Shin tsoffin shugabanni na tasiri wajen samun mulkin Najeriya?

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Umaymah Sani Abdulmumin
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
Siyasar ubangida wani abu ne da ya jima yana haifar da ce-ce-ku-ce a Najeriya musamman a lokutan zabe, sai dai bayan ga batun ubangida akwai wasu kusoshi na kasa irin tsoffin shugabanni da ake ganin kan yi tasiri ko taka rawa a tafiyar da harkokin siyasar kasar.
Kusan kowanne dan siyasa a Najeriya ba ya rasa wani wanda yake yi wa biyayya haka zalika akwai tsoffin shugabanni da ake yi wa kallon masu tasiri ko bayar da gudunmawa wajen tafiyar da tsari na dimokuradiyya.
Tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a shekaru 25 da suka gabata ake ganin yadda wasu 'yan siyasa da ke takara ko hankoron takara kan tattauna ko ziyarta da mu'amala da tsoffi ko shugabannin na siyasa.
A lokacin mulkin Olusegun Obasanjo akwai wadannan suka rinka ganin cewa tsohon shugaban mulkin soji Janar Ibrahim Babangida ya bayar da gudunmawa wajen dora shi a kujerar mulki.
Sannan akwai wasu 'yan siyasa na wannan zamani irin su Peter Obi na jam'iyyar Labour da ake gani ko zargi Obasanjo ya mara wa baya a takararsa ta zaben 2023.
To sai dai wani abu da ya fi jan hankali a wannan lokaci shi ne yadda mutanen da ake ganin na da karfi a siyasar Najeriya ke bibbiyar tsoffin shugabannin ana tattaunawa.
Me aka tattauna?
Duk da dai babu wani da zai iya fitowa takamaimai ya ce ga abubuwan da ake tattaunawa da lokacin wasu ziyarce-ziyarce da ake gani.
Ga misali, a kwanan nan an ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na irin wannan ziyara, ciki har da wadda ya kai wa taohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura, haka nan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufa’i wanda shi ma ake ganin take-takensa na kokarin taka rawar gani a zabe mai zuwa ya kai irin wannan ziyara ga tsohon shugaba Muhammadu Buhari a kwanakin baya da kuma tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Sannan Peter Obi yana ta kara-kaina da gudanar da wasu ayyukan da ke kama da neman hadin-kai ko shirya kansa gabannin zaben 2027.
Masana harkokin siyasa sun ce idan aka yi la'akari da tasirin siyasar kasar kusan duk wannan ba wani abu ne sabo ba. Hanya ce ta kulla kyakkyawan alaka da neman gwada sa'a kan wasu bukatu.
Ta yaya tsofaffin shugabanni ke tasiri?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masana harkokin siyasa irin su Farfessa Kamilu Sani Fagge daga Jami'ar Bayero da ke Kano ya jadadda cewa ire-iren wannan ziyara ko 'yar kebiya tsakanin 'yan siyasa ba bakon abu ba ne.
Farfesa ya bayar da misali da wasu fitattun 'yan siyasa a baya da suka nemi takara da amfani da salon neman goyon-baya daga wasu tsofoffin shugabannin kasa, wajen ganin sun yi tasiri.
Ya ce ana kokari ne na neman goyon-bayan manyan 'yan siyasa duk da cewa kowa na da nashin goyon-baya.
"Galibi akan yi hakan ne saboda idan takara ya zo ko lokacin zabe ba zai yi suka ba ko bata dan takara".
Sannan salon ne na hadin kai ko hada karfi da karfe wajen tafiya tare, saboda 'yan siyasa da zaran an gama zabe hankoronsu shi ne zabe na gaba.
Farfesan ya ce sirrin takara ko siyasa ba sai ana jam'iyyar guda ba, saboda akwai wasu abubuwa da hikima da kowanne dan siyasa ke da ita wajen bayar da gundumawa da ke tasiri matuka a lokutan zabe.
Ya bayar da misali da zaben 2023 inda Peter Obi ya samu goyon-bayan Obasanjo, don haka idan wadannan mutane ne masu karfi da tabbas idan an yi amfani da su ana ganin tasiri a siyasa ko takara.
Farfesa ya ce duk da cewa cin zabe ba wai dole sai da wani tsohon shugaban kasa ba, akwai wani salo ko tasiri na jan hankalin magoya-baya su yi koyi ko aiwatar da abin da suke ganin shi ubangidansu ke yi.
Sannan ana hakan wajen neman taimako daga ketare da kungyoyi. Saboda a wurare daban-daban idan aka samu irin wannan suna yi wa mutum hanyar samun kudi da goyon-bayan kasashe.
Farfesan ya kuma tabo batun masu hannu da shuni da za su iya amfani da tasirinsu wajen ganin dan takara ya kai labari, muddin an tsaya masa.
Babu jam'iyya a wannan harkar
Farfesa Kamilu ya tunasar da cewa akwai shekaru na siyasa da rayuwa da idan mutum ya kai ko rikakken dan siyasa to yakan juya akalar wasu tsare-tsare.
Kamilu ya ce kawai abin takacin shi ne yadda galibi kowa bukatunsa da ribar kanshi kawai suke bai wa fifiko a lokuta da dama na siyasa.
Masanin ya ce siyasa kasuwar bukata ce kowa idan zai samu riba ko biyan bukata yake karkata.
Don haka a cewarsa akwai rawar da kowanne dan siyasa ba wai tsoffin shugaban kasa kadai ba ke takawa idan aka zo batun zabe da takara.











