Fitattun mutane 10 da Trump ya zaɓa domin aiwatar da manufofinsa

President Trump. Behind him is the American flag and prominent political figures: Kristi Noem, Homeland security secretary. Elon Musk, Government efficiency. Also, Marco Rubio, Secretary of state
    • Marubuci, Bernd Debusmann Jr
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Journalist
  • Lokacin karatu: Minti 8

Donald Trump ya sha alwashin kawo sauye-sauye masu matuƙar tasiri daga ranar da ya karɓi mulkin Amurka a karo na biyu, a ranar 20 ga watan Janairu.

Kusan dukkanin mutanen da ya bai wa muƙamai, suna da ɗabi'a iri ɗaya - matuƙar biyayya gare shi.

To amma kowannensu na da nasa ra'ayoyin kan yadda za su tabbatar da manufofin shugaba Trump.

Za mu duba wasu daga cikin wadannan mutane, ƙwarewarsu, da kuma matsalolin da ke tattare da su sannan mu ji abin da masharhanta ke cewa a kansu.

Shige da fice: Masu tsaurarawa kan ƴan ci-rani

Wannan na daga cikin manyan alƙawurran da Trump ya ɗauka a lokacin yaƙin neman zaɓe - wato kare kan iyakokin Amurka da kuma korar mutanen da suka shigo ƙasar ba bisa ƙa'ida ba.

Ya yi alƙawarin yin korar baƙi mafi girma a tarihi - wadda ra'ayin jin ra'ayin al'umma ta nuna cewa mutane da dama na goyon baya.

Amma babu tabbas kan yadda za a aiwatar da hakan.

Kristi Noem, Homeland security secretary
Bayanan hoto, Kristi Noem, Sakatariyar tsaron cikin gida

Kristi Noem, Sakatariyar harkokin tsaron cikin gida

"Abu na farko da kowane baƙo ya shigo ƙasarmu ke yi shi ne su karya doka."

Matar, wadda ƴar majalisar dokoki ne karo huɗu, wadda ta zama gwamnar jihar South Dakota a 2018 ta ja hankalin al'umma ne lokacin da ta fito fili ta nuna ƙiyayya da dokar sanya takunkumi hana yaɗuwar korona da kuma na zaman gida.

Ta daɗe tana sukar matakan tsaron kan iyaka na gwamnatin shugaba Biden.

Noem ta ƙi ta amince da ƴan gudun hijira daga ƙasar Afghanistan, kuma ita ce mai muƙamin gwamna ta farko da ta tura jami'an tsaro daga jiharta domin su tallafa wa dakarun tsaron kan iyaka na Amurka.

Tom Homan, Border tsar
Bayanan hoto, Tom Homan, kwamandan tsaron bakin iyaka

Tom Homan, Kwamandan boda

"Wannan ne hatsarin tsaro mafi girma da ƙasarmu ta faɗa ciki tun bayan harin 9/11 kuma wajibi ne mu gyara."

Kasancewar ya kwashe gomman shekaru yana aiki a matsayin jami'in tabbatar da tsaron bakin iyaka, tsohon ɗansandan wanda ya taɓa shugabantar hukumar shige da fice da kuma ta hana-fasa-ƙwauri, da alama ya dace da muƙamin.

Yana daga cikin mutane na farko da suka goyi bayan raba iyaye da yaransu, waɗanda suka tsallaka kan iyaka zuwa cikin ƙasar ba bisa ƙa'ida ba, wani tsari na wa'adin mulkin Trump na farko mai cike da ruɗani.

Red line

Sharhi: Aiwatar da samame

Baya ga batun tattalin arziƙi, ƙuri'un jin ra'yoyin al'umma sun nuna cewa batun shigar baƙi musamman ta kan iyaka da Mexico na daga cikin manyan abubuwan da suka fi damun Amurkawa masu kaɗa ƙuri'a. Zaɓen Homan da Noem da kuma Stephen Milner su jagoranci ɓangaren na nuni da cewa da gaske Trump yake yi domin sauke alƙawarin da ya ɗauka.

Sai dai ƙudurinsa na yin korar da ba a taɓa gani ba da kuma kai samame a wuraren aiki domin kama baƙin haure abu ne da zai iya janyo masa matsala a jihohin da ke da rinjayen ƴan jam'iyyar Democrat.

red line

Manufofin ƙetare: Maƙiyan China

Masu tsattauran ra'ayi da dama sun yi amannar cewa China ce babbar barazana ga Amurka a yunƙurin Amurkar na kankane harkar tattalin arziƙi da kuma na soji a duniya.

