Mene ne ƙarin mahaifa, kuma me ya sa ƴanmata ke fama da shi?

...

Asalin hoton, Getty Images

Lokacin karatu: Minti 5

Yawanci ana ganin cutar ƙabar mahaifa wato fibroids na damun mata ne daga shekaru 30 zuwa 50 inda ake kallon ta a matsayin wata cuta da ke shafar mata manya ne kawai. Sai dai labarin Aisha Musa, wata yarinya 'yar shekara 26 daga Kaduna, ya nuna cewa wannan cutar na iya shafar mata ƙanana fiye da yadda ake zato.

Aisha ta fara lura da wasu canje-canje a jikinta shekaru biyu da suka wuce, lokacin da take cikin ƙuruciya. Ta shaida wa BBC Hausa yadda ta fara jin ciwon ciki mai tsanani da kumburin a ƙasan cikinta, da kuma jin zafi sosai lokacin da take fitsari da kuma lokutan al'ada.

"Na fara jin wani irin ciwo a cikina, kamar yana matsa min gaba da baya. Bayan wani lokaci sai ciki na ya ƙara girma kamar ina da juna biyu. Hakan ya sa na fara jin tsaro da rashin jin daɗi sosai," in ji Aisha.

Ta kara da cewa ta kuma lura da canji a al'adarta, inda jinin al'adarta ya ƙara yawa sosai fiye da da, kuma kwanakin al'adar ya ƙaru sosai inda yake ɗaukan tsawon lokaci kafin ya tsaya. Wannan ya sa ta damu kuma ta garzaya asibiti.

Bayan gudanar da gwaje-gwaje, likitoci suka tabbatar mata da cewa tana da cutar ƙabar mahaifa.

Mece ce wannan cutar?

A cewar inshorar lafiya ta Birtaniya NHS, ƙabar mahaifa wata tsoka ce da kan tsiro a ciki ko wajen mahaifa kuma ta kan kasance ƴar ƙarama kamar ƙwalar lemu amma idan tayi girma ta kan kai girman kankana.

A cewar NHS, mace ɗaya a cikin uku za su samu ƙabar mahaifa a lokacin da suke da shekaru 30 zuwa 50 kuma NHS ta ce mata baƙaƙen fata sun fi yin wannan ƙabar sannan kuma ta fi fitowa a mahiafar mata masu ƙiba saboda ƙiba tana ƙaro sinadarin estrogen a jiki.

Sai dai kuma, NHS ta ce matan da ke haihuwa ba su cika kamuwa da cutar ƙabar mahaifa ba inda ta ce a yayin da mace ke ƙara haihuwa tana ƙara kaucewa kamuwa da cutar.

Yaya alamomin cutar suke?

...

Asalin hoton, Getty Images

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Dakta Ngozi Obi, wata likitar mata da ke zaune a birnin Legas ta shaida wa BBC irin alamomin da ke nuna cewa mace na ɗauke da ƙabar mahaifa inda ta ce alamar da aka fi samu shine zubar jini dayawa kuma a wasu lokuta yakan iya zama barazana ga rayuwa.

"Idan ciwon yayin tsanani, yakan haddasa takura a ɓangaren kayan cikin mutum kamar a mafitsara, zai iya takure mafitsara ta sa ka riƙa yawan fitsari." in ji likitar.

"Ƙabar mahaifa na kuma lalata ƙoda idan ta yi tsanani, tana kuma shafar dubura, za kuma a iya samun cushewar ciki." likitar ta ƙara da cewa.

Likitar ta kuma ce ta taɓa gamuwa da cutar ta ƙabar mahaifa a baya

Wata cibiyar bincike daga jami'ar California da ke San Francisco na Amurka ta kuma ce ƙarin alamomin ƙabar mahaifa sun haɗa da ƙaruwar kwanakin al'ada da kuma girman ciki kamar na juna biyu.

Binciken da cibiyar tayi ya nuna cewa wasu matan kan ji nauyi a mararsu wani lokaci nauyin ma kan iya zuwa da ciwon ciki da zai iya hana su harkokinsu na yau da kullum.

Haka kuma binciken ta gano cewa Fabriods kan sa ciwon baya bare daga ƙasa-ƙasan baya.

Meke janyo ƙabar mahaifa kuma wa ke kamuwa da ita?

...

Asalin hoton, Getty Images

Inshorar lafiya ta Birtaniya NHS ta ce babu wani taƙamaiman abu da ke janyo ƙabar mahaifa a jikin mace amma ana kyautata zaton cewa sinadarin estrogen na tamakawa wajen kamuwa da cutar

Sinadarin estrogen a cewar NHS sinadari ne a jikin mace da ke samarwa da al'ada da sauran alamomin girma da ke bayyana a jikin mace a lokacin da ta kai shekarun balaga.

Shiyasa ƙabar mahaifa ta fi tsirowa a lokacin da mace take shekarun haihuwa wato a lokacin da za ta iya ɗaukar ciki kenan saboda a lokacin ne estrogen ya fi yawa a jikinta.

Bayannan NHS sun nuna cewa da zarar mace ta daina al'ada, sai fibriods ɗin da ke jikinta su fara motsewa suna rage girma saboda estrogen ɗin da ke jikinta ya janye a wannan lokaci.

Bayanan NHS ya kuma nuna cewa duk mace na iya kamuwa da fibroids, amma mata tsakanin shekaru 30 zuwa 50 sukan fi kamuwa da cutar, amma kuma daga tattaunawar da BBC ta yi da Aisha, wace da kamu da cutar a lokacin da take da shekara 26 ya nuna cewa wannan cuta na iya shafar mata ƙanana fiye da yadda ake zato.

NHS ta kuma ce mata masu ƙiba da waɗanda ba su haihu ba, ko masu tarihin cutar a iyali, na da haɗari mafi girma wajen kamuwa da cutar."

Za a iya warkar da ƙabar mahaifa?

Dakta Ngozi ta ce za a iya warkar da ciwon ƙabar mahaifa kuma hanyar da aka fi amfani da ita wajen warkarwa ita ce tiyata.

"Tiyatar za ta iya haɗawa da irin aikin da ake kira da 'Hysterectomy' wanda ya shafi cire mahaifa ko ɗaya da ake cewa 'Myomectomy' wanda shine tiyartar cire ƙaba daga mahaifar.

Likitar ta kuma ba da shawarwari kan rage yuwuwar kamawa da ƙabar mahaifa kamar haka.

  • Cin abinci mai gina jiki da rage yawan mai da sukari.
  • Motsa jiki akai-akai don kiyaye nauyi.
  • Gujewa damuwa da samun isasshen hutu
  • Yin gwaje-gwaje akai-akai don gano matsaloli da wuri.
  • Gujewa shan tabar sigari da barasa.

Likitar ta ƙara da cewa abin da ya fi dacewa shine mace ta je asibiti idan ta ji wasu ko dukkan alamomin da aka lissafo a tattare da ita.

"Gano cutar da wuri da samun magani na da muhimmanci sosai." in ji likitar.