Shin ya dace a mayar da zaɓen ƙananan hukumomi hannun Inec?

Wani mai kaɗa ƙuri'a

Asalin hoton, Inec

Bayanan hoto, A Najeriya, akasari jam'iyyun da ke mulkin jiha ne ke cinye komai da komai a zaɓen ƙananan hukumominsu
    • Marubuci, Daga Umar Mikail da Buhari Fagge
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja

Majalisar dokokin Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara ƙoƙarin mayar da nauyin gudanar da zaɓen ƙananan hukumomi karƙashin kulawar hukumar zaɓe ta kasa mai zaman kanta wato Inec.

Yunƙurin na zuwa ne bayan hukuncin da Kotun Ƙolin kasar ta yanke na amincewa da bai wa ƙananan hukumomi cikakken 'yancinsu a harkokin kuɗi.

Akwai jihohin Najeriya da dama yanzu haka waɗanda babu zaɓaɓɓun shugabanni ƙananan hukumomi, kuma a mafi yawan lokuta ana nuna shakku kan sahihancin zaɓen ƙananan hukumomi da hukumomin zaɓe na jihohi ke shiryawa.

Tun bayan hukuncin kotun ƙolin kuma masana da 'yansiyasa ke bayyana mabambantan ra'ayoyi game da tasirinsa a kan dimokuraɗiyyar ƙasar da kuma abin da tsarin tarayya ke nufi.

Daga cikin hukunce-hukuncen da kotun ta bayar har da wanda ta ce saɓa wa kundin tsarin mulki ne ɗabi'ar da gwamnoni ke yi ta rushe zaɓaɓɓun shugabanni da kuma maye gurbinsu da na riƙo.

Masu goyon bayan mayar da zaɓen hannun hukumar zaɓe ta ƙasa kan ce hakan zai rage ƙarfin ikon da gwamnoni ke da shi wajen naɗawa da sauke duk wanda suke so a kan mulki. Masu adawa da shi kuma na cewa matakin ƙara wa Inec nauyin da ba za ta iya saukewa ba ne.

Sai dai babu wani sauyi da za a iya yi game da zaɓen har sai an sauya wasu tanade-tanaden tsarin mulkin Najeriya, wanda shi ne ya bai wa jihohin kafa hukumomin da za su gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomin.

Ko ya dace a mayar da zaɓen hannun gwamnatin tarayya? Tambayar kenan da muka yi wa masana harkokin siyasa da kuma 'yansiyasa domin jin amsarta.

'Akwai alfanu'

Wani mutum yana kaɗa ƙuri'a

Asalin hoton, Inec

Bayanan hoto, Wani mai buƙata ta musamman yana kaɗa ƙuri'arsa a babban zaɓen 2023
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Wani abu da masu goyon bayan mayar da zaɓen ƙananan hukumomi ke ƙara jaddadawa shi ne hakan zai sa zaɓen ya zama baiɗaya a faɗin Najeriya, kamar yadda ake yin na gwamnoni.

Sada Soli Jibilya ɗanmajalisar wakilai ne daga jihar Katsina a arewacin ƙasar, kuma ya faɗa wa BBC cewa ɗaukar irin wannan mataki "yana da alfanu".

Sai dai ɗanmajalisar ya ce ra'ayinsa zai fi karkata ne ga duk abin da zai fi zama alheri daga sakamakon da za a samu na gyaran kundin tsarin mulki da aka yi.

"Akwai alfanu, saboda zaɓen zai zama baiɗaya," a cewarsa.

"Amma ya kamata mutane su gane cewa duk yadda ake tunani cewa za a ƙwace al'amuran ƙananan hukumomi daga hannun gwamnoni ba zai yiwu ba. Gwamna na da ƙarfi kuma shi ne shugaba."

Shi ma Farfesa Jibrin Ibrahim ya yarda da wannan ra'ayi, inda ya ce binciken da wani kwamatinsu ya taɓa yi kan gyaran tsarin zaɓe a Najeriya ya gano babban abin da ya damu 'yan ƙasa shi ne ƙarfin ikon gwamnoni kan zaɓen ƙananan hukumomi.

