Dalilan da suka sa Buhari ya samu karramawa ta musamman

Tinubu

Asalin hoton, State House

Lokacin karatu: Minti 4

Irin karramawar da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya samu daga gwamnatin Najeriya da ma ƴan ƙasar a tsawon kwanaki biyar tun bayan rasuwar sa na ci gaba da sanya mutane dasa ayar tambayar shin ko me ya sa marigayin ya fita daban?

Daga aika tawaga zuwa London domin ɗaukar gawar zuwa Najeriya, da kafa kwamitin yin jana'iza, da ayyana hutu ranar binne marigayin da ayyana mako guda na makoki da karɓar gawar a Katsina da faretin bangirma da kuma gudanar da addu'o'i da jawaban bankwana a fadar shugaban ƙasa, za a iya cewa babu wani shugaban Najeriya tsoho ko mai ci da ya rasu da ya taɓa samun irin wannan karramawa.

To ko mene ne dalili? Malam Bashir Gentile mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya ya lissafa wasu dalilai guda biyu da ya ce su ne suka janyo karramawar ta ba-sabun-ba.

1) Tinubu na son wanke kansa

Shugaba Tinubu lokacin da yake gaisuwar bankwana da gawar Buhari a Daura.

Asalin hoton, State House

To sai dai kuma Bashir Gentile ya ce duk da irin abin a yaba da shugaban na Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya yi wajen karrama marigayi Muhammadu Buhari, ba za a rasa dalilan da suka sa ya yi hakan ba.

"Rasuwar Buhari ta zowa wannan gwamnati a kan wani ƙadami, a daidai lokacin da take fuskantar ƙalubale inda Tinubu ke neman rasa goyon baya a arewacin ƙasar bisa zargin cewa Tinubun ya raba gari da Buhari: ƴan siyasar arewa suna neman su yaƙe shi domin kaso 99 na ƴan arewa da suka zaɓi Tinubu sun kaɗa masa ƙuri'a ne saboda Buhari yana tare da shi.

Saboda yanzu da Buhari ya rasu, dole ne ya nuna wa ƴan arewa cewa yana tare da Buhari har yanzu kuma ya yarda Buhari ya taimake shi a rayuwa" In ji Gentile.

Dangane da ko wane irin taimako marigayi Muhammadu Buhari ya yi wa Tinubu, Malam Bashir Gentile ya ƙara da cewa:

"Ai duk karramawar da Tinubu ya yi wa Buhari ba ta kai wadda Buhari ya yi masa domin Buhari ya ɗauki mulkin Najeriya kacokan ya ba shi a daidai lokacin da kaso fiye da 75 na ƴan jam'iyyar APC ba sa son Tinubu. Saboda haka wannan goyon bayan da ya samu daga Buhari har yanzu shi yake nema ƴan arewa su sake yi masa."

2) Tsantsenin Buhari

Jama'a na ƙoƙarin binne gawar Buhari a Daura.

Asalin hoton, State House

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Baya ga karramawar da gwamnati ta yi, su ma dubban ƴan Najeriya sun nuna karamci inda tun bayan rasuwar ta Muhamamdu Buhari suka yin dandazo zuwa mahaifar marigayin musamman ma a ranar da aka yi jana'izar tasa.

Malam Bashir Gentile ya ce dalili na biyu da ya janyo wa Buhari karramawa irin wadda ba a saba gani ba ga shugabanni musamman daga ƴan ƙasa shi ne yadda Buhari ya yi tasiri a zukatansu ta fuskar gaskiya da riƙon amana.

"Buhari ya kwashe shekaru fiye da 60 yana riƙe muƙamai a aikin soja da ma na siyasa. Ya yi gwamna. Ya yi minista. Ya riƙe shugaban hukumar PTF. Ya yi Shugaban ƙasa har karo biyu. Amma bai tara abin duniya ba. Wannan ne ya sa jama'a suka yi imani da cewa shi mutum ne mai gaskiya.

Shi ya sa kuma da ya rasu kowa yake ta yi masa fatan alkairi. Duk da cewa sauran shugabannin na baya da suka rasu kamar Janar Murtala da Umaru Musa Ƴar'adu'a ba wai ba su da gaskiya ba ne. A'a ba su yi tsawon ran da jama'a za su fuskanci haka ba. Sai bayan rayuwarsu ne aka fahimci irin tsantseninsu." In ji Bashir Gentile.

Tinubu ya yi rawar gani
Tinubu na miƙa wa iyalan Buhari tutar Najeriya.

Asalin hoton, State House

Tun bayan jana'izar tsohon shugaban Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari ranar Talata, ƴan Najeriya suka yi ta saka hotunan shugaba Tinubu lokacin da yake yin bankwana da marigayin, a kafafen sada zumunta suna masu jinjina masa.

Masu lura da al'amuran yau da kullum sun amince cewa lallai Shugaba Tinubu ya yi abin da babu wani shugaba mai ci da ya taɓa yi wa wani tsohon shugaban ƙasa da ya rasu.

"Shugaba Tinubu ya yi abin a yaba kuma abin da ba a taɓa gani ba. Ko lokacin da Murtala Muhamamd ya rasu bai samu irin wannan karramawa ba wataƙila saboda a lokacin jama'ar ba su da yawa sannan kuma babu batun siyasa a ciki." In ji Malam Bashir Gentile, mai sharhi kan al'amuran yau da kullum a Najeriya.

"Shi ma marigayi tsohon shugaba, Umaru Musa Ƴar'adu'a bai samu irin wannan karramawar ba duk da kuwa cewa shi ma an yi masa jana'izar ƙasa." In ji Bashir Gentile.