Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Yaushe za a doke Leverkusen bayan cin wasa na 50 a jere?
Bayer Leverkusen ta doke Bochum ranar Lahadi a Bundesliga ta kuma ci wasa na 50 a jere a dukkan fafatawa ba tare da an doke ta ba.
Leverkusen ta ci 5-0 ta hannun Patrik Schick da Victor Boniface a bugun fenariti da kuma Amine Adli.
Sauran da suka ci mata kwallayen sun hada da Josip Stanisic da kuma Alejandro Grimaldo a wasan mako na 33 a babbar gasar tamaula ta Jamus.
Kungiyar da Xabi Alonso ke jan ragama na fatan cin wasa daya nan gaba a La Liga ta kafa sabon tarihi.
Ranar Asabar Leverkusen za ta karbi bakuncin Augsburg a wasan karshe a Bundesliga na bana, idan ba a doke ta ba ta zama ta farko da ta kammala wasannin ba tare da rashin nasara ba.
Wasa daya kacal Bayern Munich ta yi rashin nasara a gabaki dayan kakar 1986-87 da kuma 2012-13 a Bundesliga.
Leverkusen wadda ta lashe Bundesliga na bana na farko a tarihin kafuwarta, na fatan daukar kofi uku a kakar nan.
Ranar 22 ga watan Mayu, Leverkusen za ta buga wasan karshe da Atalanta a Europa League a Dublin.
Haka kuma za ta buga wasan karshe a German Cup da Kaiserslautern a Berlin kwana uku tsakanin wasan Europa.
Rabon da a doke Leverkusen tun 27 ga watan Mayu, inda Bochum ta yi nasara 3-0 a wasan karshe a Bundesligar.