Wane ne zai maye gurbin Buhari a siyasar arewacin Najeriya?

A daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari, hankali ya fara komawa kan wane ɗansiyasa ne zai iya maye gurbinsa a siyasar arewacin Najeriya.
Ana dai yi wa marigayin kallon ɗan siyasa na daban wanda yake da farin jini da kwarjini a idanun talakawa, abin ya sa wasu ke cewa shi ne ɗan siyasa na biyu da ke da irin wannan tagomashi daga talakawa bayan Malam Aminu Kano.
Muhammadu Buhari shi ne ɗan siyasa ɗaya tilo a tarihin arewaci da ma sauran sassan Najeriya da ke iya samun ƙuri'a mai yawan miliyan 12 zuwa 15 ba tare da samun goyon bayan wasu jiga-jigan ƴansiyasa ba da ke da hannu da shuni.
Kafin ya samu nasarar samun zama shugaban ƙasa a 2015 a jam'iyyar haɗaka ta APC, Muhammadu Buhari ya tsaya takarar shugabancin ƙasa sau uku - 2003, 2007 da 2011 ba tare da nasara ba.
Duk da rashin nasarar tasa a zaɓukan uku, ɗan siyasar na samun ƙuri'un da suka wuce miliyan 12.
Buhari shi ne ɗan siyasar da jama'a ke dandazon tarbar shi a duk gangamin yaƙin neman zaɓen da yake yi a birane da garuruwa sannan talakawan arewaci na kaɗa masa ƙuri'a ba tare da ko kwabonsa ba. A lokuta da dama ma talakawa ne ke yi masa ƙwarƙwaryar gidauniya.
A lokacin rasuwar ma irin wannan soyayya ce ta fito fili inda talakawa suka nuna alhinin da ake kyautata zaton babu wani ɗansiyasa a Najeriya da ya taɓa samu, al'amarin da ya tsayar da al'amura cak a Najeriya.
Wannan ya sa tun yana raye ake muhawarar wane ɗansiyasa ne zai gaji wannan kwarjini da farin jinin, muhawarar da aka ci gaba da tafkawa bayan rasuwarsa.
Masu nazarin siyasa da dama na ganin cewa hasken tsohon shugaban na Najeriya, Muhamamdu Buhari ya hana wasu ƴan siyasar yankin haskakawa.
BBC ta kalato wasu fitattun ƴansiyasar da suke yankin da ake ganin suna da farin jini sosai.
Atiku Abubakar

Asalin hoton, Atiku/X
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Atiku Abubakar mai shekara 78 ya kasance tsohon mataimakin shugaban Najeriya karo biyu - a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo tsakanin 1999 zuwa 2007.
Kafin nan dai Atiku ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa a 1999, amma sai Obasanjo ya ɗauke shi a matsayin wanda zai mara masa baya.
Sau shida yana takarar shugaban ƙasar Najeriya: 1993 da 2007 da 2011 da 2015 da 2019 da 2023 ba tare da samun nasara ba.
Atiku Abubakar ya kasance tsohon ɗansiyasa wanda ya kasance ɗaya daga cikin mutanen da Janar Shehu Musa Ƴar'adu'a ya rena a siyasance.
Yanzu haka shi ne madugun ƴan hamayyar a ƙasar, inda yake jagorantar haɗakar ƴan adawa a jam'iyyar ADC domin fuskanar APC a zaɓe mai zuwa, inda ake tunanin zai sake yin takarar shugabancin ƙasar karo na bakwai a shekarar 2027.
Fitaccen ɗansiyasa ne a arewacin Najeriya da ya daɗe yana ɗaukar nauyin ƴan takarar siyasa, kuma da yawa sun samu nasara.
Babban jigo ne a siyasar ƙasar da mutane suke bi a duk inda ya shiga a siyasar Najeriya.
Kashim Shettima

