Yadda Trump ke fatan sauya fasalin Amurka a mulkinsa karo na biyu

Asalin hoton, Getty Images
Kowane shugaban ƙasa aka rantsar a Amurka, tamkar buɗe sabon babi ne na ƙasar.
Kuma a lokacin da aka rantsar da Donald Trump karo na biyu a matsayin shugaban ƙasa, yayin da ake mamakon sanyi a birnin Washington DC, manufarsa za ta zamo kafa sabon tarihi.
Bikin rantsarwar da aka yi a ƙarƙashin ƙwaryar ginin Majalisar dokokin Amurka na Capitol, shi ne karo na farko da aka gudanar da irin wannan rantsuwa a cikin ɗakin taro a tsawon shekaru.
Trump ya yi alƙawarin kawo sauye-sauye da ma wasu manyan ayyuka a ranarsa ta farko.
A lokacin wani gangami a birnin Washington a ranar Lahadi, Trump ya ce zai sanya hannu kan wasu jerin umurni na zartarwa cikin ƙanƙanin lokaci bayan kama aiki, waɗanda za su shafi shige da fice ba bisa ƙa'ida ba, abubuwan da suka shafi muhalli da kuma haƙƙoƙin masu sauya jinsi.
''Za ku yi farin ciki sosai a lokacin da kuke kallon talibijin gobe,'' ya shaida wa gwamman mutanen da ke wurin.
Sai dai, ko da gwamnatinsa ta fara da waɗannan manyan al'amuran, duk da haka akwai ayar tambaya kan yadda mulkin Trump karo na biyu zai zama.
Shin za mu ji girgizar ƙasa a ƙarƙashin ƙafafuwanmu a lokacin da ya kama aiki? Zai iya cika alƙawuran da ya ɗauka? ko zai yi munin da ƴan hamayya ke cewa?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Idan ka ji wasu daga cikin kalamansa na suka, za a iya yafe maka idan ka yi tunanin cewa samaniya za ta turnuƙe kuma tsuntsaye za su fice daga Washington a lokacin da ya sha rantuswar kama aiki.
Mutane da dama na nuna damuwa kan cewa zai yi ƙoƙarin yin mulkin mallaka wanda hakan zai zama barazana ga dimokraɗiyyar Amurka.
Wanda ya gabace shi, Joe Biden, ya yi gargadi a jawabinsa na ƙarshe a kan mulki kan cewa wasu ƙungiyar masu kuɗi da ke da haɗari, masu ƙarfin faɗi a ji za su kewaye Trump, wanda kuma hakan barazana ce ga ƴanci Amurkawa.
Sai dai babu wanda zai musanta cewa Trump, mai shekaru 78, na da manufofi da suka fito ƙarara bayan nasarar sa a zaɓen da aka gudanar a watan Nuwamba.
Ya yi nasara a jimillar yawan ƙuri'ar da aka kaɗa a faɗin ƙasa da kuma na wakilan masu zaɓe da aka fi sani da Electoral colleges. Ya kuma yi nasara a zaɓen jihohi masu muhimmanci. Ajandarsa ta samu ƙarbuwa ga masu kaɗa ƙuri'a.
A wannan karon, Trump na da yaƙinin cewa za a zartar da manufofinsa.
Ya na da tawagar ƙwararru masu yi masa biyayya matuƙa, tare da shi da za su tabbatar da hakan.
Ya na kuma da niyyar- mai yiwuwa da taimakon ''sashen kula da ingancin ayyukan gwamnati'' da ke ƙarƙashin Elon Musk - sallamar adadi mai yawa na ma'aikatan gwamnati da manyan ma'aikata.
Har ila yau Trump yana da yaƙinin cewa akwai wasu a cikin gwamnatin Amurka da za su yi ƙoƙarin kawo tsaiko ga manufofinsa.
A don haka za a iya sa ran ganin sallamar ma'aikatan gwamnati fiye da yadda aka saba gani idan an sauya gwamnati.
Akasarin shirye shiryensa, kamar rage haraji ga manyan kamfanoni da masu kuɗi, zai buƙaci amincewar majalisa.
Sai dai hakan ba zai zama matsala ba ganin cewa ya na da iko kan jamiyyar Republican da mafiya yawan ƴan jam'iyyar a majalisun biyu.
Da wuya Sanatoci da ƴan malajisar wakilai su bijire masa. Kuma yana da Elon Musk, wanda zai iya yin amfani da sahfinsa na sada zumunta da kuna dukiyarsa ya dawo da duk wanda ya bijire kan hanya.