"A 2008, tsohon Shugaban Ƙasa Umaru Musa Yar'adua ya kafa kwamatin gyara tsarin zaɓe a Najeriya kuma ina ciki," in ji shi.

"Bayan mun gama zagaye ƙasar nan, abu ɗaya da ya fi damun mutane shi ne yadda gwamnoni ba su bari a yi zaɓen ƙananan hukumomi cikin adalci, kuma suna yi ne don su dinga cinye kuɗaɗen ƙananan hukumomin."

Sai dai masanin harkokin wayar da kai da kuma kimiyyar siyasan ya ce tabbas aiki zai yi wa Inec yawa, "amma kuma za su iya".

Abubuwan da za su iya yin tarnaƙi

Ga masu adawa da wannan yunƙuri na ganin dole ne sai gwamnoni sun samu ta cewa a kan mulkin ƙananan hukumomi saboda su ne shugabannin tsaro a jihohinsu.

Haka nan, ɗauke zaɓen daga hannun jihohi tamkar tauye wani ɓangare ne na tsarin tarayya wanda Najeriya ke amfani da shi, in ji su.

Farfesa Kamilu Fagge - masanin kimiyyar siyasa a Jami'ar Bayero ta Kano - na ganin bai dace a mayar da zaɓen hannun Inec ba bisa wasu dalilai uku da ya zayyana, yana mai cewa "abu ne mai wahalar yiwuwa".

"Abu ne da zai kai ga sauya tsarin mulki, wanda ba abu ne mai sauƙi ba saboda sai an kai shi gaban majalisun jiha, kuma a nan ne gwamnoni za su ƙi amincewa da shi idan ba su so," a cewarsa.

"Ƙarin wahalarsa shi ne, a yanzu aiki ya yi wa hukumar zaɓe ta ƙasa yawa. Har yanzu ita kanta ta gaza gudanar da ayyukanta cikin sahihanci da gaskiya. Don haka idan aka ƙara mata zaɓen ƙananan hukumomi zai zama shifcin-gizo ne, idan ba a yi wasa ba sai an gwammace kiɗi da karatu.

"Sai kuma irin kuɗaɗen da za a kashe wajen mayar da shi hannun Inec."

Zaɓen ƙananan hukumomi a Najeriya

Ahmadu Fintiri

Asalin hoton, @GovernorAUF

Bayanan hoto, Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri kenan lokacin da yake kaɗa ƙuri'arsa a zaɓen ƙananan hukumomi ranar Asabar, wanda jam'iyyarsa ta PDP ta cinye duka ƙananan hukumomi 21

Tun daga komawar Najeriya jamhuriya ta huɗu, manyan alamun da aka fi sanin zaɓen ƙananan hukumomi da su - su ne rikice-rikice da kuma yadda jam'iyya mai mulkin jihar ke yin wuf da kowace kujera duk yawansu.

Zaɓen ƙananan hukumomi na farko da aka gudanar a Najeriya tun bayan hukuncin kotun ƙoli shi ne a jihar Adamawa, inda a nan ma jam'iyyar PDP mai mulki ta cinye duka ƙananan hukumomi 21.

A cewar sakamakon da hukumar zaɓen jihar ta Adamawa State Independent Electoral Commission (ADSIEC), PDP ce kuma ta cinye duka kujerun kansiloli, ban da Mazaɓar Demsa ta ƙaramar hukumar Demsa da NNPP ta ci kansila ɗaya.

Da yake sanar da sakamakon ranar Lahadi a birnin Yola, shugaban hukumar zaɓen jihar, Mohammed Umar, ya ce jam'iyya 12 ne suka shiga zaɓen daga cikin 19 da ke da rajista.

Wannan ya ƙara fito da matsalar da aka daɗe ana fama da ita, wadda ba za a iya kawarwa cikin sauƙi ba.

Yanzu haka rahotonni na cewa jihohi kusan 13 ne ke rububin gudanar da zaɓukan a jihohinsu sakamakon hukuncin kotun ƙoilin, wanda ya ce kada gwamnatin tarayya ta sake tura wa gwamnatin jiha kuɗin wata ƙaramar hukuma.