An kawo ƙarshen shirin nukiliya na Iran kenan ko da saura?

Asalin hoton, maxar technologies
Cibiyar shirin nukiliya ta Fordo ta Iran ita ce wadda masu leƙen asiri na duniya suka fi sanya wa ido.
A shekara ta 2009 ne hukumomin leƙen asiri na Yammacin duniya suka bayyana cewa akwai wani wajen aikin nukiliya na sirri a can.
A yanzu sanin ainahin irin ɓarnar da hare-haren sama na Amurka yana da muhimmanci wajen sanin inda aikin wannan cibiya ya sa gaba.
Wani rahoto na sirri daga hukumar leƙen asiri ta sojin Amurka ya nuna cewa muhimman kayayyakin aikin nukiliya na Iran suna nan ba a lalata su ba, kuma illar da aka yi wa shirin nukiliyar nata illa ce da za a ce ta mayar da aikin baya tsawon 'yan watanni kawai, amma ba shekaru ba.
To amma dai duk da haka ana ɗaukar wannan a matsayin bayanai na farko-farko da ba a kai ga tabbatar da shi ba ɗari bisa ɗari, kasancewar wajen da wannan cibiya take na da tsaro sosai.
"Za a ɗauki tsawon lokaci kafin a san ainahin illar da aka yi wa wajen" in ji hafsan-hafsoshin sojin Amurka Janar Dan Caine, a lokacin da aka kai harin.
Hotunan tauraron ɗan'Adam da ke nuna ƙofofi da ƙura ba sa tabbatar da ainahin abin da ya faru a can ƙarƙashin ƙasa, kasancewar yankin yana da zurfi sosai. Kuma ba sa nuna cewa tsaunin da ke wajen ya ruguje.
Zai iya kasancewa duk da irin girma da ƙarfin bam ɗin da Amurka ta yi amfani da shi a harin, Iran tana da nagartaccen aiki da zai hana duk wani bam fasa wajen - ta yadda ba za a iya kaiwa ga cikin wajen ba inda na'urori da kayayyakin aikin nukiliyar suke.
Hasali ma wannan shi ne karon farko da Amurka ta yi amfani da wannan bam ɗin nata, saboda haka ba za a iya tabbatar da irin ƙarfinsa da tasiri ko illarsa ba.
Sai dai na'urorin da ake amfani da su wajen inganta sinadarin yureniyom, na'urori ne da ke gudun gaske, wanda kuma ɗan abu kaɗan zai iya shafar aikinsu, saboda haka harin da aka kai zai iya yuwuwa ya taɓa aikinsu, ko ma ya lalata su.
Akwai buƙatar samun ƙarin bayanan sirri kafin a san ainahin illar da aka yi wa wajen aikin nukiliyar na Iran.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ko da an lalata wuraren aikin nukiliya na Iran irin su Fordo, kamar yadda jami'an Amurka suka ce, hakan ba zai sa a ce shirin nukiliya na Iran ya ƙare ba kenan, ko a ce an kawo ƙarshenshi.
Saboda zai iya kasancewa ƙasar na shirin a wani waje ko kuma ta ci gaba da shi a wani wajen daban.
An ga jerin gwanon motoci a Fordo kafin a kai harin, kuma babban abin tambaya a nan shi ne me waɗannan motoci suke yi a wajen kuma ina za su?
Dukkan alamu na nuna cewa Tehran ta kai kayayyakin aikin inganta sinadarin yureniyom ɗinta wani waje.
Kodayake ba lalle ba ne ta iya kwashe da yawa da za su iya ci gaba da aiki kamar yadda ya kamata a inda aka kai su.
Kuma ko da Iran tana da isasshen sinadarin yureniyom, akwai muhimman matakai da za a kai kafin a iya ƙera makaman nukiliya da su - wanda hakan na buƙatar ƙwarewa sosai ta kimiyya.
Babban abu ɗaya da Isra'ila ta yi kafin fara yaƙin shi ne kashe ƙwararrun masana kimiyya da ke aikin nukiliyar na Iran, domin ta jinkirta aikin. Wanda kuma lalle ya haifar da naƙasu ga shirin. To amma yaya girman illar yake?
Amsar wannan tambaya ta ta'allaƙa ne ga sanin abin da ya rage bayan harin, wanda kuma ƙiyasi ne kawai ba amsa ce ɗari bisa ɗari ba.
Duka wannan na nufin hukumomin leƙen asiri za su tsananta ayyukansu a watannin da ke tafe domin sanin halin da shirin nukiliyar na Iran yake ciki.
Idan har akwai alamun cewa Iran cikin sirri na sake haɗa shirinta na nukiliya ko kuma tana ci gaba sosai wajen ƙera makaman nukiliya, to lalle rikicin zai iya sake dawowa.











