Me haramta ƙungiyar Lakurawa da kotun Najeriya ta yi ke nufi?

Lakurawa

Asalin hoton, AFP

Lokacin karatu: Minti 4

A ranar Alhamis ɗin nan ne wata babbar kotu a Abuja ta haramta ayyukan ƙungiyar Lakurawa da ayyana ƙungiyar a matsayin ta ta'addanci.

Mai shari'a James Omotosho, a hukuncin nasa kan shari'ar da ministan shari'ar Najeriya, Lateef Fagbemi ya shigar.

Alƙalin ya ce " an ayyana ayyukan ƙungiyar Lakurawa da sauran ƙungiyoyi irinta masu addabar mutane a yankin arewa maso yamma da arewa ta tsakiya, da haramtattu kuma na ta'adda."

"An haramta wa duk wani mutum ko ƙungiya yin alaƙa da ƙungiyar Lakurawa da kowane irin suna ko kuma a kowane irin dandali.

Me haramta ƙungiyar ke nufi?

Barrister Bulama Bukarti lauya ne kuma mai bincike kan tsaro a yankin Sahel, ya fara da yaba wa gwamnatin Najeriya bisa ayyana ƙungiyar Lakurawa da ta yi a matsayin ƙungiyar ta'addanci "saboda idan ka duba duk wasu sharuɗɗa na ta'addanci to za ka ga ƙungiyar tana da su."

Ya kuma ƙara da lissafa wasu abubuwa guda shida da haramta ƙungiyar ke nufi kamar haka:

1) Haramta mu'amala da ƙungiyar

Barrister Bukarti ya ce a dokance abin da haramta ƙungiyar ke nufi shi ne yanzu duk wani mutum ko ƙungiya za su guji haɗa alaƙa da wannan ƙungiya saboda yin hakan ya zama babban laifi saɓanin kafin a haramta.

"Tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowane ɗanƙasa ƴancin walwala da shiga kowace irin ƙungiya. To amma idan aka ayyana ƙungiya a matsayin ta ta'addanci to shiga irin wannan ƙungiyar ya haramta. Haka kuma goya musu baya ko kuma alaƙa kowace iri da su zai zama haramun ne.

Kafin yanzu da ma ayyukan da ƙungiyar Lakurawa ke yi haramun ne amma zama ɗan ƙungiyar bai zama haramun ba kai tsaye idan ba an samu mutum da laifin aikata irin aikin da ƙungiyar ke yi ba a gaban alƙali.

Amma yanzu idan aka gurfanar da mutum a gaban kotu aka ce ɗanƙungiyar ne ma kawai to ya wadatar a hukunta shi irin hukuncin ƴanta'adda. Haka ma idan mutum ya nuna goyon bayansa ga ƙungiyar kamar ta hanyar rubuta a kafafen sada zumunta. Haka saye ko sayar musu ko kuma aure daga gare su." In ji Barrister Bulama.

2) Ƙwace duk abin da ƙungiyar ta mallaka

Tasirin ayyana ƙungiyar Lakurawa a matsayin ta ta'addanci na biyu a dokance shi ne yanzu za a iya ƙwace duk abubuwan da ƙungiyar ta mallaka:

"Idan suna da asusun banki za a iya kwace shi. Idan suna da ƙasa kamar gona ko fili ko gida duk za a iya ƙwace su. Haka ma idan suna da ababan hawa kamar motoci da babura da keke. Sannan kuma za a iya saka musu takunkumin tafiye-tafiye." In ji Bulama Bukarti.

3) Ƙarfafa ayyukan jami'an tsaro

Sojojin Najeriya sun samu damar yin amfani da duk wani ƙarfi wajen yaƙar Lakurawa

Asalin hoton, Defence HQ

Kafin ayyana ƙungiyar ta Lakurawa, jami'an tsaron Najeriya musamman sojoji na da taƙaitaccen ƴancin ɗaukar matakai kan ƴaƴan ƙungiyar.

"Doka yanzu ta bai wa sojoji da sauran jami'an tsaro ƙarin iko wajen yaƙar ƴanƙungiyar da ba su da shi wajen yaƙar ƙungiyar da ba ta ta'adda ba. Misali za su iya amfani da manya-manyan makamai.

Haka ma za su iya amfani da hanyoyin tattara bayanai na sirri waɗanda ba za ka iya amfani da su a kan ƙungiyar da ba ta ta'adda ba." In ji Bukarti.

4) Ƙungiyoyin jinƙai

Wani abu da ayyana ƙungiyar Lakurawa ke nufi shi ne yanzu an haramta wa duk wata ƙungiyar agaji yin mu'amila da ƙungiyar.

"Kafin wannan ayyanawar, ƙungiyoyin jinƙai ka iya bai wa ɗan ƙungiyar taimako. Amma a yanzu haka ayyanawar ta haramta duk wata hanya da za a taimake su." In ji Bulama.

5) Alaƙar ƙasa da ƙasa

Bayan ayyana Lakurawa a matsayin ƙungiyar ta'adda, yanzu sauran ƙasashen duniya zai bai wa ƙasashe da ƙungiyoyin duniya su yanke alaƙa da su.

"Misali ƙungiyoyi irin su ECOWAS da AU da sauransu da ma ƙasashen duniya ka iya ƙwace abubuwan da ƙungiyar ta mallaka da hana su shiga ƙasashensu da dai duk wani abu da idan suka yi da ƙungiyar Lakurawa zai zama laifi." In ji Bukarti.

6) Al'umma za su guji ƙungiyar

Da farko dai gwamnatin Najeriya ta ce Lakurawa ba wata ƙungiyar da za a ji tsoro ba ce.

Asalin hoton, Getty Images

Abun da ayyanawar ke nufi shi ne ƴanƙungiyar za su yi baƙin jini kuma jama'a za su ƙyamace su domin tsoron ka da su aikata laifi.

"Ayyanawar za ta iya illa ga mutumcin Lakurawa a idanun mutane domin yanzu idan akwai matasa da ke sha'awar shiga ƙungiyar to bayan ayyanawar jama'a za su ƙyama ce su.

Illar ayyana Lakurawa a matsayin ƴanta'adda

Sai dai kuma Baririster Bulama Bukarti ya ce duk da ayyana ƙungiyar da ta ta'addanci wanda abun a yaba ne amma kuma akwai wasu illoli guda da ka iya biyo baya kamar haka:

  • Take haƙƙin bil'adama: Matsalar irin wannan shi ne jami'an tsaro za su iya amfani da ƙarfin ikon da doka ta ba su wajen take haƙƙoƙin ƴan ƙungiyar kamar yin amfani da ƙarfi fiye da ƙima a kansu ko kuma kashe ƴan ƙungiyar ba tare da gurfanar da su a gaban alƙali ba
  • KIsan fararen hula: Ƴancin da dokar haramta Lakurawa ta bai wa jami'an tsaron ka iya zama illa ga fararen hula, kasancewar jami'an tsaron ka iya far musu da sunan kuskure.
  • Rashin damar yin sulhu: Yanzu an riga an raba gari kenan babu zancen yin sulhu tsakanin gwamnati da ƴan ƙungiyar tunda an riga an ayyanata a matsayin ƙungiyar ta'addanci.