Putin ya gana da Steve Witkoff kan yaƙinsa da Ukraine

Putin da Witkoff

Asalin hoton, Sputnik/Gavriil Grigorov/Pool via REUTERS

    • Marubuci, Laura Gozzi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 2

Jakadan Amurka na musamman, Steve Witkoff da shugaban Rasha, Vladimir Putin sun kwashe awanni uku suka ganawa a fadar Kremlin, kamar yadda kafafen watsa labarai na Rasha ke rawaitowa.

Witkof ya isa Moscow ranar Laraba a daidai lokacin da wa'adin da Donald Trump ya bai wa Rashar domin cimma tsagaita wuta a yaƙin da take yi da Ukraine.

Shugaban na Amurka ya ce Rasha ka iya fuskantar manyan takunkumai kan duk wata ƙasa da ta yi kasuwanci da Rashar idan dai har ba ta ɗauki matakan kawo ƙarshen "mummunan yaƙin" da take yi da Ukraine.

Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky ya yi gargaɗin cewa Rasha za ta ɗauki matakin zaman lafiya ne kawai idan ta ga ta fara fuskantar talauci. Ya yi maraba da barazanar tsauraran takunkumai da harajin da Amurka ta yi kan kasashen da ke sayen mai daga Rasha.

A wasu hotuna da kafafen watsa labaran Rasha suka wallafa sun nuna yadda mutanen guda biyu waɗanda suka sha haɗuwa da juna, aka gan su suna raha tare da gaisawa da juna.

Ana hasashen cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ya zuwa ranar Juma'a kuma Rasha na ci gaba da gudanar da hare-hare ta sama kan Ukraine duk da barazanar Trump na ƙaƙaba wa Rashar takunkumai.

Kafin rantsuwar kama aiki a watan Janairu, Trump ya yi iƙrarin cewa zai iya kawo ƙarshen yakin tsakanin Rasha da Ukraine a rana ɗaya. Ya gaza cimma hakan sannan yana nuna fushinsa a fili dangane da rashin hanyoyin warware taƙaddamar na fili, inda yake ci gaba da ƙara barazanar takunkumai kan Rashar.

"Mun yi tunanin mun magance yaƙin a lokuta da dama amma sai shugaba Putin ya ci gaba da harba rokoki a wasu birane kamar Kyiv inda ya kashe mutanen da dama a gidajen reno da sauransu," kamar yadda ya faɗa a watan da ya gabata.

An yi tattaunawa guda uku tsakanin Rasha da Ukraine a birnin Istanbul kuma sun gaza cimma kawo ƙrshen yaƙin, shekaru uku bayan da Moscow ta ƙaddamar da yaƙi a kanta.

Sharuɗɗan soji da na siyasa da Rashar ta gindaya kafin cimma zaman lafiya ba abin karɓuwa ba ne ga Ukraine da ƙawayenta na Turai. Rasha ta ƙi amincewa da buƙatun Kyiv na ganawa tsakanin Zelensky da Putin.

A hannu ɗaya kuma, Amurka ta amince da ƙarin sayar da makamai ga Ukraine na tsabar kuɗi har dala miliyan 200 a ranar Talata bayan wani kiran waya da tsakanin Zelensky da Trump, inda shugabannin guda biyu suka tattauna kan cimma yarjejeniyar aiki tare dangane da tsaro da samar da jirage marasa matuƙa.

Ukraine dai ta daɗe tana amfani da jirage marasa matuƙa wajen kai wa Rasha hare-hare da suka haɗa da matatun mai, inda ita kuma Moscow ta mayar da hankali wajen kai hare-hare ta sama a biranen Ukraine.