Duk da cewa Trump ya kasance mai taka-tsantsan, amma da alama ya cika ɓagaren kula da harkokin waje na gwamnatinsa da masu sukar China, waɗanda da alama za su yi ƙoƙarin ganin manufar Trump ta tsawwala kuɗaɗen haraji kan kayan Chinata samu amincewa.

Marco Rubio, Sakataren harkokin waje
Bayanan hoto, Marco Rubio, Sakataren harkokin waje

Marco Rubio, Sakataren harkokin waje

"Babbar barazanar wannan ƙarni ita ce China. Kuma muna buƙatar haɗin kan kowa da kowa domin cimma su."

Sanatan, wanda ya wakilci Florida tun daga shekara ta 2011, Ba-Amurken ɗan asalin ƙasar Cuba, Rubio gogaggen jami'in gwamnati ne wanda a baya ya taɓa sukar Trump.

Rubio da Trump sun yi zazzafar adawa da juna lokacin da Rubio ya yi yunƙurin tsayawa takarar shugabancin ƙasa ƙarƙashin jam'iyyar Republican a 2016, sai dai daga baya ya nuna goyon baya ga Trump.

Mutumin ya yi ƙaurin suna game da tsattsauran ra'ayinsa kan Iran da kuma samamen da Rasha ta kai cikin Ukraine da kuma China.

Har yanzu mutumin mai shekara 53 na da aniyar zama shugaban Amurka, kuma zai iya yin amfani da matsayin nasa wajen ƙara fito da kansa.

Michael Waltz, National security adviser
Bayanan hoto, Michael Waltz, Mai bayar da shawara kan tsaro

Michael Waltz, Mai bayar da shawara kan tsaro

"Gwamnatoci kan rikiɗe zuwa na kama karya ne sanadiyyar kallon rauni da ake yi musu, koda gaskiya ne ko kuma a'a - tunaninsu ne kawain."

Tsohon sojin da ya samu yabo, Waltz ɗan majalisar dokoki ne mai daga Florida, kamar Rubio.

Shi ma sanannen mai sukar lamirin China ne.

A shekarar 2022, Waltz na daga cikin wakilan majalisa da suka buƙaci Amurka ta ƙaurace wa gasar guje-guje da tsalle-tsalle (Olympics) a Beijing.

Ya soki lamirin manufofin gwamnatin Biden, musamman janye dakarun Amurka daga Afghanistan.

red line

Sharhi: Alaƙa mai muhimmanci

A mulkinsa na farko, Trump ya haifar da yaƙin cinikayya tsakanin Amurka da China, sannan ya bayyana cutar korona a matsayin "cutar China". Amma ya yabi shugaban Xi Jinping, inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai mulkin ba-sani ba-sabo. Wannan rashin matsaya ɗaya zai sanya saita alaƙar Amurka da China ya zamo abu mai sammatsi.

Red line

Tsimi: Masu tsuke bakin aljihu

Trump ya naɗa manyan masu ruwa da tsaki a harkar ƙere-ƙere - Elon Musk da Vivek Ramaswamy - domin jagorantar "Ma'aikatar tsimi ta gwamnati" a matsayin wani yunƙuri na kawar da abubuwan da ke kawo cikas wajen tafiyar da lamurran gwamnati.

Musk ya yi bayanin cewa za a iya rage yawan kudin da gwamnati ke kashewa da kimanin dala tiriliyan biyu, inda ya yi iƙirarin cewa zai "girgiza gwamnati".

Ramaswamy ya goyi bayan soke ma'aikatar tara haraji ta IRS da kuma ma'aikatar ilimi ta ƙasar.

Elon Musk, Government efficiency
Bayanan hoto, Elon Musk, inganta harkokin gwamnati

Elon Musk, Inganta harkokin gwamnati

Msuk, wanda aka haifa a Afirka ta Kudu, shi ne ya mallaki kafar sada zumunta ta X, da kamfanin ƙera motar Tesla da kuma kamfanin ƙera kumbon sararin samaniya na SapceX, shi ne mafi arziƙi a duniya.

Vivek Ramaswamy, Government efficiency
Bayanan hoto, Vivek Ramaswamy, Inganta harkokin gwamnati

Vivek Ramaswamy, Inganta harkar gwamnati

Ba-Amurken ɗan asalin ƙasar Indiya ya tara dunkiya ne a matsayin ɗan kasuwa a ɓangaren ƙirƙire-ƙirƙire daga halittu sannan kuma ya kafa kamfanin lura da kadarori.

Ya goyi bayan ganin an rage kuɗin da ake kashewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati, ciki har da sallamar ma'aikata da kuma rufe ma'aikatun gwamnati da dama.

