Me ya sa wasu mata ke daina al'ada a lokacin da suke kan ganiyarsu?

Asalin hoton, other
Batun daina jinin al'ada ba matsala ba ce, wani mataki da ke riskar mata a wasu shekarun girmansu na rayuwa.
To sai dai yanayin kan zo da wasu sauye-sauye. Mata kan fuskanci sauye-sauyen sinadaran halitta a jikinsu a lokacin daina al'ada.
A wannan maƙala za mu tattauna alamomin daina al'ada tare da yadda za a fuskanci wannan yanayi.
Dkta Shivani Garg ƙwararriyar likitar mata ta yi bayanin wasu daga cikin alamomin.
Me ake nufi da daina al'ada?
A lokacin daina jinin al'ada ya kusanto, ƙwayoyin halittar da ke cikin mahaifa da sinadaran da ke bayyana a lokacin saduwa kan ragu, wannan raguwa ne kuma ke haifar da canje-canje a jikin mace.
Waɗannan ƙwayoyin halitta da sinadarai ba lokaci guda suke ɓacewa ba. Sannu a hankali suke raguwa, sukan kai shekara biyu zuwa biyar.
A wannan lokaci, alamomi masu yawa kan bayyana a jikin mace, sannan akan samu sauye-sauye masu yawa.
Bayyanar waɗannan alamomi kaɗai ka iya tabbatar mana cewa muna dab da isa lokacin da jinin al'adarmu zai daina zuwa.
Alamomin daina jinin al'ada
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Saurin fushi da hasala
Babbar alama ta farko game da aina jinin al'ada ita ce mace za ta fara shiga wani yanayi, musamman abin da ya shafi halayya da ɗabi'unta, za ta riƙa yin saurin fushi, da hasala da rashin haƙuri.
Gajiya
Mata da yawa kan fuskanci gajiya a jikinsu a lokacin farko-farkon fara daina al'ada, za su ji ba sa rabuwa da gajiya ko da kuwa suna samun hutu. Hakan na faruwa ne saboda sauye-sauyen da suke samu a ɗabi'unsu.
Jin zafin a wasu ɓangarorin jiki
Ƙaruwar jin zafi a wasu ɓangarori na jiki wata alama ce ta dain jinin al'ada. Haka kuma a wasu lokata yakan zo da gumi.
Hakan kuma akan samu bayyana cutukan da ke da alaƙa da mafitsara, a wasu lokutan fitsari kan kwace wa mace ya fito musamman a lokacin da ta yi atishawa ko tari. Waɗannan na daga cikin manyan alamomin daina jinin al'ada.
Wasan jinin al'ada
Wata babbar almar daina jinin al'ada ita ce jinin ya riƙa yi wa mace wasa, ma'ana ya riƙa zuwa da ɗaukewa ba lokacin da ta saba ba.
A wasu lokutan mace kan shafe lokaci mai tsawo ba tare da jinin ya zo ba, kamar wata biyu zuwa uku, sannan idan ya zo ba zai daɗe ba kamar yadda ya sba daɗe mata.
A wasu lokutan kuma, idan jinin ya zo yakan daɗe, sannan idan ya ɗauke, sai ya sake dawowa ba tare da jimawa kamar yadda a saba ba.
Me yasa wasu matan ba sa iya haihuwa idan sun kai shekara 30 zuwa 35.
Amma abin lura a nan shi ne idan kina fuskantar yawan zubar jini, kar ki zauna, watakila wata matsalar ce.
A wannan yanayi, yana da matuƙar muhimmanci ki gaggauta tuntuɓar likitanki.
Ba kowace matsalar da ta dangancin jinin al'ada ba ce ake alƙantawa da daina al'ada. Idan kina fuskantar matsala game da jinin al'adarki a shekarun ƙuruciya, yana da matuƙar muhimmanci ki tuntuɓi likita.
