Yadda Kotun Ƙoli ta taka wa gwamnoni burki kan ƙananan hukumomi

Shugaba Tinubu da wasu gwamnonin Najeriya

Asalin hoton, @NGRPRESIDENT

Ƙananan hukumomi na cikin matakan gwamnati a Najeriya, kuma ƴancinsu batu ne da aka jima ana taƙaddama.

An shafe shekaru, ƙananan hukumomi na ƙarƙashin ikon gwamnonin jihohi ta fuskantar tafiyar da kuɗinsu - ta hanyar wani asusu da ake kira na haɗin gwaiwa tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi - da kuma wurin zaɓen sabbin shugabanni.

Tun 1976 bayan rahoton da Ibrahim Dasuki ya jagoranta, ƙananan hukumomi ya kamata a ce suna cin gashin kansu, da sakar masu mara ta fuskar kuɗaɗensu.

Amma daga baya gwamnonin jihohi suka mamaye harakokin ƙananan hukumomi wajen gudanarwa – wanda har zuwa yanzu ake jayayya.

Wannan ne ya sa gwamnatin Tarayya ta shigar da ƙara Kotun ƙoli tana neman tabbatar da ƴancin ƙanananan hukumomi.

Abin da hukuncin kotun Ƙoli ya ƙunsa

A hukuncinta na ranar Alhamis, Kotun Ƙolin Najeriya ta ce iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi da gwamnoni ke yi ya saɓa wa kundin tsarin mulki.

Alƙalin da ya jagoranci hukuncin Emmanuel Agim ya ce ƙananan hukumomi 774 na Najeriya su ne ke da haƙƙin tafiyar da kuɗaɗensu da suke samu daga kason tarayya.

Kotun Ƙolin ta ƙara fayyace ƙarfin ƙananan hukumomi inda a hukuncin ta ce tana cikin matakan gwamnati – tarayya da jiha da kuma ƙaramar hukuma.

Kotun ta kuma ce gwamnatin jiha ba ta da ikon naɗawa da kuma tuɓe shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi, dole sai ta hanyar zabe.

Yadda gwamnoni ke tafiyar da ƙananan hukumomi

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Gwamnoni suna da ƙarfi a siyasar Najeriya ta wannan lokacin, hakan ya sa wasu ke cewa sun mayar da ƙaramar hukumar ƙarƙashin ikonsu.

Wasu na ganin babban dalilin da ya sa gwamnoni ba su son ƴancin ƙananan hukumomi shi ne "facakar" da suke yi da kuɗaɗen ƙananan Hukumomin.

Duk da adawa da gwamnonin jihohin ƙasar 36, suka nuna da ƙarar da gwamnatin tarayyar ta shigar saboda yadda suka mamaye ƙananan hukumomin. Masana na ganin hukuncin Kotun ƙoli babbar nasara ce ga habaƙa ƙananan hukumomin, musamman kasancewarsu kusa da al’umma.

Dakta Kabiru Sa’id Sufi, malami a kwalejin ilimi da share fagen shiga jami’a da ke Kano kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ya ce gwamnoni sun fara ɓullo da matakai har suka karɓe ikon tafiyar da ƙananan hukumomi.

A cewar masanin, batun asusun hadin guiwa na ɗaya daga cikin hanyoyin da gwamnonin suka bijiro da shi ta yadda za a yanke kuɗaɗen ƙananan hukumomi da nufin gudanar da ayyuka tun kafin kuɗin su shigo hannunsu.

“Sannu a hankali har aka kai iko da kuɗaɗen ƙananan hukumomi ya koma ƙarƙashin ikon jihohi, sai abin da gwamna ya ga dama ya ba su – wanda ya hana su yin aikin ci gaba,” a cewar Malam Sufi.

Karfin naɗawa da tuɓe shugabannin ƙananan hukumomi na ɗaya daga cikin dalilin da masana ke ganin ya sa gwamnonin jihohin ke adawa da ƴancin ƙananan Hukumomi.

Gwamna na son kafa waɗanda yake yi da su – waɗanda ba za su iya ƙalubalantarsa ba, ko da kuwa sun hangi matsala ko ba a yi abin da al’ummarsu ke buƙata ba.

Alfanun ƴancin Kananan hukumomi

Akwai haƙƙi da nauyi kan ƙananan hukumomi da kundin tsarin mulki ya tanadar, kasancewar ƙaramar hukuma wani ɓangare na gwamnati.

Sai dai ƙananan hukumomi ba su iya sauke nauyin saboda babu kuɗin gudanar da ayyukan.

Ana ganin Kananan hukumomi su suka fi sanin buƙatun al’umma saboda kusancinsu – domin akwai buƙatun al’ummar ƙananan hukumomi da gwamnatin jiha ba za ta mayar da hankali akai ba.

Don haka a cewar Malam Kabiru Sufi, kananan hukumomi suna da damar ƙirƙiro abubuwan da suke ganin za su amfani al’umma.

Ya ce akwai ayyukan da ƙananan hukumomi za su yi waɗanda za su fi yin tasiri nan-take ga al’ummarsu.

“Za su samu damar sauke nauyin da ke kansu, idan kuɗi na shigowa, kuma za su samu damar ƙirƙiro da wasu ayyuka da suke so waɗanda suke ganin za su amfani al’umma,”

“Shigowar kuɗi kai-tsaye zai iya warware matsalolin ƙananan hukumomi,” a cewar Malam Sufi.

Masana dai na ganin za a samu sauyi ga bunƙasar ƙananan hukumomi musamman idan har suna da dama tafiyarda kuɗaɗensu muddin babu wata hanya ta zangon kasa da aka bijiro da ita.

Sai dai duk hasashen samun sauyin bayan hukuncin Kotun ƙoli, wasu na bayyana shakku kan yadda za a tabbatar ba a yi facaka da kudaden ba kamar yadda aka yi a baya.