Hotunan birnin Maiduguri a lokaci da bayan ambaliya

Lokacin karatu: Minti 3

Waɗannan hotunan na nuni da irin halin da ake ciki a birnin Maiduguri kwana biyu da abkuwar ibtila'in ambaliyar ruwa a birnin Maiduguri.

Wakilin BBC da ke birnin ya shaida cewa jama'a na cikin mawuyacin halin neman tallafi musamman na abinci da ruwan sha.

Gwamnan jihar Bornon, Farfesa Babagana Umara Zulum bisa rakiyar jami'an tsaro na ta fama zagayawa zuwa sansanoni domin raba wa jama'a abinci, ƙari a kan wanda jama'ar gari ke rabawa.