Red line
Robert F Kennedy Jr,
Health and human services
Bayanan hoto, Robert F Kennedy Jr, Harkokin lafiya

Robert F Kennedy Jr, Harkokin lafiya

Trump ya zaɓo daɗaɗɗen lauya kuma masanin muhalli wanda ya fito daga ɗaya daga cikin iyalan da suka fi suna ƴan jam'iyyar Democrat.

Duk da cewa ba ya da wata ƙwarewa ko gogewa a harkar lafiya, yanzu zai zamo mai matuƙar ta-cewa a kan hukumomin da ke tafiya da lamurran lafiya da dama - ciki har da hukumomin da ke kula da rigakafi, waɗanda ya ce zai iya sauya yadda suke tafiyar da ayyukansu.

Ya sha yin kalamai da dama waɗanda ake ganin na cike da kurakurai.

Tulsi Gabbard, National intelligence
Bayanan hoto, Tulsi Gabbard, tattara bayanan sirri na ƙasa

Tulsi Gabbard, Tattara bayanan sirri

Tsohuwar soja, wadda ta yi aiki a matsayin likitar sojoji a Iraqi, tana yawan sukar manufofin harkokin waje na Amurka.

Gabbard, wadda ta taɓa ganawa da tsohon shugaban Syria, Bashar al-Assad, inda ta nuna tababa kan bayanin sirri da Amurka ta tattara wanda ya zarge shi da amfani da makamai masu guba.

Bayan samamen da Rasha ta ƙaddamar a Ukraine, Gabbard ta soki Nato sannan ta sake nanata iƙirarin Rasha na cewa akwai wani ɗakin haɗa sinadaran guba a Ukraine, wanda Amurka ke samar wa kuɗin gudanar da aiki.

Red line

Tattalin arziƙi: Masu ƙaƙaba haraji

Jami'an da Trump ya zaɓa za su jagoranci ƙaƙaba haraji da manufofin kasuwanci, wadanda Trump ya ce za su samar da ayyukan yi ga Amurkawa.

Howard Lutnick,
Commerce secretary
Bayanan hoto, Howard Lutnick, Sakataren kasuwanci

Howard Lutnick, Sakataren harkokin kasuwanci

Lutnick hamshaƙin biloniya ne, wanda ke shugabantar kamfanin harkokin kuɗi na Cantor Fitzgerald.

Kasancewar yana cikin wadanda suka fi bai wa Trump gudumawar kuɗi a lokacin yaƙin neman zaɓe, an naɗa shi shugaban kwamitin karɓar mulki na Trump.

Ya sha nuna goyon baya ga manufofin tattalin arziƙi na Trump, ciki har da harajin da ya ce zai lafta wa kayan da ake shigowa da su daga waje.

Scott Bessent, Treasury secretary
Bayanan hoto, Scott Bessent, Ma'aji

Scott Bessent, Ma'aji

Bessent gogaggen masanin harkokin kudi ne, wanda ake ganin ya cancanci wannan muƙami.

Ya zamo mai goyon bayan manufofin masu ra'ayin ƴan mazan jiya, goyon bayan tsuke bakin aljihun gwamnati da kuma haɓɓaka ɓangaren samar da man fetur na Amurka.

Duk da cewa yana goyon bayan manufofin Trump na lafta haraji mai yawa kan kayan ƙasar waje, Lutnick ya bai wa Trump shawarar amfani da haraji a matsayin hanyar cimma yarjeniyoyi amma ba a matsayin harnyar kuɗaɗen shiga ga ƙasar ba.

Red line

Sharhi: Makamin tattaunawa na Trump

Trump ya sha nuna sha'awarsa ta lafta haraji - a matsayin hanyar bunƙasa tattalin arziƙi da kuma domin matsa wa wasu ƙasashen lamba kan abubuwa da dama. Mutanen da Trump ya zaɓa a ɓangaren tattalin arziƙi na daga cikin mafiya ƙwarewa a gwamnatinsa. Duk da cewa masu biyayya ne ga Trump, to amma sassaucin ra'ayinsu zai kwantar da hankulan masana harkokin kasuwanci.

Red line

Waɗanda suka rubuta: Anthony Zurcher, Laura Blasey, James FitzGerald, Tom Geoghegan, Bernd Debusmann Jr, Natalie Sherman, Tom Bateman da Mike Wendling. Tsarawa: Oliver Bothwell, François de Montremy da Jenny Law. Haɗawa da bita: Tom Finn, Paul Sargeant da Dominic Bailey.