Asalin hoton, Getty Images
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ɗansiyasa ne da za a iya cewa babban ɗan arewa da ya fi muƙami a ƙasar a yanzu haka, kasancewar shi ne lamba na biyu.
An haife shi ne a ranar 2 ga watan Satumban 1966, kuma ya yi gwamna karo biyu tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019 a jihar Borno, sannan ya kuma zama sanata daga 2019 zuwa 2023, bayan barin kujerar gwamna.
Tsohon ma'aikacin banki ne da ya yi kwamishina a zamanin mulkin tsohon gwamnan jihar, Ali Modu Sheriff, inda ya yi shekara huɗu a muƙamin.
A zamanin da yake gwamna ne rikicin Boko Haram ya yi ƙamari, lamarin da ya ƙara masa farin jini saboda kusan duk duniya ana bibiyar lamarin rikicin na Boko Haram.
Kujerar da yake kai ta ƙara masa ƙima da girma a siyasar Najeriya, inda ake ganin duk wani motsinsa zai iya yin tasiri ga siyasar yankin, da ma ƙasar baki ɗaya.
Rabiu Musa Kwankwaso

Asalin hoton, facebook
Mohammed Rabi'u Musa Kwankwaso ɗansiyasa ne daga jihar Kano da aka haifa a ranar 12 ga watan Oktoban shekarar 1956.
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso wanda injiniyar ruwa ne, ya yi gwamnan jihar Kano karo biyu a 1999 zuwa 2003 da kuma 2011 zuwa 2015 lokacin da ya yi kome.
Ya yi ministan tsaron Najeriya a zamanin mulkin tsohon shugaban Najeriya a 2003 zuwa 2007, sannan ya zama sanata a shekarar 2015.
Kwankwaso ya tsayar da Abdullahi Umar Ganduje domin ya gaje shi, ya kuma yi nasara, sannan bayan sun samu saɓani da Ganduje, sai ya sake tsayar da Abba Kabir Yusuf gwamnan Kano na yanzu, inda ya sake samun nasarar doke ɗantakarar da Ganduje ya tsayar.
Ƙungiyar siyasarsa ta Kwankwasiyya tana da matuƙar tasiri musamman a siyasar Kano, inda yake amfani da tsarin wajen tsayar da ƴantakara tun daga na gwamna da ƴanmajalisun tarayya da na jihohi.
Ya ƙara ɗaga darajar siyasarsa a lokacin da ya bar manyan jam'iyyun siyasar ƙasar, ya koma jam'iyyar NNPP da ba a sani ba, inda ya yi takarar shugaban ƙasa.
Jam'iyyar ta kafa gwamnain jihar Kano, da mafi rinyaje a majalisar jihar, da sanatoci biyu da ƴan maalisar tarayya da dama, lamarin da ake ganin marigayi Buhari ne kaɗai ya yi haka da jam'iyyar CPC.
Kwankwaso yana da ɗimbin mabiya da ke ɗauke da alamin jar hula domin nuna biyayya ga jagoran nasu, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso na ɗaya daga cikin ƴansiyasa da suka sauya salon siyasar yankin arewa, wani abu da ke sa masu nazarin siyasa ganin ɗansiyasar ka iya zama Malam Aminu Kano ko Muhamamdu Buhari a arewacin Najeriya.
Nasir el-Rufai

Asalin hoton, ElRufai/X
Nasir Ahmad el-Rufai tsohon gwamnan jihar Kaduna ne da aka haifa a ranar 16 ga Fabrairun shekarar 1960.
Ya yi mulkin jihar Kaduna a wa'adi biyu a jere tsakanin shekarar 2015 zuwa shekarar 2023, kuma kafin nan ya yi ministan Abuja daga shekarar 2003 zuwa 2007 a zamanin mulkin tsohon shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo.
Da shi aka assasa haɗakar kafa jam'iyyar APC, inda ya kasance sahun gaba wajen tallata marigayi Muhammadu Buhari har ya kai ga samun nasarar lashe zaɓe.
Haka kuma ya taka rawar gani sosai wajen nasarar shugaban Najeriya na yanzu, Bola Tinubu, inda shugaban da kansa ya taɓa bayyanawa cewa yana so El-Rufai ya tsaya su yi aiki tare idan ya ci zaɓe.
Haka tun bayan da ya koma jam'iyyar ADC, sai maganar haɗaka da sabuwar tafiya ta fara girma, inda ya zama fuskar haɗakar yunƙurin kafa sabuwar jam'iyyar da za ta fafata da jam'iyar APC mai mulki.
Ana masa kallon ɗansiyasa mai ƙarfin faɗa a ji a yankin arewacin Najeriya da ka iya taka gagarumar rawa a siyasar yankin.
'Abin da ya sa tauraruwar Buhari ta fi ta kowa haske'

