Birtaniya ta ce China barazana ce ga duniya

Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ya ce China barazana ce ga tsarin tafiyar da lamurran duniya, kuma dole ne Birtaniya ta damu da hakan.

Firaministan ya shaida wa BBC cewar yana ƙara yawan kuɗin da Birtaniya ke kashewa kan tsaro saboda “duniya na ƙara shiga cikin barazana” kuma “barazana kan tsaronmu na ƙara munana.”

Kuɗaɗen da Birtaniya ke kashewa kan tsaro zai ƙaru da kusan fan biliyan biyar a cikin shekaru biyu masu zuwa.

Mr Sunak ya faɗi haka ne a California ta ƙasar Amurka, lokacin da ya yi wata ganawa da takwarorin aikinsa na Amurka da Australia, domin cimma yarjejeniyar samar wa Australia jiragen ruwa masu tafiya a ƙarƙashin teku waɗanda ke amfani da makamashin nukiliya.

Yarjejeniyar, wadda ake kira ‘Aukus Pact’ a turance, an sanya mata hannu ne a 2021 a wani yunƙuri na daƙile ƙaruwar ƙarfin sojin China a yankin Indo-Pacific.’

Mr Sunak ya shaida wa ƴan jarida a lokacin ƙaddamar da yarjejeniyar cewa, alaƙar ƙasashen za ta sanya a samar da ‘jirage masu tafiya ƙarƙashin teku mafi inganci a tarihin duniya.’

A tattaunawar da ya yi da BBC gabanin yarjejeniyar, Mr Sunak ya ce “China ƙasa ce da ke da aƙidu da al’adu mabanbanta da namu, kuma tana barazana ga tsarin tafiyar da lamurran duniya.

“Shi ya sa yake da kyau mu kasance a ankare kuma mu ɗauki matakan kare kanmu, mu kare aƙidunmu da muradunmu.”

Ya ce gwamnatin Birtaniya ta ɗauki barazanar China da matuƙar muhimmanci kuma tana ɗaukar mataki a kai, shi ya sa ma take daƙile China ɗin daga zuba jari a wasu muhimman ɓangarori.”