Me ya jawo ƙaruwar matsalar tsaro a Najeriya?

Asalin hoton, Social Media
- Marubuci, Daga Umar Mikail
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Abuja
- Lokacin karatu: Minti 4
Mazauna yankuna da wasu gwamnatocin jiha a sassan Najeriya na bayyana yadda matsalolin tsaro ke ƙara ta'azzara a kwanan nan, ciki har da ƙaruwar hare-haren masu iƙirarin jihadi.
Lamarin ya ɗan fi ƙamari a arewaci zuwa tsakiyar Najeriya.
Tun mako biyu da suka wuce mazauna wasu yankuna na jihar Filato da ke tsakiyar ƙasar suka auka cikin bala'i sakamakon hare-haren 'yanbindiga da ake alaƙantawa da ƙabilanci.
Daga ƙarshen makon da ya gabata zuwa wannan kuma mazauna yankunan jihar Binuwai mai maƙwabtaka suka fuskanci sababbin hare-hare, waɗanda suka yi sanadiyyar kashe sama da mutum 70.
Wani rahoto da kamfanin Beacon mai nazarin al'amuran tsaro a Najeriya da yankin Sahel ya fitar a watan Afrilu ya nuna cewa an samu ƙaruwar mutanen da aka kashe a cikin wata uku na farkon 2025 idan aka kwatanta da wata ukun ƙarshe na 2024.
Rahoton ya ce an kashe mutum 3,610 a tsakanin watan Janairu zuwa Maris, lamarin da ya zarta yawan mutanen da aka kashe daga watan Oktoba zuwa Nuwamban 2024.
A ranar Talata mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya kai ziyara jihar Binuwai, inda ya faɗa wa mutanen jihar cewa "za mu kawo ƙarshen matsalar nan, kada ku ji cewa ku kaɗai ne - lamarin ya shafe mu baki ɗaya".
Su wane ne ke jawo asarar ɗaruruwan rayuka?
Akasarin kashe-kashen da aka fuskanta cikin mako biyu zuwa yanzu ba wasu sababbin rikice-rikice ne suka haifar da su ba.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A jihar Filato, rikici tsakanin manoma da makiyaya da kuma hare-haren 'yanfashin daji ne suka jawo asarar rayuka sama da 100 cikin mako biyu.
Hukumomin jihar sun tabbatar da cewa harin da aka kai ranar Litinin 14 ga watan Afirlu ya yi sanadiyar kashe mutum 51 a ƙaramar hukumar Bassa.
Mako ɗaya kafin haka, hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar ta ce an kashe mutum 52 tare da korar kusan 2,000 daga gidajensu sakamakon hare-haren kan ƙauyuka kusan shida na ƙaramar hukumar Bokkos.
Gwamnan jihar Caleb Muftwang ya ce hare-haren sun zarta rikciin manoma da makiyaya, waɗanda ake yawan alaƙantawa da su shekaru da dama.
A jihar Binuwai, mahara sun kashe kusan mutum 80 cikin mako ɗaya a yankuna uku da suka haɗa da Ukum da Katsina-Ala da kuma Logo.
Rahotonni na cewa a ranar Talata ne aka kashe mutanen na baya-bayan nan a jerin hare-haren da aka dinga kaiwa tun daga ranar Juma'a.
Gwamnan jihar ta Binuwai, Hyacinth Alia, ya yi iƙirarin cewa maharn ba 'yan Najeriya ba ne, "kamar yadda aka ji suna magana da wani harshe kuma ɗabi'unsu sun sha bamban da namu [yan Najeriya]".
Da yake magana ta kafar talabijin ta Channels, Gwamna Alia ya ce rikicin da aka daɗe ana yi ya rikiɗe zuwa wani sabon salo.
"Wannan zango na biyu ne muke gani. Na farkon ana yin sa ne da makiyaya - wanda ba shi da matsala sosai. Abin da muke gani yanzu na da sabon salo kuma mai tsoratarwa."
Kazalika, sabuwar ƙungiyar 'yanbindiga masu iƙirarin jihadi mai suna Mahmuda ta ɓulla a jihar Kwara, ita ma a tsakiyar Najeriya.
Mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa ƙungiyar ta kwana biyu da kafuwa, amma sai yanzu ne suka fara sacewa da kashe fararen hula a dajin Kainji Lake National Park da ke tsakanin jihar Neja da Kwara.
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya koka kan yadda ƙungiyar Boko Haram ke samun nasarar karɓe yankuna a jihar tasa sanadiyyar sababbin hare-haren da take kaiwa kan sansanonin soji, da kuma kashe mutane.
A tattaunawarsa da BBC, shugaban kamfanin Beacon Security Intelligence, Kabir Adamu, ya ce: "An samu ƙarin kai hare-hare a ɓangaren ƙungiyoyin Boko Haram da kuma Iswap a arewa maso gabas, sai kuma Lakurawa da ƴan fashin daji a yankin arewa maso Yamma."
Jihohin da aka fi kashe mutane a 2025
Rahoton kamfanin Beacon na watan Afrilu ya bayyana cewa:
- Neja: An kashe mutum 631, an sace mutum 251 a hare-hare 178 da aka kai jihar
- Zamfara: An kashe mutum 585, an sace mutum 918 a hare-hare 250 da aka kai a jihar
- Borno: An kashe mutum 514, an yi garkuwa da mutum 357 a hare-hare 397 da aka kai a jihar
- Katsina: An kashe mutum 341, an yi garkuwa da mutum 495 a hare-hare 247 da aka kai a jihar
- Kaduna: An kashe mutum 106, a hare-hare 128 da aka kai a jihar
'Kada a siyasantar da kashe-kashe'
Akasarin kashe-kashen na baya-bayan nan sun faru ne a lokacin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ke balaguro a ƙasashen Faransa da Birtaniya, abin da ya jawo 'yan'adawa suka yi ta sukarsa.
Wani abu 'yan'adawar suka dinga sukar shugaban shi ne yadda ya ƙi miƙa ragamar mulkin ƙasar ga Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, sai dai fadar shugaban ta ce ya ci gaba da aikinsa na shugaban ƙasa daga can.
Yayin ziyarar da ya kai jihar Binuwai a ranar Talata, mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya ce Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ne ya umarce shi da ya yi hakan.
Ya nemi duka ɓangarori a jihar da su kada su mayar da kashe-kashen siyasa.
"Ku ba mu dama wajen daina siyasantar da kashe-kashen nan. Ba zai yiwu a tura jami'an tsaro kowane lungu ba, amma suna yin bakin ƙoƙarinsu," a cewarsa yayin wani taron manema labarai.
"Wannan ba maganar siyasa ba ce, ko addini, ko ƙabila - zallan rashin imani ne. Ƙasashe da yawa a duniya kamar Sudan, Nijar, Mali, Burkina Faso na fama da irin wannan matsalar ko fiye da haka."











