Mutum shida sun mutu a rikici tsakanin ƴan bindiga da ƴan banga a Sokoto

A Najeriya, wani rikici da ya auku tsakanin 'yan bindiga da 'yan banga a garin Gada na jihar Sakkwato ya yi sanadin mutuwar mutum akalla shida, ciki har da wasu kwamandandojin 'yan banga biyu.
Wannan lamari ya faru ne yayin da matsalar hare-haren 'yan bindigan ke ci gaba da addabar jama'ar yankin na Gada.
Wani mazaunin garin ya bayyanawa BBC cewar: ''Ranar Alhamis da 'yan bindigar suka kaiwa wani kwamandan 'yan banga farmaki inda suka kashe shi nan take, ranar Juma'a kuma suka tare wani kwamandan a hanya tare da 'kaninsa suka kashe shi bayan sun sassara 'dan'uwansa da adda.
Duk da ya ke 'kura ta lafa mutumin mazaunin garin na Gada ya bayyana cewar, sun jima suna fama da hare-haraen 'yan bindida. '' Tsawon shekaru uku, idan maraice ya yi sai magidanta su fita wajen gari 'dauke da fitilu da makamai suna gadi ya yinda a wasu garuruwan da maraice ta yi wasu ko sallar Isha'i ba sa iya samun yi zasu fita wajen gari kuma ba zasu dawo ba sai da asuba, idan ka ga an bar mutum cikin gari, to tsoho ne amma duk wani mai jin 'karfi ko mace ko namiji ko yara zasu tsere daji su 'buya su kwanta ba zasu koma gida ba sai da asuba. A wasu yankunan ko noma ba a yi isan gonaki sun yi nisa da gari saboda ko da 'yan bindigar basu 'dauke mutum to suna yi masa duka''.
Ta'adin da 'yan bindiga suka yiwa mazauna Gada
Wani magidanci a garin na Gada ya ce 'yan bindiga sun kore musu dabbobi, sun kuma kashe mutane da dama tare da sace wasu da ba a san adadinsu ba, a wasu lokutan idan suka sace mutum sai iyalai da dangi sun bi garuruwa neman taimakon kudi don a samu su sako shi.
Babban abinda ya ke ciwa la'ummar yankin tuwa a 'kwarya shi ne yadda 'yan bindigar suke kwashe mata su kai su daji suna cin zarafinsu, ko kuma su sace mai jego su bar jariri al'amarin da ya sa magidanta da dama sun tsere sun bar iyalinsu a halin ni 'ya su.
Wanne Mataki Jami'an Tsaro suka dauka?
ASP Ahmed Rufa'i shi ne kakakin 'yan sanda a jihar sokoto ya bayyana cewar: Wasu mutane da ake zargin 'yan bindiga ne ko 'yan banga sun kutsa wata kasuwa a garin Gada inda suka kama wasu mutane kusan shida wa'danda daga baya aga gano gawarwakinsu a gefen kasuwar, al'ummar garu sun sanar da 'yan sanda kuma 'yan Sanda sun je kan gawarwakin wadanda aka tabbatar da mutuwarsu. Har yanzu jami'an tsaro na ci gaba da bincike tare da 'daukar matakan shawo matsalar a jihar ta Sokoto.









