'Muna cike da fargaba kan sake dawowar hare-haren 'yan Boko Haram'

.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mayakan Boko Haram
Lokacin karatu: Minti 3

A Najeriya al'umma mazauna wasu daga cikin garuruwan da ke fama da dawowar hare-haren Boko Haram a baya-bayan a jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasarn ne ci gaba da bayyana damuwarsu, saboda matsanaciyar fargaba da suka tsinci kansu a ciki, sakamakon janyewar sojoji daga yankunan da suke zaune.

Hakan na zuwa ne yayin da gwamnan na Borno Babagana Umara Zulum ya yi gargaɗin cewar wasu daga cikin yankunan jihar sun fara komawa ga mayaƙan ƙungiyar ta Boko Haram, bayan wasu zafafa hare-haren.

Janyewar sojojin dai ya jefa fargaba a zukatan mutanen da ita kanta gwamnatin jihar ta Borno, inda ta fara tsugunarwa a wasu garuruwa da aka samu zaman lafiya a baya.

Wani mazaunin garin na Wajiroko a yankin karamar hukumar Damboa, inda mayakan boko haram suka tarwatsa kauyka uku da a baya suke hannu sojoji.

Ya bayyana cewar 'sun kawo hari a Sabon Gari ba a jima ba suka kawo wani nan Wajiroko, suka tada mutane, mu kuma talakawa mun shiga damuwa, sun kuma fada mana cewar, yanzu sai mu da ku, tunda mun fatatataki sojoji, sai kuzo mu zauna lafaiya', a cewar mutumin.

Haka zalika ya ce a halin da ake cikin yanzu ala tilas suke rayuwa da mayaƙan na boko haram, inda har ta kai ga cewar 'yan boko haram din kan zo akan babura suna fada masu cewar yanzu sun koma ƙarkashin daularsu, tunda sun kori sojoji', a cewar sa.

Ya ce hare haren mayakan boko haram din ne dai yasa sojojin Najeriyar ja da baya, inda hakan ya baiwa mayakan boko haram din ci gaba da cin karensu babu babbaka a yankin. sun kai hari Sabon Gari, sannan su kawo Wajiko.

"Babu sojoji a Wajiko da Sabon garin, yan boko haram ne suka kore su, akwai wata gada da ta hada garuruwan biyu, sun karyata, wanda hakan yasa mukan yi doguwar tafiya kafin mu kai iyalanmu asibiti" a cewar sa.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Ba wai iya al'ummar Wajiroko da ke karamar hukumar ta Damboa ne ka ai ke cikin irin wannan faragaba ba, chan su ma a Gamborin Gala, hare haren mayakan boko haram din ya sa su tsallakewa zuwa makobciyar Najeirya Kamaru.

Wani mazaunin garin ya ce suna kwance suka tashi suka ga hayaki bayan da suka binckasai akace da su yan boko haram ne suka kashe sojoji suka debi makamai, da motoci, sun kai hari kan sojoji har kusan sau uku.

'Bayan da muka ga sojoji ma suna kaura shi ne mu ma muka tsallake ruwa, muka shiga Kamaru, tun da kaga an raunata sojoj, ai kaga zama bai same mu ba.

Mayakan na boko haram dai na mayar da hankali ne kan sansanin sojoji ko inda gwamnatin jihar ta fara mayar da mutane gidajensu, bayan samun zaman lafiya. Abin da ke nuna akwai bukatar hukumomi tsaro a da ita gwamantin tarayya su dauki matakan shawo kan lamarin don kaucewa koma gida jiya, na taɓarɓarewar tsaro.

Ita ma ƙungiyar tuntuɓa ta arewacin Najeriya ACF ta bi sahun sauran al'umma wjen damuwarta kan dawowar hare-haren Boko Haram ɗin a jihar Borno, da na ƴan bindiga a wasu daga cikin jihohin arewacin ƙasar a baya-bayan nan, da har ta kai ga ƙungiyar ta ACF gudanar da wani taron gaggawa jiya Alhamis a Kaduna.