Ko haƙar ƴan adawar Najeriya za ta cimma ruwa a zaɓen 2027?

Asalin hoton, FB/Multiple
Shugabannin jam'iyyun adawa na ci gaba da kai wa juna ziyara, tare da bayyana aniyar hada hannaye don tunkarar babban zaben kasar na shekara ta 2027.
Ziyara ta baya-bayan nan dai ita ce wadda dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben shekara ta 2023, Mista Peter Obi ya kai wa gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad.
A ƴan kwanakin baya kuma an ga yadda tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai ya ziyarci tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar.
Al'amarin da ke nuni da cewa, da alamun ƴan bangaren hamayar sun fara shirin tunkarar zaben shekara ta 2027.
Ziyarar da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasiru El-Rufa'i ya kai wa tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, ta kasance tamkar wani dan-ba.
Kwatsam kuma, sai ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Leba a zaben da ya gabata, Mista Peter Obi ya kai tasa ziyarar ga gwamnan jihar Bauci, Bala Muhammadna na babbar jam'iyyar adawa, wato PDP a ranar Alhamis.
Inda aka ruwaito gwamnan yana cewa, a shirye yake ya yi aiki da bakon nasa don dada karfafa tsarin dimokuradiyya gabanin babban zaben shekara ta 2027.
To, ko me ire-iren wadannan ziyarce-ziyarce ke nufi?
Farfesa Umar Abubakar Kari, masanin ƙimiyyar siyasar da ke jami'ar Abuja ya ce jam'iyyun adawa na kokarin hada kansu ne gabanin zaben 2027.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
''Sannu a hankali tana kara fitowa cewa manyan jiga-jigan ƴan siyasar Najeriya suna wani gagarumin yunkuri na hada kansu domin tunkarar jam'iyya mai Mulki ta APC da shugaba Bola Ahmad Tinubu musaman a zabukan 2027''
''Akwai maganganu da dama a kasa, kuma za a ce biri ya yi kama da mutum,a kan cewa suna da dubaru daban-daban domin su ga sun hana jamiyyar APC mamaye fagen siyasar Najeriya kamar yadda itama take yi sanu a hankali,'' in ji shi .
Farfesa Umar Abubakar Kari ya kuma bayyana wani abu da ya ce kan iya cikas ga yunkurin ƴan hammaya.
''Babban abin da ya ke kawo shaku akan yiwuwa ko rashin yiwuwar wannan hadaka ko hadin kai shi ne cewa yawancin wadanan mutane sune buri iri daya''
''To akwai babbar aya tambaya kan ko wani zai janyewa wani? Ko ma wacce irin hadakar za'a yi? Sanan kuma wadane matakai za a dauka a ga an kaucewa yin tuntube ko kuma samun matsala tun tafiyar ba ta yi nisa ba?'' in ji shi
Sai dai kuma Farfesa Kamilu Sani Fage, wani masani a fannin ƙimiyyar siyasar da ke jami'ar Bayero ta Kano, na ganin haƙar wannan yunkuri za ta iya cimma ruwa, amma fa sai 'yan hamayyar sun bi matakan da suka dace:
''Na farko dai su taru a bayan mutum daya kamar yadda APC suka taru su ka wa Buhari, sanan na biyu kuma sai sun hade sun zama tafiya daya, sanan abu na uku kuma gaskiya sai sun kawo wa yan Najeriya zabi da ya sha banban da abinda APC suka yi''
''Yanzu inda su ƴan siyasar sun kala abubuwan da APC ta yi kamar kamfe ta ke yi mu su domin gwamnatin APC ta yi kuruce -kuruce wanda yan Najeriya ba su amince da shi ba wadanda suka haifar da tsananin yunwa da talauci da rashin aikin yi ga matsalar tsaro da hauhawar farashi''
''To idan su ƴan siyasar za su hadu, su kuma kawo ƴan Najeriya mafita ga wadanan abubuwa to ko shaka babu za a zabesu''
Sannan abu na hudu kuma daga nan zuwa 2027 sai sun shiga sako da lungu na Najeriya sun sayar da manufofinsu kuma sun sayar da ƴan takarasu'' in ji shi.














