Ana zaman sauraron ra’ayin jama’a kan gyaran dokar masarautu a Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto

Asalin hoton, AHMED ALIYU FACEBOOK PAGE

A yau Talatar nan ne kwamitin da Majalisar Dokokin jihar Sokoto ta miƙa wa ƙudurin dokar gyaran fuska ga masarautu zai fara zaman sauraren ra’ayin jama’a game da dokar da ta shafi ƙanannan hukumomi da masarautu.

Tun da farko gwamnatin jihar ta ce zai yi gyara ne ga sashe na 76, kashi na biyu na dokar ƙananan hukumomin jihar ta shekarar 2008.

An riga an yi wa dokar karatu na farko da na biyu a wani zama da aka yi ranar Talatar makon jiya, inda ake sa ran da ƙudurin ya zama doka, ƙarfin ikon nadawa da cire hakimai da dagatai zai koma ƙarƙashin ikon gwamnan jihar Sokoto, maimakon Sarkin Musulmi.

Dokar ta shafi damar da Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ke da ita, kan naɗa hakimai da dagatai kai tsaye, inda ikon hakan zai koma hannun gwamnan jihar da zarar dokar ta tabbata.

Sai dai lamarin na ta haifar da ce-ce-ku-ce, inda jama’a da dama a Najeriya suka bayyana matakin da shirin rage ƙarfin ikon Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku.

Daga cikin waɗanda suka mayar da martini har da ƙungiyar Muslumi ta Najeriya Muric, da ta bayyana cewa taɓa kimar Sarkin Musulmin tamkar taba ruhin Musulman Najeriya ne.

Haka kuma, a cikin jawabin da ya gabatar ranar Litinin ta makon jiya, a wajen taro kan matsalar tsaron da ke addabar jihohin arewa maso yammacin Najeriya, mataimakin shugaban Najeriya, Kashim Shettima shi ma ya ce dole ne a kare martabar Sarkin Musulmin.

Wannan ma ya jawo wasu ‘yan majalisa na ɓangaren jam’iyya mai hammaya ta PDP a jihar suka bayyana cewa babu wani muhimmanci ga sabuwar dokar face wata manufa ta bi-ta-da-kulli irin na siyasa.

A cewarsu, gwamnatoci da dama sun bar dokar a yadda take cewa Sarkin Muslumi ne mai alhakin nadawa da cire sarakuna da hakimai da ke ƙarƙashin ikonsa, ba gwamnan jiha ba.

Sai dai a wani martani da ta mayar, gwamnatin jihar ta Sokoto ta ce dokar da aka yi wa karatu na farko da na biyu da kuma aka miƙa ga kwamitin da zai gudanar da sauraren ra’ayin jama’a a ranar Talatar nan ba ta da wata manufa face mayar da tsarin naɗin hakimai da dagatai zuwa yadda ya kasance tun fil-azal.

Kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Sambo Bello Danchadi ya ce: “Dokar kawai za ta sake dawo da tsarin da ake amfani da shi ne a gomman shekaru da suka gabata.”

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Idan ana iya tunawa a baya a cikin watan Afirilu gwamnatin jihar Sokoto ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Ahmed Aliyu Sokoto ta ɗauki matakin sauke hakimai 15 daga kan muƙamansu.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin jihar ta fitar a ranar 23 ga watan Afirilun shekaran nan, wadda ta samu sa hannun sakataren yaɗa labarun ofishin gwamnan jihar, Abubakar Bawa, ta ce an sauke su ne bisa dogaro da shawarwarin kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa domin sake duba naɗe-naɗen sarauta da sauya wa kadarorin gwamnati suna.

Sanarwar ta ce hakiman da abin ya shafa sun hada da na Unguwar Lalle da Yabo da Wamakko da Tulluwa da Illela da Dogon Daji da Kebbe da Alkammu da kuma Giyawa da sauran su.

An zargi wasunsu da rashin biyayya ga gwamnati da neman rura wutar rashin tsaro da mallakar kadarorin gwamnati ta haramtacciyar hanya.

Sai kuma waɗanda aka ce an cire sanadiyyar rashin bin ƙa’ida wajen naɗinsu ko kuma rashin samun karɓuwa tsakanin al’ummarsu.

Wannan jin sauraren ra’ayin jama’a da ya haɗa da ɓangarori daban-daban da suka haɗa da na gwamnatin jihar da malamai da masana shari’a da sauran al’umma shi ne zai iya zama zakaran gwajin dafin makomar wannan doka da aka mayar da hankali a kai.

Dokar da ake ganin ƙarfin ikon masarauta na son komawa ga hannun gwamnatin jihar ta Sokoto.