Muna so a kafa kotu ta musamman don hukunta laifukan zabe – INEC

Asalin hoton, INEC
Hukumar zabe mai zaman kanta a Najeriya, wato INEC, ta jaddada kiran da a kafa kotu ta musamman domin hukunta laifukan da suka shafi zabe.
Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, ne ya nanata wannan kira a wajen wani taro da ya yi da manema labarai a babban birnin tarayya Abuja, in da ya yi nuni da cewa kafa kotun ya zama wajibi, idan akai la'akari da tarin laifukan zabe da ake aikatawa a kasar.
Ya ce kafata kuma zai saukaka matsalolin da ake fama da su a shari'o'in da suka shafi laifukan na zabe.
Hajiya Zainab Aminu Abubakar, itace mai magana da yawun hukumar ta INEC, ta shaida wa BBC cewa kafa hukumar abu ne mai alfanu idan aka yi la'akai da irin ci gaban da ake samu a harkar gudanar da zabe to amma kama ko hukunta wadanda ke aikata laifuka a lokacin zabe shi ne babban abin da ke ci wa hukumarmu tuwo a kwarya.
Ta ce,"A baya an kafa kwamiti daban-daban inda kowane kwamiti akwai shawarar da ya bawa hukumar INEC, daga cikin shawarwarin da kwamitocin suka bayar har da batun kafa kotun hukunta laifukan da suka jibanci zabe."
"Shugaban hukumarmu ta INEC, ta kara nanata kiran da a kafa kotunan zabe ne domin su rika zaba darasi ga masu aikata laifi a lokacin zaben." In ji ta.
Zainab Aminu, ta ce," Kafa kotunan zaben na da matukar muhimmanci domin a yanzu idan aka kama masu aikata laifi a lokacin zabe ana kai su kotunan majistire ne ko kuma manyan kotunan da ke jihohi, to amma saboda yawan kararrakin da ke gaban kotuna sai kaga an dauki lokaci ba a yanke wa masu aikata laifin zabe hukunci a kan kari ba."
Ta ce," Idan kuwa aka samar da kotunan zabe zasu taimaka matuka gaya domin aiki zai yi sauki domin duk wanda aka kama ya aikata irin wannan laifi to za a hukunta shi a kan lokaci."
Mai magana da yawun hukumar ta INEC, ta ce" Samar da kotun zaben za ta taimaka ma wajen hukunta jami'an INEC din da aka samu da aikata laifi a lokacin zabe."
"A don haka yana da kyau a duba kiran da shugaban hukumarmu ta INEC ya yi na kafa kotun da zata rika hukunta wadanda suka aikata laifukan da suka shafi zabe domin a hanzarta kafa ta."