Asalin hoton, Getty Images
"Buhari haƙuri ya yi sannan ya daɗe tare da magoyansa tun bayan da suka fara masa kallon yana da abin da sauran ƴansiyasar ba su da ita, "wato gaskiya. Shi ya sa aka fara cewa sai mai gaskiya. Sai ya yi ta haƙurin kasancewa tare da masoyansa na tsawon lokaci, duk da ya sha saɓawa da wasu ƴansiyasa na kusa da shi."
Kalaman Malam Kabiru Sa'id Sufi, kenan, malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami'a da ke Kano kuma mai sharhi kan al'amuran yau da kullum, dangane da halayyar da ƴansiyasa za su nuna kafin su maye gurbin marigayi Muhamamdu Buhari.
Masanin ya ƙara da cewa akwai ƴansiyasa masu farin jini, amm dole sai sun ƙara haƙuri sannan sun nuna wa talakawa sun damu da al'amuransu.
"Wataƙila idan aka yi haƙuri irin nasa, za a iya samu. Shi ma daga farko a hankali ya fara, har ya game arewar baki ɗaya, sannan daga bisani haɗaka ta sa ya kai zuwa kudancin ƙasar."
Ya ce akwai waɗanda suke da farin jini sosai, waɗanda ya ce suna da ƙarfi a siyasance amma kuma ƙarfin nasu bai faɗaɗa zuwa sauran jihohin yankin ba sannan kuma akwai waɗanda ba su samu karɓuwa ba sosai a wurin talakawan yankin.
"Duk da cewa ƙarfinsu yanzu yana jiha ɗaya ne ko biyu, amma akwai yiwuwar ƙarfin ya faɗaɗa, har ma su kai zuwa kudu idan aka samu haɗaka. Akwai kuma waɗanda suke da ƙarfi a ko'ina amma har yanzu ba su samu karɓuwa a zukatan talakawa ba"
"Kamar yadda ake da masu bin aƙida Kwankwasiya da yadda guguwar ta yi tasiri kusan karo biyu ne ya sa ake tunanin guguwar za ta iya tsallakawa zuwa wasu jihohin, sannan wataƙila idan aka yi haƙuri, za ta Iya game arewa, sannan idan aka samu damar haɗaka, za ta iya tsallakawa zuwa kudancin Najeriya."
Masanin siyasar ya yi kwatance da irin guguwar da Peter Obi ya yi, inda ya ce ba a yi tsammani ba, amma guguwarsa ta karaɗe duk da ba shi da gwamnoni a lokacin.
Kabir Sufi ya ce, "Akwai masu alamun samun irin wannan tagomashin, wataƙila guguwar Buharin ce ta danne tasu guguwar. Wataƙila yanzu su ƙara samun tagomashi," in ji shi.
Sufi ya ƙara da cewa akwai wasu ƴansiyasa da suke da jajircewa, "irin su Atiku Abubakar da sauran su, amma gaskiya masu farin jini sosai ba su da yawa."
Sai dai ya ce ba lallai ba ne su yi haƙurin da farin jininsu zai yi irin tagomashin da ake buƙata, amma lallai akwai masu masoya sosai ko kuma suka nuna alamar wannan damar."
Sai dai kuma masanin ya ce kafin talakawa su aminta da kowane ɗansiyasa to dole ne su amince da yarda da gaskiya da riƙon amanar mutum kamar yadda suka gani a tare da tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari.











