Mece ce gaskiyar cire shugaban INEC Mahmood Yakubu?

Shugaban INEC Mahmood Yakubu

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

A ranar Litinin ne aka yi ta yaɗa jita-jitar cewa shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya cire shugaban hukumar zaɓen ƙasar INEC, Mahmood Yakubu daga mukaminsa.

Labarin ya yi ta ƙewayawa a shafukan sada zumunta da ke faɗin ƙasar duk da cewa shugaban baya cikin ƙasar a halin yanzu, inda aka yi tattauna batun - mutane suka yi ta tofa albarkacin bakunansu.

Amma, mece ce gaskiyar labarin na tsige shugaban na INEC?

Me fadar shugaban ƙasa ta ce?

Fadar shugaban Najeriya dai ta musanta labarin tsige shugaban na INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban ƙasar kan harkokin yaɗa labarai, Daniel Bwala ya fitar a shafinsa na X, ya ce babu kamshin gaskiya a labarin.

"Labarin da yake yawo cewa shugaba Tinubu ya cire shugaban INEC tare da maye gurbinsa da wani ba gaskiya ba ne," in ji Bwala.

Ya buƙaci mutane su yi watsi da labarin saboda ba shi da tushe balle makama.

Ya ƙara da cewa: "Ana sanar da batun aiwatar da wani abu a hukumance daga fadar shugaban ƙasa ne ta hanyoyin da suka dace ba yaɗa jita-jita ba.

Jita-jita ce kawai - INEC

Ita ma a nata ɓangare, hukumar zaɓen Najeriya INEC ta ce babu gaskiyar a batun cire shugabanta, Farfesa Mahmood Yakubu.

Wata jami'a a hukumar ta shaida wa BBC cewa jita-jita ce kawai.

"Labarin ƙarya ne babu ƙamshin gaskiya kamar yadda fadar shugaban ƙasa ta musanta," in ji jami'ar.

Ana sa ran Mahmood zai kammala wa'adin mulkinsa na biyu ne a karshen shekarar 2025 lokacin da zai kammala wa'adinsa na biyu a shugabancin hukumar.

A watan Oktoba 2015 ne tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.