sani ba." In ji Babachir.

Martanin gwamnati

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Tun dai bayan kalaman tsohon gwamnan Kano, Rabi'u Musa Kwankwaso da sauran ƴan siyasar yankin gwamnatin Tinubu ke ta fama mayar da martani.

Ko a ranar Talata a wurin taron da gaiduniyar tuna wa da Sardaunan Sokoto a Kaduna sai da mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribaɗo da sakataren gwamnati, George Akume suka musanta kallaman nuna wariya ga arewacin ƙasar.

A hirarsa da BBC, Malam Ribadu ya ce yanzu lokaci ne da gwamnatinsu ke ganin ya kamata ta fito ta bayyana irin nasarorin da ta samu a fannin tsaro.

"A baya, ƴanta'adda sukan kai hare-hare a gidajen yari da jirgin ƙasa da sansanonin soji, amma tun da gwamnatin nan ta hau mun yi maganin hakan."

"Yanzu ba wuri ɗaya da za a ce an kai harin ta'addanci tun da wannan gwamnati ta hau baya ga wanda ake yi a Borno," in ji Malam Ribadu.

Ya ƙara da cewa, sun yi nasarar kashe shugabannin ƴanbindiga da dama. Amma a cewarsa, "shugabanni da aka kashe da ake kira kacalla sun kai 300"

"Yanzu mutane da dama na zuwa gonakinsu kuma wurare da dama da a can baya ba a isa a shiga ba yanzu ana zuwa," a cewar mai ba shugaban Najeriya shawara kan sha'anin tsaro.

Shin ko arewa za ta sake zaɓar Tinubu a 2027?

Gwamnan jihar Gombe, Inuwa Yahaya ya bayar da masa inda ya ce Arewacin ƙasar zai sake bai wa shugaba Tinubu damar yin wa'adi na biyu a 2027 bisa la'akari da irin ayyukan alkairin da gwamnatinsa ke shimfiɗawa a yankin.

Inuwa Yahaya ya faɗi hakan ne a yayin taron da aka gudanar a Kaduna na ranar Talata.

"A lokacin da Bola Ahmed Tinubu yake kamfe na zaɓen 2023, ya yi alƙawura na musamman ga arewacin Najeriya. Kuma bisa imanin da shi, Arewa ta zaɓe da gagarumar ƙuri'a inda ta bayar da kaso 60 na ƙuri'un da ya samu....Kuma ayau mun ga irin ayyukan sakayya da ya yi mana....saboda haka a 2027, dole ne mu saka masa kuma abin da hakan ke nufi shi ne Tinubu ya samu goyon bayanmu." In ji Inuwa Yahaya.

To sai dai jam'iyyar haɗaka ta ADC ta mayar wa da gwamnan na jihar Gombe martani cewa ba shi da bakin da zai yi magana da yawun ƴan arewacin ƙasar.

"Gwamnonin na da damar faɗin duk abin da za su faɗa. Amma tabbas ba su ne ke da damar yin magana da yawun talakan Arewa ba waɗanda ke fama da matsalar tsaro da yunwa da jam'iyyar APPC ta ƙaƙaba musu," in ji Malam Bola Abdullahi, mai magana da yawun jam'iyyar na riƙon ƙwarya a cikin wata sanarwa ga gidajen watsa labarai.

Sharhi

Malam Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami'a da ke Kano wato CAS kuma mai nazarin kimiyyar siyasa a Najeriya, ya shaida wa BBC Hausa a kwankin baya cewa amsa tambayar ko arewa za ta sake zaɓar Tinubu ko a'a lokaci ne kawai zai tabbatar da hakan.

"To lallai al'ummar yankin suna da ƙulli ga wannan gwamnati inda suke zargin ana nuna musu wariya tsakaninsu da abokan zamansu na kudancin ƙasar. Wannan ba wani sabon abu ba ne. Su ma haka ƴan kudanci suka yi irin wannan zargi a lokacin marigayi Muhammadu Buhari." In ji Malam Sufi.

Malam Sufi ya kuma ƙara da cewa "mun ga yadda a baya-bayan nan Tinubu yake ta ƙoƙarin bayar da muƙamai ga ƴan arewa duk domin shawo kansu. To za a iya cewa har yanzu yana da dama nan da shekaru biyu wajen gyara abubuwan da suke zargin sa da shi.

Sannan wani abu shi ne ya danganta da irin mutumin da sauran jam'iyyu suka fitar domin ƙalubalantar Tinubu. Misali idan sauran jam'iyyu suka fitar da ɗantakarar da ba shi da ƙima da kwarjini a idanun al'ummar arewa, akwai yiwuwar mutanen yankin su sake zaɓensa.

Haka kuma mun san irin rawar da gwamnoni ke takawa a zabe kuma jam'iyyar APC na da mafi yawancin gwamnonin yankin duk da dai mun ga yadda a baya gwamnoni suka kasa yin tasiri a zaɓen shugaban ƙasa." In ji Malam Kabiru Sufi.