Waɗanne dokoki ne Trump ya sanya wa hannu a ranarsa ta farko?

Donald Trump a ranarsa ta farko cikin ofishin shugaban ƙasa a wa'adinsa na biyu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump a ranarsa ta farko cikin ofishin shugaban ƙasa a wa'adinsa na biyu
    • Marubuci, Christal Hayes & Phil McCausland
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News
  • Lokacin karatu: Minti 8

Bayan jerin umarnin shugaban ƙasa da ya sanya wa hannu jim kaɗan bayan rantsar da shi a ranar farko, ana sa ran Donald Trump zai ci gaba da sanya hannu kan irin waɗannan dokoki a kwanaki masu zuwa.

Nan take bayan shan rantsuwa, Trump bai tsaya ɓata lokaci wurin fara nuna ƙarfin da kundin tsarin mulki ya ba shi ba, inda ya fara ɗora harsasin tabbatar da manufofinsa.

Abubuwan da ya sanya wa hannu sun haɗa da batun shige da fice da sauyin yanayi da kuma yafiya ga mutanen da aka kama da laifi a kutsen da aka yi cikin ginin majalisar dokokin Amurka na Capitol a shekarar 2021.

Umarnin shugaban ƙasa tamkar dokoki ne da aka saba assasawa, sai dai shugaban ƙasa na gaba na iya soke su ko kuma kotuna. Yawancin dokokin da Trump ya sanya wa hannu na fuskantar ƙalubale na shari'a.

Sai dai wasu umarnin, kamar na fatar baki da shugaban ƙasa ke bayarwa ba su da gurbi ta fuskar doka.

Ga wasu daga cikin abubuwan da Trump ya yi a ranarsa ta farko...

Shige da fice

'Dokar ta-ɓaci'

Trump ya yi iƙirarin cewa "ƴancin Amurka na fuskantar barazana", bayyana hakan a matsayin babbar matsalar da ta shafi ƙasa zai ba shi damar sakin ƙarin kuɗaɗe ga ɓangaren ƙarfafa tsaron kan iyakar Amurka da Mexico.

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Kuma hakan wani sabon saƙo ne a hukumance na ƙoƙarin ci gaba da ginin katangar da ta raba Amurka da Mexico, wadda aka fara a wa'adin mulkinsa na farko. Wannan ba dokar umarnin shugaban ƙasa ba ce, babu tabbas kan yadda umarnin zai

yi aiki da kuma yadda za a iya ware wa ɓangaren kuɗi.

Rufe boda

Shugaban ƙasar ya umarci sojoji su "kulle iyakokin ƙasar" - bisa hujjar cewa miyagun ƙwayoyi na kwararowa cikin ƙasar sannan ana yin safarar mutane da ayyukan laifi ta iyakokin.

Samun takardar zama ɗan ƙasa ta haihuwa

Trump ya bayar da umarnin cewa jami'ai su daina bayar da takardar zama ɗan ƙasa ga jariran da baƙi suka haifa, waɗanda suka shigo ta bayan gida ko kuma waɗanda ke ƙasar na ƙanƙanin lokaci.

To amma an tabbatar da cewa gyaran doka na 14 na kundin tsarin mulkin Amurka ya tabbatar da ƴancin samun takardar zama ɗan ƙasa ga irin waɗannan jarirai, kuma nan take aka ƙalubalanci wannan mataki na Trump a gaban kotu.

Ayyana gungun masu safarar ƙwaya a matsayin ƴan ta'adda

Trump ya ayyana ƙungiyoyin masu safarar miyagun ƙwayoyi da kuma na masu aikata miyagun laifuka a matsayin ƴan ta'adda - inda ya sanya ƙungiyar MS-13 ta ƙasar El Salvador cikin jerin ƙungiyoyi kamar na Islamic State (IS).

'Umarnin jira a Mexico kafin samun takarda'

Trump ya dawo da dokarsa ta tilasta wa masu son shiga Amurka "jira a Mexico" wadda ya bijiro da ita a mulkinsa na farko. Lamarin ya sanya an mayar da ƴan ci-rani 70,000 waɗanda ba ƴan asalin Mexico ba zuwa cikin Mexico domin jiran makoma, kafin daga baya shugaba Joe Biden ya soke dokar.