Asalin hoton, Getty Images
Shin akwai abin da zai hana Trump tattarawa tare da korar miliyoyin baƙin haure da ke ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, da kuma amfani da ɓangaren shari'a wajen muzguna wa ƴan adawa da yake kallo a matsayin maƙiyansa?
Babu shakka za a samu matsaloli ta fannin jigila da kuma fannin kuɗi, musamman wajen korar baƙin hauren, sai dai adawar jam'iyyar Democrats kaɗai ba ta isa ta hana yin hakan ba. Ko da yake ma jam'iyyar ba ta gama farfaɗowa daga rashin nasarar da ta yi a zaɓen ba.
Akwai ɓaraka a cikin jam'iyyar a yayin da ƴaƴan jam'iyyar suka shafe tsawon lokaci su na bahasi kan sakamakon zaɓen da ya gabata.
Su kuma ƙungiyoyin ƴan tawaye da suka tattaru gabanin wa'adin mulkin Trump na farko, suka ƙaddamar da zanga-zangar gama-gari na tsawon kwanaki bayan rantsar da shi wanda ya kai ga miliyoyin mutane fitowa kan tituna, a wannan karon da alamu ba su da ƙarfin gwiwar sake yin hakan.
Bayan rashin nasararsa a zaɓen 2020, an kori Trump daga shafukan sada zumunta sakamakon boren da mabiyansa suka yi a majalisa da kuma zarge-zarge marasa tushe da ya yi kan maguɗin zabe.
A wannan karon kuwa waɗannan kamfanonin na sake sabuwar mu'amula da shi.
Wasu daga cikin mutanen da suka fi kowa arziƙi a duniya sun zauna a ɓangaren da aka ware wa baƙi na musamman domin shiada bikin rantsuwar.

Asalin hoton, Getty Images
Elon Musk, Jeff Bezos da Mark Zuckerburg duk sun halarci taron.
Waɗannan mutanen duk sun sabunta mu'amularsu da Trump. Kamfanin Zuckerburg mai suna Meta ya yi watsi da binciken sahihancin bayanai a shafukansa na Facebook da Instagram, shi kuwa Bezos ya hana jaridar Washington post (wanda mallakinsa ne) goyon bayan Kamala Harris. Kuma dukkaninsu sun bayar da gudunmawar miliyoyi zuwa asusun bikin rantsar da Trump.
Trump zai ƙarbi mulki a wannan karon da tarba ta musamman daga masu ƙarfin faɗa a ji a Amurka, na ɓangaren majalisa da ma manyan kamfanoni.
Babu shakka rattaba hannu da zai yi kan wasu jerin dokoki na umarnin shugaban ƙasa a ranarsa ta farko zai ƙunshi wasu ayyuka da za su janyo hankali kansa. Ciki har da yin afuwa ga mafiya yawa, ko kuma dukkanin waɗanda aka yanke wa hukunci kan zanga-zangar da mabiyansa suka yi a majalisa.
Mabiyansa za su yi farin cikin ganin waɗanda suke kallo a matsayin waɗanda aka kulle saboda siyasa sun shaƙi iskar ƴanci.
Trump zai buƙaci ci gaba da irin waɗannan abubuwan na burge mutane. Saboda akwai fargabar wasu daga cikin tsare-tsarensa ba za su yi daidai da abin da wani ɓangare na mabiyansa ke so ba.
Akasarinsu na buƙatar farashin kaya su yi sauƙi bayan shafe shekaru ana samun hauhawar farashin kaya. Sai dai ƙawararru a fannin tattalin arziƙi da dama na ganin sanya haraji kan kayan da ake shigowa da su zai iya ƙara tsadar kayyayakin.
Ƙorar miliyoyin baƙin haure za ta iya haifar da ƙarancin ma'aikata musamman a fannin gine-gine - wanda hakan zai yi karo da alƙawarinsa na gina gidaje da dama - da kuma fannin noma wanda hakan zai ƙara hauhawar farashin abinci.
Kuma masu kuɗi ne za su amfana da rage haraji mafi girma da za ayi, ba ma'aikata ba.
Tsare-tsarensa masu jan hankali kamar alƙawarin canza sunan Gulf of Mexico zuwa Gulf of America zai iya zama abin farin ciki ga waɗanda suka zaɓe shi. Sai dai ana zuba ido domin ganin yadda akasarin Amurkawa za su amfana da manyan tsare-tsarensa.
Sai dai Trump ya kasance ɗan siyasa mai burga. Iya nishaɗantarwar Trump wani ɓangare ne na ƙarfin ikonsa da kuma burgewa.
Sai dai manufofinsa na wa'adin gwamnatinsa na biyu sun zarce burga kawai, za su iya kawo sauyi idan aka zartar da su.
Dawowarsa gwamnati karo na biyu zai kasance cike da abubuwa masu ban mamaki waɗanda za a ji tasirinsu a faɗin duniya. Hakan zai iya sauya tarihin Amurka da kuma ɗorewarta.











