INEC ta yi gargaɗi kan ayyana sunan ƴan takara gabanin lokacin kamfe

Asalin hoton, INEC
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Najeriya ta ce ayyana 'ƴan takara da jam'iyyun siyasa ke yi tun a tsakiyar wa'adin mulki ya saɓawa dokokin zaɓen ƙasar.
Hukumar ta ce kamata ya yi a bari masu mulki su sauke nauyin alƙawurran da suka ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓensu na baya, maimakon fara gangamin zabe na 2027 tun kafin lokaci ya yi.
INEC, ta yi wannan jan hankalin ne bayan yawaitar al'amurra masu kama da yaƙin neman zaɓe a tsakanin jam'iyyu da kuma ƴan siyasar ƙasar.
An riƙa ganin yadda a matakai daban-daban ake tallata masu sha'awar tsayawa takarar muƙamai, da ma musayar kalamai irin na lokacin gangamin neman zaɓe.
Wani abu mai kama da gangamin tsayar da dantakar shi ne yadda aka ga gwamnoni da 'ƴan majalisa da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya suka sanar da cikakken goyon bayan su ga sake tsayawar shugaba Tinubu takara a zaɓe mai zuwa, har ma suka jaddada cewa babu wanda zai fito domin karawa da shi wajen neman kujerar a cikin jam'iyyar su.
INEC ta ce irin wannan mataki ya saɓawa dokar zaɓe kuma dole a kauce masu.
Hajiya Zainab Aminu, itace kakakin hukumar zaɓen ta Najeriya ta shaida wa BBC cewa, duk irin wadannan abubuwa sun sabawa dokoki na zabe bisa la'akari da cewa akwai tanadi da aka yi don lokacin gudanar da irin wadannan abubuwa.
Ta ce, "Ya kamata ace jam'iyyun siyasa da su kansu masu sha'awar tsayawa takara su kiyaye wadannan dokoki domin ya samar da yanayin da ya kamata da kuma bawa hukumar zabe damar ta shirya zaben kamar yadda ya kamata."
Hajiya Zainab, ta ce," A hukumance abin da ya kamata ace jam'iyyun siyasa sun mayar da hankali yanzu shi ne cika alkawuran da suka dauka a lokacin da suke yakin neman zabensu na baya."
Kakakin hukumar ta ce a yanzu abin hukumarsu shi ne jan hankali da gargadin 'yan siyasa akan su daina irin wannan abu da suke su bar batun yakin neman zabe a lokacin da doka ta tanada.
Sashi na 94 sakin layi na ɗaya na dokar zaɓen Najeriya dai ya yi tanadin cewa za a fara yaƙin neman zaɓe ne daga lokacin da ya rage saura kwana 150 a yi zaɓen, a kuma kammala duk wani nau'in neman zaɓen ana saura sa'oi 24 a kaɗa ƙuri'a.
Akwai kuma dokoki masu tabbatar da cewa 'ƴan takara da jam'iyyun siyasa ba su zarce ƙa'ida ba wajen kashe kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe, duk da cewa an sha ƙorafi a kan ayyuka masu yin hannun riga da waɗannan dokoki.