Wannan doka ta kuma ƙunshi soke tsarin a 'kama a saki', tsarin da ke bai wa ƴan ci-rani ƴancin zama a cikin Amurka yayin da ake tantance buƙatarsu ta zama a Amurka. Dama Trump ya yi alƙawarin yin "korar baƙi mafi girma a tarihin Amurka", sai dai wannan manufa na iya fuskantar ƙalubale a gaban kotu.

Hukuncin kisa kan baƙin da aka kama da aikata laifi

Trump ya bayar da umarnin sake dawo da yanke hukuncin kisa a matakin tarayya. Ba a zartar wa wani da hukuncin kisa ba a baya-bayan nan. Za a yanke wannan hukuncin a kan "duk wani baƙon haure da ya aikata babban laifi a wannan ƙasar" da duk wanda aka kama da kisan jami'in tsaro.

Sake tsugunar da ƴan gudun hijira

Trump ya dakatar da shirin Amurka na tsugunar da ƴan gudun hijira, duk da dai babu cikakken bayani kan wannan.

Sauyin yanayi da makamashi

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Ficewa daga yarjejeniyar birnin Paris (karo na biyu)

Trump ya sanya hannu kan ficewa daga yarjejeniyar sauyin yanayi ta Paris - wata yarjejeniya mai muhimmanci da aka samar domin taƙaita ɗumamar yanayin duniya. Ya taɓa ficewa daga wannan yarjejeniya a shekarar 2017, kafin Biden ya sake shigar da Amurka.

'Makamashi'

Trump ya ayyana "dokar ta-ɓaci a kan makamashi", inda ya lashi takobin ƙara yawan mai da ƙasar ke adanawa. A cikin jawabinsa na shan rantsuwa ya yi alƙawarin "ƙara ƙaimi wajen haƙo mai."

Albarkatun mai na Alaska

Ya sanya hannu kan dokar "bankado albarkatun da ke Alaska", inda ya yi alƙawarin fito da man fetur da gas da sauran albarkatun ƙasa daga jihar.

Kawar ga yarjejeniyar kare sauyin yanayi ta 'Green New Deal'

Trump ya dakatar da yarjejeniyar 'Green New Deal', wasu jerin matakai da Biden ya fito da su da nufin bunƙasa samar da ayyuka a ɓangaren kare gurɓacewar muhalli, da sanya ido kan makamashi mai gurɓata muhalli domin taƙaita gurɓata muhalli.

Ya umarci hukumomi su dakatar da kuɗaden da aka ware wa ɓangaren.

Hukumar Lafiya ta Duniya

Trump ya sanya hannu kan wata dokar shugaban ƙasa domin fara janyewar Amurka daga Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya (WHO).

Wannan ne karo na biyu da Trump ke bayar da umarnin ficewar Amurka daga hukumar, bayan Biden ya sake mayar da ƙasar. Trump ya soki yadda hukumar ta tafiyar da al'amura a lokacin annobar korona.

Jinsi

Masu sauyin jinsi

Trump ya sanar cewa a yanzu Amurka za ta riƙa la'akari ne da "jinsi biyu kawai, mace ko namiji. Ba za a iya sauya waɗannan jinsuna ba kuma ba za a iya sauya su ba".

Wannan zai shafi manufofin gwamnati da suka jiɓanci mutanen masu sauya jinsi musamman a yanayin yadda ake ambaton mutane, kare hakki da kuɗin da gwamnati ke samarwa da kuma gidajen yari. Zai shafi takardun gwamnati da kuma takardun tafiya da na biza.

Haka nan dokar ta kawar da duk wasu shirye-shirye da manufofi na gwamnati da suke tabbatar da ƴancin zaɓen jinsi.

TikTok

Trump ya sanya hannu kan izinin tsawaita haramta amfanin da TikTok a Amurka da kwana 75.

TikTok ya ɗauke jim kaɗan kafin rantsar da Trump bayan hukuncin kotun ƙoli na haramta amfani da shi har sai an sayar da shi ga wani kamfanin Amurka.

Trump banner

Yafe wa mutanen da suka yi bore a Majalisa

...

Asalin hoton, Getty Images

Pardoning hundreds who stormed US Capitol

Trump ya sanar da cewa zai yafe wa kimanin magoya bayansa 1,600 waɗanda aka kama sanadiyyar boren da suka yi a ginin Majalisar dokokin ƙasar na Capitol a 2021.

Dama Trump ya sha bayyana magoya bayan nasa da aka kama a matsayin waɗanda aka yi garkuwa da su.

