Donald Trump ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 47

Donald Trump a lokacin da yake shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 47

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump a lokacin da yake shan rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban Amurka na 47
Lokacin karatu: Minti 3

Donald Trump ya sha rantsuwa a matsayin shugaban Amurka na 47, bayan nasarar da ya yi a zaɓen shugaban ƙasar na 2024.

An rantsar da Donald Trump ne a cikin ginin Majalisar Dokokin ƙasar na Capitol, karon farko a cikin shekaru.

Gabanin Trump, an rantsar da mataimakinsa, kuma tsohon mai sukarsa, JD Vance.

Jim kaɗan bayan shan ranstuwa, Trump ya sanar da wasu tsauraran matakai da zai ɗauka, musamman a ɓangaren tsaron iyaka da kuma rage kwararar baƙi zuwa ƙasar.

Wani abin kuma shi ne yadda Trump ya riƙa sukar magabacinsa, Joe Biden, a gabansa, jim kaɗan bayan shan rantsuwa.

Donald Trump ya dawo kan mulki ne bisa alƙawarin kawo tsauraran sauye-sauye waɗanda suka sha bamban da na Biden.

A jawabinsa na farko, Trump ya ce ''Sabon babin ci gaban Amurka zai fara ne daga yau''.

''Daga yau, ƙasarmu za ta fara samun ci gaba kuma za a mutunta ta a duniya''

"Zan sanya muradun Amurka a gaban komai."

Abubuwan da Trump zai yi a ranar farko bayan shan ranstuwa

Donald Trump ya yi jawabi jim kaɗan bayan rantsar da shi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Donald Trump ya yi jawabi jim kaɗan bayan rantsar da shi

Shige da fice:

  • Trump zai ayyana dokar ta-ɓaci a kan iyakar ƙasar don aikewa da ƙarin sojoji da ma'aikata
  • Zai umarci jami'ai su ci gaba da ginin katangar kan iyakar Amurka da Mexico
  • Shugaban na son soke izinin zama ɗan ƙasa ga ƴaƴan baƙin haure da suka shiga Amurka ba bisa ƙa'ida ba
  • Yana shirin mayar da tsarin da ake kira 'Remain-in-Mexico', wanda ke buƙatar baƙi su yi zaman jira a Mexico yayin da suka miƙa buƙatar neman mafaka.

Tattalin Arziki:

  • Trump na shirin kafa dokar ta-baci a ɓangaren makamashi na ƙasar, wanda a cewarsa zai bai wa ƙasar damar samar da albarkatun ƙasa da kuma samar da ayyukan yi.
  • Har ila yau, yana son "kawo ƙarshen batun tilasta aiki da motoci masu amfani da lantarki" da kuma ƙoƙarin da ake yi na daƙile zaɓin masu amfani kayayyaki, a cewar gwamnatinsa.
  • A cewar jaridar Wall Street, Trump na shirin bai wa gwamnati umarnin sake fasalin alaƙar kasuwancin tsakanin Amurka da China - amma bai shirya sanya sabbin haraji ba.

Batutuwan da suka shafi jinsi:

  • Yana shirin aiwatar da dokar da za ta kawo ƙarshen tsarin DEI, wanda ke tabbatar da daidaito kan batun jinsi a cikin gwamnatin tarayya"
  • Wani umarni na zartarwa zai "bayyana cewa manufar Amurka ce ta tabbatar da jinsi biyu kaɗai- namiji da mace" waɗanda ba za a iya sauya su ba.