Hotunan birnin Maiduguri a lokaci da bayan ambaliya

..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Wani matashi na tsallakar da kare daga ambaliyar ruwan a birnin Maiduguri
Lokacin karatu: Minti 3

Waɗannan hotunan na nuni da irin halin da ake ciki a birnin Maiduguri kwana biyu da abkuwar ibtila'in ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri.

Wakilin BBC da ke birnin ya shaida cewa jama'a na cikin mawuyacin halin neman tallafi musamman na abinci da ruwan sha.

Gwamnan jihar Bornon, Farfesa Babagana Umara Zulum bisa rakiyar jami'an tsaro na ta fama zagayawa zuwa sansanoni domin raba wa jama'a abinci, ƙari a kan wanda jama'ar gari ke rabawa.

..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Nan wasu yara ne da magidanta a kan soron gidaje, inda suka kwashe kwanaki suna kwana a saman domin gudun ka da ruwa ya cinye su
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Yadda mata da ƙananan yara ke samun tallafin tsallakarwa daga ambaliyar ruwa a Maiduguri, inda wasu ke amfani da wuyansu domin ɗaukar yara
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Wani matashin ɗnsintiri a tsaye a tsakiyar ambaliya inda yake yi wa jama'a jagora tare da tsallakar da su a birnin Maiduguri
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Yadda matasa da ƴansintiri ke amfani da ababan hawa domin tsallakar da mata da ƙananan yara zuwa sansanin da aka tanada a birnin na Maiduguri
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Wani ɗansintiri kenan ɗauke da wata yarinya lokacin da yake tsallakar da ita zuwa tudun mun tsira
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Nan wata mata ce da kayanta da takalmanta a hannu ke bin gefen titi domin gujewa tafiya a cikin malalen ruwan da ke kan titi
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Wani magidanci da ke tura kekensa sakamakon ambaliyar da ta hana shi tuƙa keken
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Wani mutum ke duba lafiyar injin motarsa bayan ruwan da ya shanye ta ya janye
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Nan Keke Napep ne ya maƙale a ruwa yayin da ya kwashi mata da ƙananan yaran da ke son tsira
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Yadda matasa ke yi wa masu ababan hawa jagora dangane da wuraren da ya kamata su bi domin ka da su faɗa ramukan da za su nutse a cikin ruwa
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Nan wasu matasa ne da magidanta ɗauke da jarkokin ruwa a hannunsu da suke amfani da su wajen yin linƙaya a wuraren da ruwan ke shanye kai
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Yadda jama'a ke neman mafaka bayan ruwan ya ɗan janye a wasu sassan birnin na Maiduguri
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Yadda wata ƙaramar mota ta bayyana bayan ruwa ya ɗan janye daga wasu sassan birnin Maiduguri
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum tare da sojoji lokacin da yake zagayen ganewa idanunsa yadda ake rabon abinci a Maiduguri
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Nan wani matashi ne ke zaune a kan mota ƙirar a-kori-kura domin tsira daga ambaliyar ruwan da ta mamaye titunan birnin Maiduguri
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Wasu mutane da ke amfani da jirgin kwale-kwale wajen ceto mutane daga ambaliar ruwan
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Nan masu rabon abinci ne a manyan motocin sojoji
..

Asalin hoton, BBC/GIFT

Bayanan hoto, Nan wani magidanci ne goye da ƙaramar yarinya yayin da yake ɗaga hannu domin a jefo masa abincin da ake rabawa