Sauyin harkokin gwamnati

Inganta aikin gwamnati da Elon Musk

Trump ya sanya hannu kan ƙirƙirar ma'aikatar inganta harkokin gwamnati da tsimi - wadda za ta taimaka wajen rage kudin da ake kashewa a harkar tafiyar da gwamnati.

Ana sa ran Elon Musk ne zai jagoranci ma'aikatar.

Dakatar da ɗaukar ma'aikata

Wata dokar ita ce ta dakatar da ɗaukan ma'aikatan gwamnati a matakin tarayya - amma ban da ɓangaren sojoji da wasu fannonin - har sai Donald Trump ya kafu a gwamnati.

Kowane ma'aikacin gwamnati ya koma aiki a ofis

Trump ya sanya hannu kan dokar da za ta umarci kowane ma'aikacin gwamnati ya koma aiki a ofis, babu sauran aiki daga gida.

Soke manufofin gwamnatin Biden

'Fifita muradun cikin gida'

Trump ya bayyana cewa zai dakatar da duk wani taimako da Amurka ke bai wa ƙasashen waje, ya ce yana son sake yin nazari kan taimakon da ƙasar ke bai wa wasu ƙasashe. Mai magana da yawun fadar White House Karoline Leavitt ta ce wannan na daga cikin tsarin Trump na 'Amurka a farko'.

Cuba

Trump ya soke matakin da Biden ya ɗauka na cire Cuba da jerin ƙasashen da Amurka ta ayyana a matsayin masu taimaka wa ta'addanci. Kuma akwai yiwuwar zai sake ƙaƙaba takunkumai kan Venezuela.

Dakatar da ɗaukan matakai

Trump ya umarci hukumomin gwamnati su dakatara da bayar da duk wani sabon umarni har sai gwamnatinsa ta kafu kan mulki.

Mayar da ma'aikatan da aka kora kan ƙin yin rigakafi

Trump ya soke matakin gwamnatin Bidenna wajabta wa ma'aikatan gwamnatin tarayya yin rigakafin korona. Ya sha alwashin mayar da sojoji 8,000 da aka sallama daga aiki sanadiyyar tsarin Amurka na wajabta yin rigakafin korona.

Tattalin arziƙi

Magance tsadar rayuwa

Trump ya sanya hannu kan dokar da ta wajabta wa duk wata ma'aikatar gwamnatin ƙasar ɗaukar mataki kan rage tsadar rayuwa. Dokar ta buƙaci ma'aikatu su duba hanyoyin rage tsadar gidaje da kula da lafiya da man fetur da kuma kayan masarufi.

Dokar ta buƙaci ma'aikatun gwamnati su bayar da rahoto kan ƙoƙarin da suka yi a wannan fanni cikin kwana 30. Babu tabbas game da hanyoyin da gwamnatin Trump ke son ta bi wajen rage tsadar rayuwa, sannan babu bayanai cikakku kan yadda wannan umarni za ta yi aiki.

Sauya sunan mashigin Mexico

'Mashigin Amurka'

Trump ya umarci sakataren harkokin cikin gida ya sauya sunan Mashigin Mexico zuwa 'Mashigin Amurka'.

Abubuwan da Trump bai taɓo ba - tukuna

Haraji

Bayan ɗamarar da ta sha na shiga yaƙin kasuwanci tsakaninta da Amurka, ya zuwa yanzu Canada ta sha - daga haraje-harajen da Trump ya yi alƙawarin lafta mata da zaran ya kama aiki.

Amma Trump ya bayyana cewa akwai yiwuwar harajin da yake son lafta wa Canada da Mexico zai fara ne daga ranar 1 ga watan Fabarairu, sannan ya umarci jami'an gwamnati su sake duba alaƙar kasuwancin Amurka da sauran ƙasashe, ciki har da Canada da Mexico da kuma China.

Takardun sirri

A wani taro a ranar Lahadi, Trump ya ce zai saki takardun sirri da dama waɗanda suka shafi kisan Shugaban Amurka John F Kennedy a 1963, wani lamari da ya janyo saci-faɗi da dama, da kuma kisan Sanata Robert Kennedy na shekarar 1968 da na Martin Luther King Jr.

Rumbun kirifto

Wasu na da yaƙinin cewa Trump zai yi azama wajen samar da rumbun kuɗin kirifto na Amurka, kamar yadda Amurkar ke da rumbun zinare da man fetur - wanda ya ce zai zamo ɗaya daga cikin manyan kadarorin Amurka da zai amfani al'umma.