A irin wannan yanayi, gaban mace kan bushe, kuma akwai yiyuwar ta kamu da matsalolin ciwon sanyi
Daina jinin al'ada da kula da lafiya
Kula da lafiya da na matuƙa muhimmanci a lokacin da mace ta daina jinin al'ada. A wannan lokaci, akan ga alamomi masu yawa sakamakon sauye-sauyen da ake samu a kwayoyin halittar jiki.
Don haka yana da kyau mata su kula da lafiyarsu a wann lokaci, saboda daina jinin al'ada na haifar da wasu ƙarin matsaloli ga lafiyar jiki.
Yayin da hatsarin kamuwa da hawan jini ke ƙaruwa, hatsarin mauwa da cuiwon suga kan ƙaru, sannan kuma akan samu matsalar kitse a jiki, wanda kuma ke haifar da cutukan da suka shafi zuciya.
Ban da wannan, akan samu raguwar sidanrin calcium a cikin ƙasusuwa da jiki, wanda shi ma kan haifar da lalurorin da suka shafi ƙasusuwa
Ta ya za ki kauce wa matsalolin da daina al'ada kan haifar?
Matsalar daina al'ada kamar yadda muka bayyana na haifar da tarin matsaloli , don haka yana da kyau mu san yadda za mu kauce musu,
Motsa jiki
Wannan da matuƙar muhimmanci, don haka akwai buƙatar yawaita motsa jiki, don haka sai ki duba nau'in motsa jikin da za ki iya yi, amfanin hakan shi ne don jikinki ya zama yana aiki.
Abinci
Yana da kyau ki kula da abincin da za ki riƙa ci, da lokutan da ya mata ki riƙa cin abinci da shan abin sha.
Ki guje wa cin abincin da aka soya ko masu zaƙi. Ana bayar da shawarar yawaita amfani da garin waken suya, saboda yana ƙunshe da sinadaran da za su daidaita miki jikinki a lokacin da jinin al'ada ya daina zuwar miki.
Sannan ana so mace ta riƙa amfani da garin ragi, saboda yana ƙunshe da sinadaran calcium masu yawa a cikinsa. Garin ragi na da matuƙar muhimmanci ga lafiyar ƙasusuwa.
Haka kuma akwai buƙatar cin kayan marmari ga 'ya'yan itatuwa da ganyayyaki.
Ya kamata ki sauya yadda kike gudanar da rayuwarki domin dacewa da yanayin, dole ki tsara yadda za ki gudanar da rayuwarki, musamman abinci da abin sha da motsa jiki, da yanayin aiki.
A waɗanne shekaru ne mata ke daina al'ada?
A yanzu mata kan daina al'ada a shekara 30 zuwa 35. Hakan na nufin mata da dama kan daina al'ada a waɗannan shekaru.
Amma a wasu wuraren a duniya, mata kan daina al'ada tsakanin shekara 45 zuwa 50.
Me ke haddasa saurin zuwan daina al'ada?
Wasu na ganin hakan ba ya rasa nasaba da ire-iren abinci da muke ci a yanzu.
Mafi yawan abincin da muke ci yanzu a soyayyu ne ko gasassu. Haka kuma cin abinci mai nauyi na daga cikin abubuwan da ke haddasa daina al'ada da wuri.
Baya ga matsalar ingantaccen abinci, akwai kuma matsalar rashin motsa jiki, da tiriri mai ɗauke da guba da ke fita da wayoyin salula da talbijin duka waɗanna matsaloli ne da ke haddasa daina al'ada da wuri ga mata.
Don haka yana da matuƙar muhimmanci a ɗauki matakan inganta abincin da za mu riƙa ci da kuma motso jiki.
Haka kuma yana da kyau mu kauce wa shan giya ko abubuwan sha da ke ɗauke da sinadaran giya a cikinsu.
Idan muka kula da waɗannan ƙannana abubuwan, to ba za mu daina jinin al'ada da wuri ba, kuma mace ba za ta fuskanci wata matsala da hakan ke haddasawa ba.











