Sabuwar ƙungiyar ƴan bindiga ta ɓulla a jihar Kwara

Bandits

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 2

Wata ƙungiyar masu iƙirarin jihadi da ake kira Mahmuda ta zafafa ayyukanta na addabar jama'a a wasu garuruwa na ƙananan hukumomin Kaiama da Baruten na jihar Kwara da ake tsakiyar Najeriya.

Bayanai sun ce ƴan ƙungiyar sun samu mafaka ne a gandun dajin Kainji Lake National Park, kuma daga can ne suke kai hare-hare a garuruwan da ke makwabtaka da dajin har ma da wasu sassa na jihar Neja mai maƙwabtaka.

Yanzu haka dai mutanen garuruwan da abin ya shafa na ta yin hijira zuwa wasu wurare, domin guje wa hare-haren ƙungiyar ta Mahmuda.

Mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa dama ƙungiyar ta taɓa kafa sansani a ƙananan hukumomin Kaiama da Baruten.

''Sun fi shekara uku da bayyana," in ji mutumin da ya buƙaci a sakaya sunansa.

Da aka tambaye shi me ya sa sai yanzu ake jin ɗuriyarsu, sai ya ya ce a baya babu ruwansu da jama'ar gari.

"Sun nuna mana babu ruwansu da mutanen gari kuma hakan ya sa muka saki jiki da su. Amma haka kawai sai suka fara kashe mana mutane, suna yawo da makamai, suna kama mutanen gari da kuma yanke masu hukunci.

''Daga gabas da gari zuwa yamma, mutum ba shi da halin zuwa gona mai nisan kilomita biyu. Gaba ɗaya na tsorata, kashi 50 cikin 100 na mutanen garin sun gudu.''

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

A cewar mutumin, ƙungiyar ta Mahmuda ta haramta wa mutanen Kaiama da Baruten noma.

''Kashi 95 cikin 100 na mutanenmu manoma ne, to yanzu sun ce ba mu da damar yin noman, ka ga dai yanzu mutuwa ce ke fuskantarmu, ba ma yunwa ba,'' in ji shi.

Dokta Kabir Adamu, shuagaban kamfanin Beacon mai nazari da bincike kan harkar tsaro a Najeriya da yankin Sahel, ya ce a fahimtarsu wannan ƙungiya ta Mahmuda tana da alaka da kungiyar ISWAP.

''Kusan aƙidarsu da abubuwan da suke ƙoƙarin yi ya zo ɗaya. Mu a yadda muke kallon abin bai canza komai ba," kaamr yadda ya shaida wa BBC.

Ya yi bayanin cewa dama can akwai irin waɗannan ƙungiyoyi a dajin wannan yanki na jihar Kwara, amma sojoji suna fatattakar su, kuma wasu na sake ɓulla.

Ya ce: ''Idan ba za ka manta ba a kwanakin baya akwai wata ƙungiya da ake cewa Darussalam, wadda ta yi ƙarfi sosai kafin daga baya sojoji suka fatattake ta daga yankin.''

Masanin tsaron yana ganin wajibi ne a tashi tsaye wajen yin "amfani da 'dabarun bincike da amfani da ƙarfin soji, da kuma amfani da dokokin da suka dace wajen zartar da hukunci a kan masu hannu a ciki'' domin ganin an murkushe wannan nau'i na ƙalubalen tsaro a Najeriya.