Bidiyon ƴanbindigar da suka sace amarya farfaganda ce – Gwamnatin Katsina

Asalin hoton, AFP
- Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
'Yan bindigar da suka sace mata 53 da ke rakiyar kai wata amarya a jihar Katsina a makon da ya gabata, sun saki wani bidiyo da ke nuna matan tsaye cikin daji.
A ranar Alhamis da daddare ne 'yan bindigar suka yi garkuwa da matan masu rakiyar amarya har da direban motar da suke ciki a karamar hukumar Sabuwa da ke jihar ta Katsina.
Abin da bidiyon 'yan bindigar ya kunsa
A bidiyon mai tsawon minti 2:20, an ga dan bindiga sanye da kayan sojoji dauke da bindiga. Sun nuna matan sanye da hijabi a tsaye cikin surkukin daji. Cikin matan, akwai guda biyu masu rike da jariri.
Bidiyon ya nuna amaryar sanye da kakin soji da bindiga a wuyanta sai wani mutum wanda bisa jawaban 'yan bindigar ke nuna shi ne direban motar da wata mata dukkansu rataye da bindiga a wuya.
"In kuma akwai wanda zai iya amsar su dai ya jarraba ya gani." Wadan nan sune kalaman da aka fara ji cikin bidiyon da 'yan bindigar suka saki a ranar Talata.
Kalaman 'yan bindigar dai na nuna yanayi na kalubalantar duk wani mai iko da zai iya kubutar da matan da kuma direbansu da suka sace.
An kuma jiyo wani dan bindiga daga gefe yana Fulatanci yayin da guda a cikin su ke fassara kalmominsa da Hausa.
Sun kuma yi ikirarin mata 63 ne suka yi garkuwa da su ba 53 da gwamnatin Najeriya ta sanar an sace ba. Sai dai mai maganar da farko ya ambata 53 kafin daga bisani wata murya ta gyara masa zuwa 63.
'Yan bindigar sun yi barazanar daura wa amaryar aure idan har ba a biya kudin fansa ba.
Bayan sun gama wadannan bayanan ne kuma aka nuna matan suna rokon hukuma ta kai musu agaji cikin shasshekar kuka.
"A taimaka mana, hukuma ba za ta kwace mu ba, a kawo kudi don Allah, ba a yi mana wulakanci ba." in ji matan da aka nuna a bidiyon.
Ba duka ba zagi, ba abin da aka yi mana amma muna neman taimako, a taimaka mana, "don Allah ku taimaka mana, " - kalaman da matan suka yi ta fada ke nan.
Daga baya kuma, 'yan bindigar sun bukaci shi ma direban motar ya matso gaba ya yi bayani inda aka ji yana cewa jama'a su kai musu dauki saboda gwamnati ba za ta iya ba.
A cewarsa, "a taimaka mana, a taimaka mana, 'yan uwanmu su kawo kudi a fanshe mu, a sallame mu, gwamnati ba za ta iya wannan aiki ba, ya fi karfinta wannan aikin, an kawo mu ba duka ba zagi, Alhamdulillahi," in ji mutumin da aka ayyana direban 'yan rakiyar amaryar ne.
'Mun kadu da ganin bidiyon'
Bayan bullar bidiyon, wasu al'umma a kauyen Damari inda aka sace matan sun shaida wa BBC cewa sun kadu matuka da ganin bidiyon.
Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa mutanen yankin suna zaune jugum-jugum a bakin shaguna da gidaje suna cikin jimami na yanayin da suka ga matan da aka nuna a bidiyon suke ciki.
Sai dai sun ce ba za su iya bayyana ra'ayinsu ba saboda hukumomi sun yi ikirarin suna daukan matakai domin ganin an kubutar da matan daga hannun masu garkuwar.
Iyalan matan kuma, kamar yadda BBC ta samu bayanai sun dage da addu'oi na neman agajin Ubangiji domin ganin 'yan matan sun dawo ga iyalansu.
Martanin gwamnatin Katsina
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Kwamishinan tsaro da harkokin ckin gida na jihar Katsina, Nasir Mu'azu ya ce gwamnati za ta ci gaba da aiki ba dare ba rana domin ganin an kubutar da matan da aka yi garkuwar da su kuma suka bayyana a bidiyon.
A cewarsa, bidiyon da 'yan bindigar suka fitar wani salo ne na nuna ikonsu da kalubalantar hukumomi kan yakarsu da ake yi.
Ya ce a baya 'yan bindigar suna zuwa manyan garuruwa suna cin karensu ba babbaka sai dai an rage karfinsu saboda kokarin da ya ce gwamnatinsu take yi na fatattakar barayin dajin.
"Gwamnatin jihar Katsina ta fito da hanyoyi masu kyau, nagartattu wadanda muka ba su wahala, muka kore su suka koma daji," kamar yadda kwamishinan ya bayyana.
Ya ce sun samu sace matan ne saboda kuskuren da aka samu, matan da ke rakiyar amarya suka fita cikin dare zuwa wajen biki.
A cewar jami'in, barayin dajin sun sace matan ne domin su nuna cewa "suma sun isa" kuma su nuna "bakin cikinsu da fushin da suke na mun hana su ci gaba da cin mutuncin mutane suna kashe su, suna kama su domin su amshi kudin fansa."
Kwamishinan ya ce gwamnati ba za ta lamunci irin wannan ba kuma "za mu ci gaba da fada da mutanen nan".
Ya ce zuwa yanzu, an baza jami'an tsaro kuma suna aiki "ba dare ba rana" domin kubutar da mutanen, su koma gida lafiya da nagartarsu.
Matsalar tsaro dai na kara tabarbarewa a sassan Najeriya inda sace-sacen mutane don neman kudin fansa ya zama ruwan dare.
Ko a farkon shekarar nan ma wasu 'yan bindiga sun sace 'yan mata shida 'yan gida daya a yankin Bwari na babban birnin Najeriya sai dai bayan shafe kwanaki a hannunsu, yan bindigar sun kashe daya daga cikin yan matan daga baya kuma suka saki ragowar bayan an biya kudin fansa.
Sai dai gwamnati ta sha bayyana irin kokarin da take na gyara lamarin na tsaro ikirarin da masana suka ce bai wadatar ba.











